HAYATUL ƘADRI! page 43-44

118 16 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*©️HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 43-44

*WANNAN LITTAFIN MAI SUNA HAYATUL ƘADRI, KACOKAM! MALLAKINA NE DA DUK ABIN DA YAKE CIKIN SA, A GUJI ƊAUKAR MINI A JUYAR MINI DA SHI TA WANI ƁANGARE NA DABAN, DOMIN AKWAI TSATTSAURAN MATAKI KAN HAKAN DA ZAI IYA KAI MU GA HUKUMA, HAƘƘIN MALLAKAR HASSANA ƊANLARABAWA NE*

Na rikice ganin yanayin Mama, saboda ba kasafai na fiye ganin ɓacin ranta ba, mace ce mai matuƙar haƙuri, don zan iya cewa idan ana gadon haƙuri to tabbas a wurinta na gada ni ma. Da muka shiga ɗaki guiwata na zube a ƙasa ƙirjina na matuƙar bugu,  haka na gaishe ta bakina na mugun rawa, muryar da tayi amfani da ita wajen amsa mini gaisuwar ta ƙara ankarar da ni matsanancin ɓacin ran da take ciki, domin da ƙyar ta iya furucin fuska a turɓune babu walwala.
"Sannu Rahama! Sannu kin ji, na gode miki da abin da kika yi mini."
Ras! Gabana yayi wata irin faɗuwa, hawaye ya cicciko idanuwana, na dube ta a yayin da hawayen ya tsiyayo mini kan fuskata, na sanya bayan hannu ina sharewa, wasu na sake fitowa. Da ƙyar na matsa kusa da ita na ce.
"Mama...!
Ta ɗaga mini hannu alamun dakatarwa, na yi shiru idanuwana a kanta ina haɗiyar zuciya, ta girgiza kai tare da ce wa.
"Ban yi tsammanin kina da abin da za ki ce mini ba Rahama, domin da da gaske kin ba ni matsayin uwa a zuciyarki da ba ki aikata abin da kika aikata ba, a tsawon rayuwata da ke tunda na haifeki kin taɓa ganin na je na roƙi wani? Aliyu ɗan uwana ne da muka fito ciki ɗaya, amma ban taɓa zuwa gare shi neman wani abu ba sai dai idan shi ne ya yi niyya ya ba ni, a wajen ALLAH nake nema, sai yau 'yar da na haifa ce za ta zama haka? Ki wanke ƙafafu ki tafi roƙon abinci saboda zubar wa da kai ƙima Rahama! Duk da ba wajen bare kika je ba ɗan uwana ne amma tabbas ban ji daɗi ba, me yasa ni ba za ki same ni ki faɗa mini halin da kuke ciki ba? Ni ya fi cancanta na san duk wani hali da kike ciki a matsayina na mahaifiyarki."
"Kiyi haƙuri Mama, don ALLAH ki yafe mini...
Na ambata cikin kuka. Ta girgiza kai ta ce.
"A duk duniya idan da wanda ya kamata ya san matsalar da kike ciki bai wuce ni ba, a kan me za ki ɓoye mini halin da kike ciki ki kasa buɗe baki ki sanar da ni? To abin da ba ki sani ba shi ne, tuni na fara ɗago yanayin da kike ciki tun a kwanakin baya, na zuba miki ido ne kawai domin na ga iya gudun ruwanki Rahama."
A firgice na sake kallonta, fuskarta a tamke ta cigaba da magana.
"A duk lokacin da kika ziyarci gidan nan nakan ga abubuwa sun ragu, ma'ana na kula kina ɗiban abinci a ɓoye ki tafi da shi, ki kan ɗebi shinkafa, mai, maggi, ki ɓoye ki tafi da shi, a zatonki ban sani ba ko?"
Wata matsananciyar kunya ce tayi masifar lulluɓe ni, tabbas idan haka ne babu wanda ya kai uwa ankara da halin da yaranta suke ciki, domin kuwa an yi haka babu adadi, a lokacin da muke cikin halin tsananin yunwa ina ziyartar gida sosai, kuma duk lokacin da zan je da leda ta nake tafiya, wadda nake fakar idanuwan Mama da ƙannena na ɗibi shinkafa ko da kwano biyu ce, na ɗibi mai da maggi da wasu abubuwan na ɓoye, idan zan tafi na faki ido na fito da su, a lokacin tamkar wadda aka rufewa baki domin ina ji a raina ba zan iya buɗe baki na faɗa wa Mama halin da muke ciki ba, dalilin ba na son tona asirin aurena da mijina, ashe ni duk ban sani ba Mama tana ankare da ni, duk lokacin da na ɗiba idan na koma ɗakina haka zan ta kuka ina takaicin ɗibar abincin gidanmu ba tare da sanin iyayena ba, in ta roƙon ALLAH ya yafe mini kar ya kama ni da laifin satar wa iyayena abinci duk da tarbiyya da ilimin da nake da shi.
Mama ta katse mini tunani da kukan da nake yi ta hanyar ci gaba da maganar ta.
"Rahama na sha saka shakku a raina a kan shin da gaske ke ce ke aikata hakan? Ban tabbatar ba sai da na gani da idanuwana, sai na zauna ina nazarin to shin me yake faruwa? Me yake faruwa da rayuwar aurenki? Me yasa ba za ki fito ki sanar da ni ba? Sai na ce bari na zuba miki idanu na ga inda ɓoye-ɓoyenki zai ƙare, tunda na san ke ba yarinya ba ce, kuma ke ba jahila ba ce, kin mallaki hankalinki, kina da ilimi da komai, amma abin da kika aikata a yau ya kawar mini da tunanin da nake a kanki, ya alamta mini cewar har yanzu akwai ƙuruciya a tare da ke."
Na matso ina ta kuka na kamo hannayenta na riƙe cikin nawa na ɗorasu kan cinyarta, na buɗe baki da ƙyar na ce.
"Mama ban aikata hakan don na tozarta kaina ko don na tozarta iyayena ba, kaina ne ya kulle Mama, na kasa hango mafita saboda yanayin da muka shiga ni da shi na matsin rayuwa, kuma ban ɓoye miki don wani abu ba, sai don kar na ɗaga muku hankali a matsayinku na iyayena, gara ni na shiga tashin hankalin a kan ku ku shiga, sannan Mama ba na son tona asirin mijina, domin yana matuƙar ƙoƙari a kaina ta yadda duk wahalar da zai sha zai nemo ya ba ni, idan bai ba ni ba sai dai idan ALLAH bai nufe shi da samu ba, amma don ALLAH kiyi haƙuri idan na ɓata miki rai, abu ma fi tsanani a duniyata shi ne na wayi gari mahaifiyata tana fushi da ni."
Ta zare hannuwanta daga cikin nawa, ta kai hannun kan fuskata ta share mini hawaye, a yayin da nata idanuwan suka ciko da ƙwalla.
"Ba tonan asiri ba ne don kin same ni kin faɗa mini halin da kike ciki, wallahi Rahama zan iya taimaka muku ba tare da ko mahaifinki na bari ya sani ba, abin da ya sake ɓata mini rai shi ne zuwa wurin Aliyu da kika yi har ya san matsalarki, amma shike nan babu komai haka ALLAH ya ƙaddara, ALLAH ya yi ta sanadin zuwanki wurinsa zan san komai, duk da ina zargi daman, na kuma san Ahmad mutumin kirki ne wanda yake son ki da gaskiya, halin da ya shiga lokacin da ba ki da lafiya kaɗai ya tabbatar wa duniya shi ɗin ya kai maƙura a son ki, don kin rufa masa asiri ba ki yi laifi ba, sai dai akwai hanyoyin da ya kamata ki bi wurin rufa masa asirin ba wai ku zauna cikin yunwa da wahalar rayuwa ba, duk da dai bawa bai isa ya gujewa ƙaddarar shi ba, ba komai na haƙura na yafe miki, ALLAH ya maganta ya yi miki albarka."
Cikin farincikin yafe minin da tayi na rungume ƙafafuwanta gam ina faɗin.
"Na gode Mamana."
Ta shafa kaina, sannan ta ɗago kaina daga kan ƙafafuwanta ta dube ni ta ce.
"Amma ina so na sanar da ke cewa, rayuwa ba za ta yiwu a haka ba, shi babu abin yi ke babu abin yi, shawarar ɗaya zan ba ki, mai zai hana ki tambaye shi idan ya amince ki fara aikin koyarwa? Kinga ɗan albashin da za ki riƙa samu zai toshe muku abubuwa da yawa kafin ALLAH ya kawo masa mafita."
Na gyara zama sosai na ce.
"To ai Mama matsalar garin da muke babu wata makaranta taƙamaimai da zan samu aikin, domin da da akwaita da tuni shi ma ya nema ya fara, kuma matsalar ƙasar nan kin san yadda samun aiki yake da wahala, shi ne kawai matsalar."
Ta sauke numfashi ta ce.
"Daman ina nufin ki samu koyarwar a nan garin, makarantar da nake koyarwa lokacin da nake da cikin 'yan biyu na daina zuwa, har kika karɓeni kika cigaba da zuwa lokacin da kike T.P. Na san da gudu za su karɓe ki saboda kin gwada sun ga yanayin aikinki kuma sun yi alfahari da shi, kinga ita private ce."
Wani farinciki na ji sosai a raina, a take na ji a raina yayewar matsalarmu ta zo, ban taɓa wannan tunanin ba saboda cushewar da kaina ya yi, amma yanzu daga sanin matsalarmu har mahaifiyata ta kawo mini mafita, uwa mai daɗi kenan!
Hawayen daɗi ya kwararo mini, na tashi na rungumeta jikina na rasa bakin magana ma, ita kam sai murmushi take yi tana saka mini albarka tare da addu'a.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now