HAYATUL ƘADRI! page 79-80

144 14 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️79-80

*INA BAYAR DA HAƘURI SAKAMAKON JI NA SHIRU KWANA BIYU, BA NA JIN DAƊI NE, KUMA GA SHI MUN YI BIKIN ƘANWATA DA YAYANA, NA GODE DA ADDU'O'I DA FATAN ALHERINKU GARE NI, ALLAH YA BAR ZUMUNCI.*

Ƙirjina tamkar ya faɗo ƙasa saboda razana, muka ci gaba da kallon juna yana riƙe da kafaɗuna muna sauke numfashi, ƙarar da ta sake tashi daga tsakar gida da wani irin rugugi tamkar ana gudu shi ya sake zaburar da mu, ina shirin miƙewa tsaye kan gadon a gigice, ya mayar da ni ya zaunar yana shafa gashin kaina, a hankali ya yi magana idanuwan shi a kaina.

"Zauna Jannat! Ki nutsu kin ji, bari na je na duba."

Ya saki kafaɗata, har ya juya na riƙo hannunsa cike da tsoro, ya juyo ya zuba mini idanu yana kallona, cikin rawar murya na ce.

"Ina za ka je? Tsoro nake ji kar ka fita."

Ya sunkuyo ya sumbaci goshina, muka saki ajiyar zuciya a tare, na lumshe idanu, ya zame hannunsa ya ce min.

"Yanzu zan dawo fa, kiyi addu'a."

Kafin na sake magana ya juya yana wani irin taku ya fice daga ɗakin, ni kuwa zuciyata sai ɓal-ɓal take yi, na maƙure a jikin gado ina karanta duk addu'ar da ta zo bakina.

Sautin maganar shi da abin da yake furtawa yasa na gane da matar shi yake magana a tsakar gidan, na yi kasaƙe ina jiyo maganar da suke yi cike da tsoro.

"Maman Nur lafiya kuwa? Me yake faruwa kika fito da tsakar daren nan?

Ina jiyo yadda take fizge-fizge tamkar wadda ta tada iskokai, tana wata irin magana cikin ƙaraji.

"Ni ka sake ni, ka cika ni nace maka, fita zan yi daga gidan nan, ba zan zauna ba."

Ya riƙe ta gam a jikin shi cikin tashin hankali yake faɗin.

"Ki fita ki je ina? Ina za ki je wai? Me yake faruwa da ke haka ne?"

Suka fara kokawa, yana ƙoƙarin riƙe ta a jikin shi ita kuma tana ta fizge-fizge wai sai ta fita, har ta fara wasu irin abubuwa da suke nuna alamun aljanu ta tayar, ina zaune tamkar na saki fitsari don tsoro da fargaba, ƙaddara ta haɗa ni da zama da mai aljanu kenan.

Da kokawa ya ɗauketa cak ya shige da ita cikin ɗakinta, sun jima ina ta jin tashin muryoyinsu, kafin ya fito ya kulleta a ɗakin ta waje, sannan ya dawo cikin ɗakina.

Dayake a tsorace nake, a zabure na miƙe na diro daga gadon jikina na rawa, da hanzari ya ƙaraso ya kama ni ya saka cikin ƙirjin shi ya rungume ni tsaf, na kwantar da kaina tsakiyar ƙirjin ina jan numfashi, ya riƙa shafa kaina zuwa tsakiyar bayana yana magana a hankali.

"Kwantar da hankalinki Jannat, ba wani abu ba ne, Shamsiyya ce ba ta da lafiya kuma na mayar da ita ɗakinta, yanzu haka ma ƙila ta yi barci."

Na gyaɗa kaina muna daga tsaye, har na samu nutsuwata ta fara daidaita, ya ɗago kaina ya tallafi kumatuna ya zuba mini ido tare da sakin wani murmushi da ya kassara ɓargon jikina, ya tsurawa leɓunan bakina idanuwa, ya haɗiyi miyau tare da ɗaga mini gira ya yi magana cikin sigar jan hankali.

"Jannat kin yarda na tsotsa?"

Murya can ƙasa na amsa masa, saboda gabaɗaya jikina ya saki.

"Me...? Me za ka tsotsa?"

"Zumarki!" Ya ba ni amsa yana ta shafa kumatuna.

Da ƙyar idanuwana suke iya buɗuwa, sai lumshewa suke yi saboda azabar yanayin shauƙin da ya afka ni. Na yi magana a rikice cikin sigar tambaya.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now