HAYATUL ƘADRI! page 85-86

143 17 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 85-86

Kwana biyu bayan hakan na shirya tafiya ganin gida, ina ta zumuɗi zan tafi Haɗejia domin na ga Mama da Muhibba da sauran dangina, wanda da ƙyar Mustafa ya amince mini kan na yi kwana biyu, saboda ba ya son na yi nesa da shi. Da ni da Ramlat za mu tafi.

Kamar a lashe mu don murnar ganinmu, bakin Mama yaƙi rufuwa a lokacin da ta yi arba da 'ya'yanta, Anti Zulaihat kuwa a gidan muka same ta, ta kasa jurewa tunda taji labarin za mu zo shike nan ta tawo gidan Mama ba za ta iya jiran muje gidanta ba.

Muka haɗu kafataninmu ana ta hira cikin farinciki da annashuwa, ni dai sai wulga idanuwa nake yi ban ga Muhibba ba, har dai na gaji na tambayi Mama.

"Mama wai ina Muhibba ne? Tunda muka zo ban ganta ba."

Kafin Mama ta ba ni amsa sai na ji gabaɗaya sun fashe da dariya, Ramlat cikin dariya ta ce.

"Kawai shiru na yi, amma na gane tunda muka zo kike zoƙara wuya kina son hango inda Muhibba take."

Maimunatu ta amshe tana dariya ita ma.

"Lah! Anti Ramlat ashe kema kin lura, ni tunda kuka zo nake ganin Anti Rahama tana ta zare idanuwa da kallon loko-loko na gidan nan, ashe Baby Muhibba take nema."

Na zoɓara baki na kaiwa Maimunatu dundu a baya, ta kauce tana dariya, sai lokacin Mama tayi magana tana murmushi.

"To banda abin ku laifi ne don uwa ta nemi 'yarta? Ƙaunar da ke tsakanin Rahama da Muhibba ai mai girma ce, ni banga laifinta ba."

Ta juyo gare ni ta cigaba da faɗin.

"Kinga Rahama rabu da su, Muhibba tana ɗaki tana bacci yanzu haka."

Na saki murmushi na miƙe zan nufi ɗakin Mama, Anti Zulaiha cikin dariya ta ce.

"Kai Mama ina ma ba ki faɗa mata ba, so na yi na tsokaneta na ce mata dangin babanta sun zo sun ɗauketa."

Dab da zan shige ɗaki maganar Anti ta daki kunnuwana, a hanzarce na juyo na dalla mata harara don na manta ma cewar ita yayata ce ta girme ni, sai da na ga ta riƙe baki tana kaɗa kai ta ce.

"Ni kike harara? Da idanu tulu-tulu kamar gujiyar lahira."

Na ɓata fuska kamar zan fashe da kuka, Mama ta dube ni ta ce.

"Wuce ki shige ki ga 'yar ki kin ji, bar su su ƙarata da shirmensu."

Na kuya na yi musu gwalo sannan na shige, suna bi na da tsokana Mama tana tare min.

A hankali na zauna bakin gadon inda Muhibba ke kwance, na tsura mata idanuwa cikin bugun zuciya ina kallon fuskarta mai kama da ta mahaifinta, yatsanta guda biyu a baki tana tsotsa idanuwanta a rufe,  ta yi kyau ta ƙara ƙiba da haske tamkar ba ita ba, wata matsananciyar ƙaunarta ta yunƙuro mini, sai ga ni na zame bakin gadon na kwanta kusa da ita tare da rungumota  zuwa tsakiyar ƙirjina.

Danshin da na ji a fuskata ya tabbatar min hawayena ne ya zubo, hawayen tausayin Muhibba da halin da take ciki na rashin mahaifinta a kusa, ko ina za a je da uba ake ado, kamar yadda nake ganin Abbana nake jin daɗi ina tinƙaho ita ma watarana za ta buƙaci hakan, za ta buƙaci ganin wanda ya yi silar zuwanta duniya, za ta so ganin mahaifinta, za ta so haɗuwa da shi domin ta kira shi Abbanta kamar yadda kowane yaro yake kiran mahaifin shi, za ta so ta ji ɗumin shi, za ta so ya riƙe hannuwanta ya ambaci sunanta da ya raɗa mata, duk waɗannan abubuwan ta ya ya za su faru alhali ba a san inda yake ba, shekaru sun fara shuɗewa, watanni da dama sun wuce, sati bayan sati har zuwa kwanaki da awanni da mintuna, zuwa sakankunan da basu da adadi, amma babu ɗuriyar Ahmad, babu wanda ya san inda yake bare a san halin da yake ciki, gabaɗaya rayuwar baya ta dawo mini sabuwa fil, na riƙa kuka ina rufe baki saboda kar su Mama su jiyo ni, har ban san lokacin da hawayena ya riƙa gangarawa kan fuskar Muhibba ba.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now