HAYATUL ƘADRI! page 81-82

137 16 1
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 81-82

Sai bayan awa biyu da tura mata hoton sai ga kiran Karima ya kuma shigowa wayata, da hanzari na ɗauka cikin zumuɗin jin abin da zai fito daga bakinta.

"Karima wai me yake faruwa ne don Allah? Kin saka ni a tunani fa."

Sakin baki na yi jin ta bushe da wata irin dariya, ina niyyar sake yin magana ta tsagaita da dariyar ta ce.

"Kin san me?"

"Sai kin faɗa, ke nake saurare." Na ambata cike da zaƙuwa.
Ta sake yin dariya kafin ta ce.

"Labarin yayarki na kawo miki, wato Atika."

Sai da na ji ƙirjina ya buga da ƙarfi, na gyara zama tare da sake maƙale wayar kamar zan cusa ta cikin kunnuwana, kafin cikin sarƙewar harshe na ce mata.

"Atika kuma? Me ya faru ne wai?"

Ta sauke ajiyar zuciya ta fara koro min bayani kamar haka:

"Rahama ɗazu ina zaune a gidan ƙanwar Ummanmu an mini lalle, kawai sai ga wata Antinmu ta zo gidan ita da wata aminiyarta, ta rako aminiyartata ne domin ta kawowa ƙanwar Ummanmu wani ɗinki, dayake tana ɗinki sosai, bayan sun zo suka zauna ana ta hira, ni dai kallon aminiyar antin tamu kawai nake yi saboda kallo ɗaya na yi mata na ji ba ta kwanta mini a raina ba. To ashe akwai dalili, dalilin kuwa ashe ita ce Atika Auyo, matar da ta gallaza miki a dalilin auren ɗan'uwanta da kika yi, kuma ta yi sanadiyyar raba ki da shi, kuma ita ce ta yi sanadin mutuwar mijin Ummata, kin san bayan mahaifina ya rasu Ummana ta sake aure, to bayan ya aureta ya sake auro wata mata wadda aminiyar Atika ce, kuma da Atika da wannan matar su suka haɗa baki wajen kashe mijin Ummana saboda ba sa tsoron Allah, dayake ban taɓa ganin Atika a fuska ba sai a ranar, kuma ban san ita ce ba, sai da hira ta yi hira ana zancen mutuwar aure sannan na gane ta, a lokacin da na ji ta yi tsagal tana ce wa.

"Ni ma nan akwai 'yar garin nan Haɗejia, wata tsinanniyar yarinya wai ita Rahama, ta auri ɗan'uwana Ahmad ta mallake shi, ni kuwa na ga ba zan iya ba muka bi ta bayan fage muka tsige auren muka kaɗa shegiya gaba, sannan muka samu sukuni."

Wato ƙunshi ne a ƙafata, amma ina jin ta faɗi hakan ban san lokacin da na take ƙunshin ba na miƙe tsaye ina nunata da yatsana a rikice, na ce mata.

"Rahama kuma? Baiwar Allah kodai ke ce Atika Auyo?" Saboda a lafazin bakinta kaɗai na gane ke take nufi, tunda babu wanda bai san sune silar mutuwar aurenki ba a lokacin.

Ta gyara wuyan rigarta tana wani fari da idanu irin na 'yan duniya, ni kam zuba mata idanuwa na yi ina kallon wasu irin ƙasusuwa a wuyanta, a komaɗe take kamar wadda ta shekara ba ta ci abinci ba, ta washe mini jajayen haƙoranta da suka yo gaba saboda molewar da kumatunta ya yi.

"Ƙwarai ni ce Atika Auyo, ai na ci dubu sai ceto, ina jin kin taɓa jin suna na da labarina ne ko?"

Ina jin ta faɗi hakan na ce mata.

"Ɗan jira ni ina zuwa." Na ɗauki wayata na kira ki a lokacin na ce ki turo mini hotonki, saboda ina son raba gardama.
Kina turo mini ni kuma na haskawa Atika hoton na ce mata.

"To mguwa azzaluma mai baƙin hali, kalli nan ki ga yadda Rahama ƙawata ta zama, ki kalli yadda tayi kyau ta wuce tunaninki, matsayin da ta taka a yanzu mijin da take aure ya zarta ɗan'uwanku a komai da kika sani na rayuwa fiye da inda ba kya zato, asararriya kawai."

Sakin baki kawai ta yi tana kallon hotonki cike da tsoro da mamakin yadda ta ga kin dawo kin yi fes da ke, jikinta sai mazari yake yi. Ita kuwa Antina da suka zo tare bata gane kan zancen ba, shi yasa ta tambaye ni wai me yake faruwa ne ita bata gane ba, nan da nan kuwa na juya na fara kora mata jawabi.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now