HAYATUL ƘADRI! page 15-16

163 16 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 15-16

Albishir d'in haihuwar y'ar uwata Sa'adatu, wannan daddad'an labari ya k'ayatar da ruhina musamman da haihuwar ta zo ina cikin hutun makaranta, na rik'a zakwad'i da zumud'i, burina bai wuce na ganni a kano gaban Sa'adatu da babyn da ta haifa. Mama dai dariya ta rik'a yi mini tana tsokana ta.
"Oh! Rahama irin wannan zakwad'i haka? Lallai abin na yi ne wai an biya wa bazawara aikin hajji."
Na k'yalk'yale da dariya na ce "Mama wani ya yi rawa ma bare d'an makad'i, tilas na kasance cikin murna da k'aruwr da muka samu, wai yau Sa'adatu ce ke da babynta a hannu." Na k'arasa da alamun mamaki.
"Idan da rai da lafiya ke ma kamar yau ne za ki ganki da na ki babyn idan Allah ya so." Mama ta ambata tana dariya.
Kunya ta rufe ni, na tashi da sauri ina rufe fuska na  ruga d'aki ina fad'in.
"Kai Mama! Ni fa ba haka nake nufi ba."
Na bar Mama tana dariya.

Saura kwana biyu suna muka isa kano, Sa'adatu duk da jegonta sai da tayi tsalle ta rungume ni cikin matuk'ar murna muka fad'a kan kujerar falon, da sauri  goggo mahaifiyar Sa'adatu ta d'auke babyn ganin za mu danne shi saboda murna.

An sha bidiri ba kad'an ba a wannan haihuwa, Yaya Bashir ya saki hannu wajen ganin ya bayar da duk abinda ake buk'ata,
Sai bayan suna da kwana biyu sannan muka yi shirin koma wa Had'ejia. Sa'adatu duk ta damu ji take yi tamkar ta bimu, sai da Mama ta rik'a rarrashinta tukun, ni kam ji nake kamar na tafi da babyn saboda k'aunar yara da nake matuk'ar yi, haka muka yi sallama da Kano ta dabo tumbin giwa, ko da me ka zo an fika, jalla babbar Hausa mai d'umbun jama'a. Mu ma mun shaida kirarin kano domin ta cancanta.

A wannan hutu na k'arshen shekara Ahmad yakan ziyarce ni sosai, a lokacin ne ma ya fara matsa wa a kan yana so a fara maganar aurenmu, ni kuma na rik'a lallab'a shi a kan ya yi wuri a fara maganar auren, ya bari a k'ara kwana biyu tunda akwai sauran shekarun da zan kammala karatu a gabana, haka ya hak'ura duk da ransa bai so ba. A kullum k'orafinsa shi fa tsoro yake ji, ya san a yadda nake na had'a komai na k'ara gogewa kar wani ya zo ya yi masa kutufo ya bar shi da jinya ko ma ya yi silar barinsa duniya, idan ya fad'i hakan nakan yi murmushi na ce.
"Har yanzu baka yarda da kanka ba ne? Rahama ta yi wa mazaje da yawa katanga da zuciyarta, da kai kad'ai ta amince, kuma ko a bayanka babu wani."

Wannan hutun ma na k'are shi ne cikin murna da farinciki, daga nan na tattara na koma makaranta domin shiga Lavel 2 don cigaba da karatu.

A rana d'aya muka koma makaranta ni da su Saudat, muka yi registration lokaci guda domin mu samu d'akin da za mu cigaba da zama a tare, muka cike takardar neman d'aki a take muka samu aka sauya mana d'aki, domin ba za mu cigaba da zama a wancan d'akin ba tunda mun kammala lavel 1. Da ni da Saudat, Kadija, da kuma Halima muka kama d'akin, domin cigaba da zama a tare duk da kowa course d'in sa daban amma akwai shak'uwa a tsakaninmu ta yadda muke son zama tare da juna.
Karatu ya k'ara d'aukar zafi sosai, domin akwai bambanci da karatun lavel 1 da lavel 2, karatu muke babu kama hannun yaro, haka nan bamu cillar da zuwa asibiti domin duba marasa lafiya ba. Domin akwai watarana da muka shiga asibiti ni dai ranar har lalura sai da na yi, na k'ara jin matuk'ar tsoron Allah yana ratsa b'argon jikina, hak'ik'a duk bawan da bai ji tsoron Allah ba ya tab'e duniya da lahira, mun firgita ne da ganin wani hatsari(accident) da aka kawo (emergency) cikin asibitin, yadda muka ga jikin d'an Adam ya yi fisis, hannu daban k'afa daban, sassan jiki duk ya fita, wannan tashin hankali ya k'ara mana tsoron Allah a zukatanmu, musamman da na tuna da watarana da Abbana yake mini nasiha a kan tsoron Allah, har ya ce mini.
"Rahama a ko'ina kika kasance to ki rik'a jin tsoron Allah da tsoron tsayuwarki a gaban sa, saboda Allah (S W A) ya yi alk'awarin kyakkyawan lada ga duk wanda ya ji tsoronsa, kuma ya kame kansa ga barin bin son zuciya. Allah ya ce:

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now