HAYATUL ƘADRI! page 65-66

107 20 1
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 65-66

*WANNAN FEJIN DUK DA BA SHI DA YAWA YANA WAKILTAR FEJIKA GUDA HUƊU RIGIS! JIYA; YAU; GOBE; JIBI; KU CANCANA SHI MU HAƊE RANAR LITININ DA YARDAR ALLAH.*

BARKANMU DA RANAR JUMA'A, RANA MUHIMMIYA MAI TARIN ALBARKA.

Da daddare ina kwance, Muhibba na gefena ina shayar da ita, a duk lokacin da nake shayar da ita ina tsintar kaina cikin matuƙar tausayinta da wata soyayyarta da ke ratsa ni, yarinyar ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba, saboda ba ni da maiƙon nono, don ma dai tana ɗan cin abinci amma ba sosai ba, sai kuma madara da Mama take ƙoƙarin ganin ta samar mata da ita.
Sabuwar wayata da ke gefena ta ɗauki ƙara alamar kira, Muhibba ta fara bacci shi ya sa na zame ta na gyara mata kwanciyarta. Na lalubi wayar na ɗaga, da na ɗaga sai aka katse kiran, can aka sake kira, na ɗaga aka katse, haka aka yi ta yi wajen sau huɗu, a na biyar ɗin ne kawai kamar a mafarki sai na ji muryar Ahmad ta ratso kunnuwana, irin faɗuwar gaban da na samu kaina a wannan lokaci babu misali, ko mayar masa da amsa ban yi ba kawai na saka lambar a black list na jefar da wayar, na koma da baya na kwanta ina sakin gwauron numfashi, wasu zafafan hawaye suna fito mini daga idanuwana.
A lokacin babu wani mahaluki da nake ganin baƙinsa a zuciyata da idanuwana idan ba shi ba, saboda ina jin haushinsa a kan batun sakin nan, shi ɗin ba mutum ne mai zafi ba, amma ina tuhumar shi da laifin biye wa su Hajiya da Atika da ya yi, tunda ni a tunanina tun kafin su fara asirce-asircen nasu da kirsa da munafurci suka ja shi, kuma ya biyr musu, ya san waɗannan mutane ba masu ƙaunar shi ba ne amma ya biye musu hatta abincin su ya riƙa ci, a lokacin babu irin abin da ban nuna masa ba don ya gujewa hakan, amma yaƙi ji yana ganin kamar raba musu zumunci zan yi, wanda ni kuma ba hakan ba ne a raina, a ganina ko da asiri to akwai sakacinsa a ciki, domin suna tsare shi su bugi cikinsa a kan zamana da shi, shi kuma yana buɗe musu komai, ba ya iya ɓoye musu sirrinmu kamar yadda ni na ɓoye hatta iyayena ban yi saken da suka sani ba. Tun a wancan lokacin ya kamata ya ɗauki mataki a kan juyashin da suke yi, kuma ya tashi ya nemi tsarin jikin shi, amma shi sai ya nuna tsoron su yake ji yaƙi taɓuka komai har suka samu nasara a kansa.
Sai daga baya kuma bayan sun gama shan cikinsa, sun riga sun gama jin abin da za su ji, don ko tawowa gida da na yi a lokacin da suka ce za su ba shi mashin ya tafi lagos, babu irin bugar cikin da basu yi masa ba, Atika tarewa ta zo ta yi a ɗakina kullum tana zaryar zuwa wurin shi, tun a lokacin me yasa bai bijire musu ba? Ya saki jiki da su tare da sakin baki yana bayyana musu sirrin zamana da shi, ya riga ya yi wauta a lokacin saboda sun ɗora shi a keken ɓera ya riga ya hau. Ya kasa riƙe komai kamar yadda ni na riƙe. Ni na tabbatar a wancan lokacin kafin asirin ya fara aiki wallahi shi ma da laifinsa, ya riga ya bada kansa a wurinsu, sun mayar da shi mara wayo, shi kuma ya biye musu ya zama soloɓiyo.
A haihuwar Muhibba ne ya yi fushi da su kan ba su zo sun yi barka sun ga jaririya ba, wanda bai sani ba ashe tuni lokaci ya ƙure masa sun gama da shi, wannan dalilin ya sa ya banzatar da su, ya daina kula su ya ɗauki gaba da su, ya yi rantsuwa a kan ba shi ba su tunda suka aikata hakan, har da faɗin sai ya ɗauki mataki a kansu, wanda a lokacin ni na riƙa ba shi baki a kan ya bar komai ya manta da komai, don basu zo barka ba ai dubunsu sun zo, ba na so ya nuna musu ɓacin rai tunda ya san halinsu, bamu san masifar da za su ƙullo mana kan hakan ba, amma buɗar bakinsa cikin fushi sai ya ce mini.
"Na rantse da ALLAH Mami sai na ɗauki mataki, ALLAH ya ba ni arziƙin samun ɗiya amma su ka sa ko da yi mini barka duk yadda nake da su? Wallahi ba zan bari ba sai na ɗau mataki, kuma babu ni babu su."
Matakin da ya ɗauka shi ne daina yi wa Atika magana, tare da daina zuwa inda take, ko ta aiko ya je ba ya zuwa, ba ya ɗaga wayarta, ko ganinta ya yi a hanya canja hanya yake yi.
A take sai suka yi tunanin ai ni ce na saka shi ya daina mu'amala da su, wanda ALLAH ne shaidata ban taɓa nuna masa damuwata kan basu zo barka ko suna ba, shi ne ya nuna damuwar shi ya fito da ita sarari, kuma na yi iya bakin ƙoƙarina don ya danne damuwarsa amma yaƙi fuskanta a wannan lokacin, wannan abin suka riƙa wajen ganin sai sun ga bayan aurena da shi, kafin na raba su da shi su bari su raba ni da shi kenan.

HAYATUL ƘADRI!Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang