HAYATUL ƘADRI! page 39-40

114 17 2
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 39-40

Kuka nake sosai hawaye na malala, ya ɗago ni ya riƙa goge mini hawayen yana girgiza mini kai fuska ɗauke da damuwa ya ce.
"Don ALLAH Mamina ki daina kuka, hankalina tashi yake yi, ki faɗa mini me yake faruwa?"
Cikin shessheƙa na ce masa.
"Babu komai, kawai dai ina so ka tafi da ni yau don ALLAH, ba zan iya kuma kwana ba."
"An miki wani abu ne?" Ya tambaye ni yana kallona.
Hawaye ya sake ɓullo mini, na girgiza kai na ce.
"A'a! Kawai dai gida nake so"
Ya tsura mini idanu yana sauke ajiyar zuciya, ya zaro wayarsa cikin aljihu ya daddana ya kara a kunne.
"Zo inda muke tsaye."
Haka ya ambata bayan ya ɗaga wayar, ya kashe ya mayar aljihu, yana riƙe da hannuna ya sunkuyar da ƙai ƙasa.
Maryam ta ƙaraso, da alamun ita ya kirawo, tana zuwa ya ɗaga kai ya kalleta.
"Maryam shin zuwanku an yi wa Mami wani abu ne da bai kamata ba?"
Maryam ta dube ni ta sunkuyar da kai, a sanyaye ta fara magana ta ba shi labarin duk wulaƙancin da aka yi mini da horon yunwa. Hankalinsa ya tashi sosai, ya riƙa kallona idanuwansa suka cika da ƙwalla, ya yi magana yana girgiza hannuna.
"Mamina! Kiyi haƙuri kin ji, akwai ALLAH, duk wanda kika ji ana ba wa haƙuri tabbas an cutar da shi ne."
Na gyaɗa kai ina share hawaye. Ya dubi Maryam ya ce.
"Ku shirya Maryam, yau za mu juya."
A take na ji wani sanyi a raina, Maryam tayi murmushi cike da murna ta ce.
"To Yaya Ahmad."
Ta ja hannuna muka yi gaba, ina waiwayensa ina kallon bakinsa da ke furta mini kalamar "I love you Mamina!"

*********

Muka dawo gida, ni dai a gakabaice nake saboda yunwa, duk da ya sama mini abinci na ci amma ban dawo daidai ba, haka muka kwana biyu da dawowa ina jin kaina sama-sama.
Ranar talata ina zaune kamar saukar wahayi na ji wani irin ciwo ya sakko mini, bayana da ƙirjina suka riƙe gam! Hankalin Ahmad ya tashi ya kwashe ni sai babban asibitin Haɗejia can garinmu, saboda garin da nake babu babban asibiti, muka je ya yi buga-buga aka rubuto mini magungunan da zan sha, don hankalina ya kwanta kawai sai ya wuce da ni gidanmu domin na ga su Mama ko zan ji sanyi a raina.
Gabaɗaya 'yan gidanmu sai hankalinsu ya yi masifar tashi ganin ramar da na yi, na dawo kamar ba ni ba, musamman Mama ta gigice sosai da ganina cikin wannan yanayi, nan Ahmad yake ce musu ba ni da lafiya ne shi ne ya kawo ni asibiti domin a duba ni.
Mama ta riƙe ni a jikinta tana ta tattaɓa ni, hankalinta ya dugunzuma, sai ambaton sunana take yi da faɗin.
"Rahamatullahi wane irin ciwo kika yi haka gabaɗaya halittunki suka sauya, kin fita daga kamanninki, hasbunallahu wani'imal wakeel!"
Ina jikin Mama sai numfashina ya fara sama-sama tamkar zai ɗauke, na fara haki idanuwana na shirin ƙaƙƙafewa. A rikice suka kuma kwasata sai asibiti,  nan da nan aka karɓe ni aka ba ni taimakon gaggawa tare da yi mini wasu allorori, na ɗan dawo hayyacina.
Da Abba ya ga na marmaro sai ya bari muka tafi da magariba muka koma garinsu Ahmad, don Ahmad yana cike da fargabar kar na faɗa wa su Mama halin da muke ciki.
Misalin ƙarfe tara na dare ya raka ni banɗaki zan yi fitsari, na kammala na fito kenan kamar wadda hantsilota sai ga ni rigijib! Na faɗi a wurin, numfashina na tafiya tamkar ana fizgarsa, ya saka salati a ruɗe ya ɗauke ni tamkar jaririya ya yi ɗaki da ni, a hanzarce ya ɗauki waya ya kira gidanmu yana kuka ya faɗa musu halin da nake ciki.
Yayyena da muke cousins da su, su ne suka tawo tare da Mamana da motarsu, suka tarar da ni ranga-ranga rai a hannun ALLAH, iya ruɗewa sun ruɗe tuni suka fara kuka, a daren suka kwashe ni da ni da mijina sai asibiti. Muna isa emergency aka karɓe ni aka ba ni gado.
Ban san halin da na kasance ba saboda sumewar da na yi, kawai na farka tsakar dare ne sannan na gane a cikin asibiti nake.
Dangina da 'yan uwana da Ahmad suna zagaye da gadon da nake, lokacin kusan ƙarfe biyu na dare, kowa da abin da yake saƙawa a ransa.
A lokacin hankalin iyayena ya yi matuƙar tashi da halin da suka ganni a ciki, musamman da likita ya yi musu bayanin mummunar Olsa ce cronic ta kama ni, wadda take tafiya da numfashin mutum, sannan kuma ina cikin tsananin damuwa.
Babban tashin hankalin da na farka sai nake wani irin gigitaccen tari na fitar hankali, wanda idan na yunƙura zan yi tamkar ƙirjina zai fita daga gangar jikina, don da a lokacin da aka yi corona virus ne tsaf za a killace ni, don tarin ya kai maƙura wajen gigitarwa. Asibitin babba ne sosai general hospital ne, amma idan tarin ya tasar mini duk mahalukin da ke cikin asibitin zai iya jiyo ƙarar tarin indai da daddare ne, tari ne wanda kamar ba daga cikina yake fita ba, tare ne wanda wasu suka ɗauka jinnu ne ma saboda yanayin ƙararsa tare da fitar da wata irin majina mai kama da dafarar mutuwa.
Iyayena, 'yan uwana, mijina, babu wanda yake iya rintsawa ko na minti guda, sun tattara suna kallon ikon ALLAH da yadda ALLAH ya mayar da ni lokaci guda, kaf cikin emergency a lokacin babu mara lafiya abad tausayi kamar ni. Saboda abin ya yi tsananin da kowa yake ganin lokacina ne kawai ya yi, mutuwa zan yi na koma ga Ubangijina.
Ba zan iya kwatanta halin da mijina ya kasance ba, tunda ya ga yadda rayuwata ta kasance ya fita daga hayyacinsa, domin halittuna duk sun sauya, na koma kamar ƙwarangwal ko wadda take fama da ciwon ƙanjamau, an yi test kala-kala domin a gane wane irin ciwo ne nake fama da shi haka, amma ba a gano ba, sai dai tsananin azaba da nake sha, daga baya ma sai aka canja mini ɗaki saboda abin ya ta'azzara, kuma majinyatan da muke tare da su sun fara razana da ni.
A wannan ɗaki na cigaba da ɗanɗanar wahala da azabar ciwo, tari kamar wanda ake rura shi, numfashi yana sarƙewa, an rasa gano kan wannan lalura duk binciken likitoci, sai na dawo jikina a cikin kashi goma babu kashi tara sai kashi ɗaya, kamar yagulallen tsumma haka na dawo, ba kowa yake iya shaida ni ce Rahamatullahi ba.
A wannan hali da na shiga, 'yan uwan Ahmad na wurin uwa babu wanda ya zo ya duba ni, haka ɓangaren mahaifinsa babu wanda ya zo illa mahaifinsa da Umman Fati, wanda tunda suka zo suka ga yanayin da nake ciki suka sallama suka riƙa kuka da tausaya mini.
Sai ta kai ta kawo numfashi sai da taimakon likitoci aje ƙwato mini shi, idan ya tafi kamar zai ɗauke Abbana da Mamana ke riƙe ni suna kuka tare da yi mini addu'a. Mijina yana kuka na tashin hankali yana kife kansa kan ƙirjina a gaban su Abba, hawayensa na malala kan ƙirjina yana faɗin.
"Mamina! Kiyi mini rai kar ki tafi ki bar ni, ke kaɗai nake da ita wadda ke faranta raina a halin da na shiga ƙunci da raɗaɗin rayuwar duniya, ba na fatan rashin ki ya zamo daga cikin ƙaddarorin da ke bibiyar rayuwata, don ALLAH ki tashi Mami, ki tausayawa Ahmad kar ki tafi ki bar shi a filin duniyar da ke cike da gararin rayuwa...
Ina jin sa, amma ba ni da ikon yi masa magana domin na rarrashe shi, illa hannuwansa da na riƙo na ɗora kan ƙirjina domin ya danne mini don kar ya fita daga jikina saboda zabar da nake ji.
Na fara fidda rai da rayuwa, a jikina nake jin wa'adina ne ya zo, don wata ranar juma'a wani mutum da kusan muke ɗaƙi ɗaya da shi ALLAH ya yi masa cikawa, sai rasuwar ta bige ni sosai, a take na riƙa jin ni ma mutuwar zan yi, sai lokacin ALLAH ya buɗi bakina na janyo hannun Mamana da ke kusa da ni tana mini addu'a, cikin tsananin ciwo na ce mata.
"Mamana idan ta ALLAH ta kasance a kaina don ALLAH ku gatantani wajen yi mini addu'a, da ke da Abbana da sauran 'yan uwana, addu'arku kawai nake buƙata Mama."
Mama ta fashe da kuka tana damƙe hannuna ta ce.
"Ki daina faɗin haka, kina tayar mini da hankali Rahama, in sha ALLAHU za ki tashi, ALLAH zai ba ki lafiya ya tashi kafaɗunki."

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now