HAYATUL ƘADRI! page 61-62

103 17 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 61-62

Yanayi na masifaffen ɓacin rai da bala'in fushi mai girgiza mutum, yanayi rikitacce mai wahalar fassaruwa, don gabaɗaya idanuwansa sun zazzaro jikinsa na mugun rawa da wata irin tsuma, yana fitowa daga banɗakin kawai ni ya nufo, ni kuma ina daga zaune, kawai sai na tsinci muryar shi wadda ta zama kakkausa cikin wani irin yanayi ya rufe ni da faɗa, abin da ko a mafarkina ban taɓa riska ba.
"Abincin ki ɗin banza, abincin ki ɗin wofi! Abincin ki da yake cutar da ni kina zuba mini guba a ciki, ba zan ci abincin ba domin guba ne a gare ni, ke ɗin banza ke ɗin wofi da za ki wani dafa abinci ki ce sai na ci, to ba zan ci ɗin ba, banza kawai...
Muryar shi gabaɗaya ta karaɗe cikin gidan yana zazzaga mini faɗa kamar zai hau ni da duka, faɗa yake yi ba ji ba gani yana ta nanata mini ba zai ci abincin ba, idan ina da matakin ɗauka in ɗauka.
Ina daga zaune na zuba masa ido har ya ƙare, ban ji ko ɗar a raina ba, sai ma wata irin dariya da na tuntsire da ita har da riƙe ciki, na dube shi a lokacin da ya saki baki yana kallona na ce.
"Ka san me? Na rantse da ALLAH wannan character ɗin bata dace da kai ba, sam-sam wannan acting ɗin bai maka kyau ba, to ai ko su 'yan film ɗin da ka kwaikwaya wani zubin idan suka yi acting director yakan ce musu su canja bai yi ba, don haka kai ma naka bai yi ba, maza hanzarta ka canja...
Na ƙara fashewa da dariya ina kallon shi na ce.
"Action!"
Wata irin zabura ya yi yana nuna ni da yatsa, bakin shi har kumfa yake yi saboda azabar masifa, yana zare mini ido ya ce.
"Ke ni za ki kalla ki ce ina miki acting ko wasa? Wasa nake miki? Ko ni sa'an wasanki ne? Lallai wannan yarinyar ba ki da hankali da kike tunanin wai acting nake, ki mayar da hankalinki idan ba haka ba kuma...
Ban ma tsaya cigaba da sauraren shi ba na tashi na shige ɗaki ina dariya, har lokacin a matsayin wasa na ɗauki abin, saboda yadda na ga mun yini cikin farinciki da ƙaunar juna, to me zai sauya shi haka cikin ƙanƙanin lokaci.
Ina zama bakin gado yana shigowa, ya cigaba da surfa masifa ko ina na jikin shi na rawa, yana faɗin.
"Na rantse Mami ba zan ci abincin ba, kuma ni a yanzu ma wurin aikina zan tafi, ba zan zauna kina cutar da ni ba."
A lokacin ne jikina ya ɗan fara sanyi, na fara tunanin ko wani abu ne ya faru, sai na ɗauke ID card ɗin shi na ɓoye na hana shi tafiya, cikin sanyin murya da 'yar shagwaɓa na fara lallaɓa shi ina faɗin.
"Wane irin wurin aiki kuma? Yau fa asabar weekend ne, kuma kana maganar za ka tafi ba tare da ka ci abincin ba, wanda kai ne ka saka ni na girka abincin saboda kana jin yunwa, ni gaskiya ba zan iya barinka ka fita kana jin yunwa ba, don ALLAH ka yi haƙuri ka zauna ka ci abincin, idan ya so ko tafiyar ne sai ka yi."
Ya hayayyaƙo mini tamkar ya kifa mini mari.
"Ke billahillazi ba zan ci abincin ba, wallahi ba zan ci ba, cikinki ne ko nawa? Ina ruwanki da yunwar da zan ji idan ma kashe ni za ta yi?"
Ni kuma sai na dage a kan ba zan bari ya tafi wurin aiki ba tare da ya ci abincin ba, tunda na san babu aiki ma a ranar, kuma idan ya tafi bai ci ba ba lallai ya samu a can ba, tunda ba wani kuɗi ne da shi ba. Hakan ya sa na yi rantsuwa ina duban shi na ce.
"Ka san ALLAH? Idan ba ka ci abincin nan ba ba zan ba ka ID card ɗin nan ba, ka zauna ka ci ka ƙoshi sai na ba ka ka tafi."
Ya nufo ni jiki na rawa yana faɗin.
"Na ce miki ba zan ci ba ko? Ko ana dole ne, dalla malama ba na son iskanci da rashin mutunci, ki ba ni ID card ɗina ko ranki ya yi mummunan ɓaci, ba na son rainin hankali da wulaƙanci."
Ni kuma na dage na hana shi, domin ban za ci abin babba ba ne, ya riƙa masifa yana bala'i kan na ba shi ni kuma na hana, ya tsaya yana kallona ƙirjinsa na sama da ƙasa cikin fushi alamar bugawa da ƙarfi yake yi, kawai kuma sai ya juya a fusace ya fice daga ɗakin, a lokacin da ni kuma na koma jaɓar na zauna kaina na masifar juyawa.

Bai jima da fita ba sai ga shi ya dawo ɗakin kamar an wurgoshi, ya dube ni a harzuƙe kuma a fusace.
"Ki zo in ji Baba idan kin ga dama."
Na ɗago a rikice na ce.
"Baba kuma?"
"Eh! Ko ba za ki je ba ne?" Ya tambaye ni a fusace.
Na girgiza kai ilahirin jikina ya yi mugun sanyi, da ƙyar nake iya taka ƙafafuwana na bi shi a baya har zuwa wurin Baban.
Muna zuwa sai Baba ya tambaye shi shin me ya faru? Buɗar bakinsa sai ya ce.
"Baba yarinyar nan yanzu ta raina ni, wani irin rashin mutunci take mini a kwanakin nan, yanzu ma saboda wulaƙanci  haka kawai ta ɗauke mini ID card ɗina ta hana ni tafiya wurin aikina."
Dayake Baban shi ma a lokacin an juya masa tunani, tunda Yaya Atika tana ta zarya da haɗa ƙulle-ƙulle, kawai sai ya hau kai ya zauna, ya rikice da faɗa kamar zai doke ni.
"Ke daman na lura yanzu kin canja hali ba ki da mutunci, na ga take-taken ki wani iskanci kike ji da fitsara, wato ba ki da kunya ko? Kina ganin kamar kin fi ƙarfin kowa a gidan nan, to zan je na samu iyayenki na faɗa musu baƙin halin da kika fara domin su ɗauki mataki a kanki, tunda nan kin fara fin ƙarfinmu, ban da wulaƙanci haka kawai ki ɗauke masa abu ki hana shi, to maza-maza ki ɗauka ki ba shi idan ba haka ba zan yi mummunan saɓa miki, zan ci miki mutunci da zarafi, yarinyar banza kawai, mara kunya fitsararriya kawai."
Tunda Baba ya fara wannan faɗan kaina ke sunkuye ina zubar da hawaye, wani irin tsoro ne a raina ina tuhumar kaina da shin me ke faruwa haka ne? Me ya sauya waɗannan mutane haka? A lokacin da Baba ke surfa mini faɗa shi kuma Ahmad ya juya ya kuma ficewa ya koma kewayenmu, ni kuma Baba ya cigaba da ci mini zarafi yana zagina da aibatani, wanda na so kare kaina amma Baba ya hana ni hakan, ya gwasale ni tare da ɗora mini laifi kacokam!
Duk da hakan ina kuka na riƙa ba wa Baba haƙuri ina faɗin.
"Don ALLAH Baba ka yi haƙuri, ban aikata hakan da wata mummunar manufa ba wallahi, ka yi mini afuwa don ALLAH Baba."
Bai saurare ni ba, ya wuce a fusace yana zagina ya bar ni a wurin, wanda tsananin mamaki ya kusa halakani, saboda na san wannan mutumi ba shi da faɗa, ba ya hayaniya, amma lokaci ɗaya ya canja, ni bai taɓa yi mini sulhu da mijina ba, amma su Algaje idan suka tashi faɗa da miji har kokawa da zage-zage suke yi, ko sulhu suka je wurin Baba ba ya iya taɓuka komai saboda duk sun raina shi, abin zai iya dawowa kansa ma, kusan kaf gidan na fi kowa ganin girman wannan bawan ALLAH, kuma shi ma yana mutuntani, amma sai ga shi a ranar komai ya zube tsakanina da shi.
Da lalube na miƙe daga tsugunon da na yi, na isa kewayena ko gabana ba na iya gani saboda hawayen da ke sharara, zuciyata zafi take mini, tun daga waje nake jiyo wani azababben kuka da Muhibba ke yi, saboda a kewayen muka barta muka fito, na ƙarasa na ga Muhibba a kwance sai tsala ihu take, shi kuma yana zaune yana ta haɗa kayansa a jaka ko kallon yarinyar bai yi ba balle ya ɗauketa, da hanzari na ƙarasa na ɗauke ta, a wannan lokaci na kai maƙura a mamakin abin da ke faruwa da mu a wannan rana.
Na ɗauki ID card ɗin na matsa gaban shi na tsuguna ina hawaye na dafa guiwarsa, cikin kuka na fara magana.
"Ga ID card ɗin ka, amma ban ji daɗin abin da ka aikata ba, me ya yi zafi haka da za ka kwashi maganarmu ka je ka kaiwa Baba? Yanzu ga shi ka sanya ya yi fushi da ni yana ta faɗa, wallahi da na san za ka faɗa masa da ban riƙe maka ba, da na san ƙarata za ka kai wurin Baba da tuni na ba ka, da na san da gaske kake yi tafiya za ka yi gun aikin nan da tuni na ba ka, ni ba na son ka tafi da yunwa ne shi ya sa na hana ka, yanzu ga shi ka sa ran Baba ya ɓaci a kan wannan ƙanƙanin abun sai faɗa yake yi, abin da bai taɓa faruwa a tsakaninmu ba, ka ɓata mana record ɗin zamanmu."
A matuƙar fusace ya miƙe tare da ingije ni gefe ɗaya, kamanninsa suka sauya gabaɗaya, a lokacin ba fuskar Ahmad ɗina nake gani ba saboda yadda ya fita kammaninsa, cikin bala'in masifa ya ce.
"Oh! Kina nufin mahaifina shi ne mafaɗaci kenan? Don uwarki don ubanki me kike nufi da hakan? Don kutumar bura ubanki mahaifina ne mafaɗaci? Mami nace ki faɗa mini mahaifina ne mafaɗaci don abu ta kazar ubanki? Don me cusa wa uwar....
Wasu irin zagi manya na ban mamaki ya riƙa cusa mini, zagin da ban taɓa ji ko a bakin yara ba, balle bakin shi mai tsarki da ban taɓa jin ya yi ashar ba, amma a wannan lokaci zagin da ya yi mini ba shi da adadi, kamar ba shi ne a 'yan awannin da suka shuɗe ya riƙa karanta mini kalaman so da ƙauna ba, duniyar ta fara juyawa da ni, idanuwana suna ganin baƙi-baƙi, masoyina ya juye min zuwa maƙiyi, a gurfanen da nake sai nake tunanin wani mummunan mafarki nake wanda nake alla-alla na farka, domin babu alheri a cikinsa, tunda Mama ta haife ni ban taɓa riskar kaina cikin damuwa da ɗimuwa da kaiwa maƙura a tashin hankali ba sai a wannan lokaci. Ban dawo daga gigitar tashin hankalin da na shiga ba na tsinci muryar shi cikin wani irin yanayi, yana furta mini kalmar da duk macen duniya ba za ta so a furta mata ba, kalmar da tun ina ƙanƙanuwata na tsaneta, nake addu'a da fatan har na koma ga Ubangijina ba za ta hau kaina ba, sai ga shi ALLAH ya jarrabe ni da ita a lokacin da ban yi zato ko tsamanni ba.
"Ki je na sake ki, kuma saki uku na yi miki wallahi, duba nan ki ga ni...
Ya ɗaga yatsun shi guda uku yana lissafawa da faɗin.
"Kin ga haka? To kamar haka na yi miki, na rantse  miki saki uku na yi miki."

HAYATUL ƘADRI!Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt