HAYATUL ƘADRI! page 11- 12

135 12 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 11-12

Lambar Ahmad da sunansa suna yawo kan fuskar wayar, na gyara kwanciyata wasu hayawayen na tseren gudu suna jik'a filon da na d'ora kaina a kai, da k'yar na iya danna wayar na kai kan kunnena tare da yin sallama da shak'ak'k'iyar muryata. Ban ji amsa sallamar ba, illa muryarsa da na ji tamkar a rud'e yake yana ambatar.
"Mamina! Me yake faruwa ne? Ya na ji muryarki haka?"
Na kai bayan hannu na share hawayen, na ja hanci na sauke ajiyar zuciya.
"Babu komai, ina fatan kana lafiya? Ya Abuja?" Na ambata ina k'ok'arin danne damuwata.
"A'a Mami kar ki ce haka, na rantse a jikina na ji cewa kina cikin damuwa, sai ga shi muryarki ta k'ara ba ni tabbaci." Ya ambata a marairaice.
Na k'ara k'ank'ame wayar ina lumshe idanu na ce "Baka ba ni amsa ba, ya Abuja?"
Ya sauke ajiyar zuciyar da ta ratsa ilahirin jikina ya ce "Abuja babu dad'i Mami, tunda babu ke a cikinta, jin dad'in d'aya ne, da ya kasance na zo cikinta ne domin na samu y'an canjin da zan yi hidimar aurenmu da su idan lokaci ya zo."
Sai ya ba ni kunya tare da cillani cikin wani shauk'i, na runtse idanuwa tamkar a gabansa ina sakin ajiyar zuciya a hankali, ya dawo da ni hayyacina wajen fad'in.
"Na amsa taki tambayar, daure ni ma ki amsa tawa Mamina."
Na tattakura na mik'e zaune da k'yar saboda yadda jikina ya yi mini nauyi, na sa filo na jingina da garu wayar tana kunnuwana.
"Ba wani abu ba ne, wata rasuwa a ka yi mini da ta gigita tunanina." na fad'a cikin rawar murya.
"Waye ya rasu?" Ya tambaye ni da sauri.
Ba ni da zab'i illa bayyana masa abinda ya faru, ganin ya rud'e tunda ya fuskanci yanayin da nake ciki. Sosai ya tausaya bayan ya gama jin labarin ya ce,
"Allahu akbar! Allah ya gafarta wa wannan mata, ina miki ta'aziyya Mami."
Na share hawaye "Amin. Na gode." Na amsa cike da rauni.
Ya sauke ajiyar zuciya yana rage murya "Mami hankalina ya tashi da yadda na ji halin da kike ciki, na samu kaina da azarb'ab'i da kaiwa mak'ura a son ganin ki, don Allah ki ba ni damar zuwa gareki mana."
Na girgiza kai kamar yana ganina na ce.
"Ba ina k'in zuwan ka ba ne, na dai fi so ka zauna ka mayar da hankalinka wajen sana'ar da ka fara kai da Baba, ka ga dai ba ka jima da fara wa ba, idan Baba ya lura kana tsalle-tsalle da k'in maida hankali ba zai ji dad'i ba, ba lallai sai ka ganni ba, tunda sa'i da lokaci kana jin muryata."
"To Mami wani lokacin muryar ma ai rowarta kike mini, idan na je aiki na wuni kujiba-kujiba dare ne lokacin da ya kamata na saurari muryarki mai warware mini gajiyar da na kwasa, amma kuma sai ki k'i bari mu gana da juna, me yasa hakan?" Ya k'arasa da tambaya.
Na gyara zama na mayar masa da amsa "Ba haka bane, ka san dai ni shugaba ce ta (M S S N) A makaranta, kuma a cikin aikina akwai hana y'ammata yawaita yin wayar dare da samari ko tsayuwa da su, to mai zai sa ni da nake hana wa na b'ige da aikata wa? Idan na yi hakan kamar ban yiwa kaina adalci ba ko?"
Sautin murmushinsa ya ratsa jikina, ya yi magana cikin wata irin murya wadda kana jin ta ka san cikin shauk'i yake.
"Allah ya taimaki Mamina! Shi yasa ki ka mamaye ruhina gabad'aya babu ragowar gurbi, ina bayanki, ki ci gaba da kwatanta adalci a duk wani shugabanci da Allah zai d'ora miki. Ina son ki Mami!"
Kalmar k'arshe da ya ambata ta tayar da tsigar jikina, a take wasu hawaye masu sanyi suka kore masu zafin, suka zubo mini kan fuskata a yayin da na lumshe idanuwana ina sauraren muryar Ahmad da ke ambata mini so.

*************

Muka ci gaba da karatu babu kama hannun yaro, ban tab'a mantawa da mamaciyar nan ba nakan yi mata addu'a kullum idan na yi sallah.
Karatu ya fara d'aukar Zafi a lokacin da jarabbawa take tunkaromu, ni dai ban gigice ba saboda na san kaina kuma ina bawa karatu lokaci da rayuwata, nakan hak'ura da duk wani hutu ko jin dad'i domin na ga na yi karatu, son karatu a jinina yake, a yayin da tuni d'alibai da yawa idanuwansu suka fara raina fata, wad'anda suka watsar da karatu suke sharholiyarsu yadda suka ga dama, a farkon semester ba su da aiki sai wasa da d'aukar wanka, a fidda kud'i a sayi kayan kwalliya na dubunnai ai ta kwalliya ana saka suttura ta ke ce raini ana yanga kamar ba za a taka k'asa ba. Da jarrabawa ta zo sai ga shi ko mai ba sa iya shafa wa a jikinsu, butu-butu suke rayuwa a firgice, wata ma kayan da ta saka sai suyi kwana uku bata cire ba saboda razana, dalilin makarantar akwai rik'on wuta a wurin malamai, a kan maki d'aya cal idan ka rasa sai ka koma baya, ashe duk k'aryar banza ce da b'ata wa kai lokaci, yarinya a farkon semester tai ta shiririta, sai lokacin jarrabawa idanu su raina fata.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now