HAYATUL ƘADRI! page 5-6

186 21 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 5-6

https://chat.whatsapp.com/EykycDYZDn64yObhFIA7WC

Na ja k'afafuwana cikin dukan zuciya na isa gaban Sa'adatu. Na durk'ushe a kan guiwoyina tare da sanya hannayena na d'ago kanta da ta matse tsakankanin cinyoyinta, na bi fuskarta da kallo wadda ta yi jage-jage da hawaye, hankalina ya sake tashi. A duniya na tsani na ganta cikin damuwa, domin ni ma ba ta barin damuwa ta samu muhallin zama a gareni, takan yi duk mai yiwuwa domin ganin ta sama mini farinciki a lokacin da ta fuskanci ina cikin damuwa.
"Ya subhanallah! Sa'adatu me ya faru da ke tsakar dare kike kuka haka? Mene ne yake damunki?" na tambayeta a rikice.
Sai kawai na ji ta fad'o jikina ta rungumeni ta kuma fashewa da kuka, tausayinta ya yi matuk'ar ratsa jikina duk da ban san damuwarta ba, na yi namijin k'ok'ari wajen mayar da nawa hawayen da ke k'ok'arin fitowa, don kar a yi d'a kwance uwa kwance. Na d'ago ta daga jikina na sanya hannu ina share mata hawayen da ke saraftu da tseren gudu daga idanuwanta zuwa kan fuskarta.
"Haba Sa'adatu sa'ar mata! Don Allah ki fad'a mini abinda ke faruwa kafin ni ma na fara kukan, kin san ba na son ganinki cikin damuwa ko?"
Ta jijjiga kai, da k'yar kuma ta iya fizgo maganar da take so tayi ta furtata.
"A kan maganar da Umma ta zo wa da Abba ne d'azu, na kasa runtsawa saboda ba haka na zab'arwa kaina ba Rahama."
Na sauke numfashi na ce, "Wai kina nufin maganar Yaya Bashir?"
Ta gyad'a mini kai "Eh! Ita, kin san cewa mun tsara komai namu yadda zai tafi ni da ke a tare, me yasa za a wargaza nawa shirin kawai don buk'atar Yaya Bashir? ni ba za a dubi uzurina ba kenan?"
Na gyara zama sosai na rik'o hannayenta cikin nawa hannun, na zuba mata idanuwana na ce?,
"Wa ya fad'a miki duk  abinda bawa ya tsarawa kansa tilas shi yake faruwa da shi? Kar ma ki saka wannan tunanin a ranki Sa'adatu, duk wani tsari da muka yiwa rayuwarmu ba lallai ya tafi a kan abinda zukatanmu ke so ba, k'addara takan sauya komai."
"Ban gane ba Rahama." Ta fad'a cikin rawar murya.
Na ce "K'addara ta zab'a mini cigaba da karatu, ke kuma k'addara ta zab'a miki yin aure."
Ta zame hannunta daga jikin nawa ta share hawayen da ya kuma zubo mata, sannan ta ce,
"To amma ai laifin Yaya Bashir ne, tunda yana sane da muradina shi ne cigaba da karatu kafin aure, akan me zai b'arar mini da damata saboda cika muradin tasa zuciyar?"
"Saboda yana matuk'ar son ki da k'aunarki." na amsa mata.
"Haka ake so? Zuwa fa ya yi ya had'a ni da Umma a kan maganar, shi ne ita kuma ta goya masa baya har ta samu Baba da Abba da maganar, su ma kuma suka biye mata, ni yanzu ina ji ina gani sai dai kiyi karatu ni kuma na yi aure kenan?"
Na yi ajiyar zuciya na ce, "Duk fa ba wani abu ne na tashin hankali ba, Yaya Bashir yana son ki. Kuma ya shirya aure yanzu, kawai kuma don kina son karatu sai ya hak'ura ya zauna zaman jiran ki?"
Ta ce "Eh! Tunda ya ji ya gani yana so na ba sai ya hak'ura ya jira ni na kammala ba, tunda shi dai ya ce ba zai barni a gidansa ina fita makaranta ba."
"To kiyi hak'uri don Allah, ina nemawa Yaya Bashir afuwa idan har ya b'ata miki, amma ki sani, so ne ya janyo hakan, dubunnan mata nawa ya tsallake ya zab'o ki? ki goya masa baya kawai mu ragargaji biki, daman mun jima shekaru kusan uku zuwa hud'u bamu rak'ashe da biki ba tun bikin Anti Zulaiha, ki godewa Allah ke kin samu karatu mai yawa ma da ya kai matakin kammala Sakandire, wasu suna nan ko Firamare ba su kammala ba kuma aka katse su aka yi musu aure, duk da na san karatu yana da matuk'ar fa'ida da alfanu amma aure gaba yake da shi a gareki yanzu, tunda kina da ilimin da za ki yi rayuwar zaman aurenki." na k'arasa tare da sakar mata murmushi domin dai na samu k'uncin da ke ranta ya warware.
Ta rausaya kai ta ce "Hmm! Kawai dai kin cika  ni da dad'in baki ne, gabad'aya kun k'i ganin laifin Yaya Bashir, shikenan, amma idan kina so na hak'ura sai dai ke ma ki bar k'udurinki na cigaba da karatu muyi auren a tare."
Na kama baki cike da mamaki na ce "Kin san dai ni tsoron maza ma nake yi a halin yanzu, kuma babu wanda nake ganin ya cancanta na aura a duk masu fitowa suna so na."
Ta d'an harareni ta ce "Haka dai kika ce kawai, amma ai ga Auwal, wace irin soyayya ce bai nuna miki ba? amma kika saka shi a kwandon shara, ga kuma Malam Adam na makarantar dare da ya mato a kanki shi ma, kwana kwanan nan ji nake har Ankul Mustafa d'an yayar Mama sai da ya fito yana son ki, amma duk kika bad'awa idanuwanki toka kika k'i amincewa da su."
Na yi murmushi na ce "Ba k'in amincewa da su nayi ba, da Auwal da Malam Adam ina da dalili mai k'arfi da ya saka na gujewa aurensu, shi kuma Ankul Mustafa kin san irin tsananin izzarsa saboda yana ganin yana da y'ay'an banki, kuma a tsarina kin sani ba na son auren mai kud'i wanda ba ya ganin darajar d'an adam, ko fa wurina ya zo kina ganin yadda yake mini magana a tsaitsaye cike da gadara, duk da ina da hak'uri na tsani wulak'anci Sa'adatu, shi yasa ba zan iya aurensa ba."
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "To amma....
Na katseta na dakatar da ita "Ya isa haka, dare ne fa bai kamata kowa yana bacci mu mun zauna muna ta surutai ba, ki tashi mu d'aura alwala mu raya daren tunda ko mun kwanta ma ba barcin za mu iya komawa yanzu ba."
Da wannan na kashe bakin Sa'adatu, ta mik'e ta shige band'akin da ke cikin d'akinmu, jim kad'an ta kammala ta fito ni ma na shiga. Muka raya daren da salloli, bamu koma mun kwanta ba sai da muka sallaci Asuba har gari ya fara haske, sannan muka yada hak'ark'arinmu.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now