HAYATUL ƘADRI! page 49-50

124 17 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 49-50

"Hmmm! Wasu dai idan za su fita jaka suke saɓawa a baya su tafi gantalin su, mu kuwa 'ya'ya muke saɓawa a baya mu tafi."
Sosai na ji saukar maganar kamar aradu! Na tsaya cak ina juya ma'anar ma'anar jimlar da ta furta, wadda a take na gane baƙar magana ta faɗa mini mara daɗi, irin ai ita tana haihuwa ni kuma ba na haihuwa, wanda a lokacin ba ta san da ciki a jikina ba.
Murmushi kawai na saki na girgiza kai, ina mata fatan shiriya da samun ilimi domin ta fita daga duhun jahilcin da ya lulluɓe duniyarta, na ga idan ma na tsaya mayar mata da martani mun taru mun zama ɗaya kenan, kawai sai na ba wa banza ajiyarta na watsa ta a kwandon shara na fice daga gidan.

Ina tafe a mota amma tunane-tunane sun cika raina, ban san me na tare wa mutane da suka sanya mini ido a rayuwata ba, ban shiga rayuwar kowa ba, amma ni an maida tawa wurin da kowa zai shiga ya yi dabdala son ransa, mutane da yawa na mini gorin haihuwa, suna ganin ai na kwashi shekaru biyu da aure amma har yanzu ban dire albarkar aure ba, kowa da abin da zai faɗa, wasu suce tsarin iyali nake yi, wasu ma ce wa suke zubar da cikin nake yi idan na samu, don ba zan manta ba labari ya zo mini a kan ƙin zuwan su Hajiya su duba ni lokacin da na sha jinya a asibiti, cewar Hajiya ta ce ai zubar da ciki na yi a lokacin, shi ya sa bata ga dalilin da zai sa ta zo duba ni ba ita da iyalanta. Ban taɓa ɗaga kai na kalli masu maganganun ba, domin ba ka isa ka hana kowa faɗin albarkacin bakinsa ba, tunda na yi nazari na ga tsakanina da Ubangijina a gyare yake, sai na kawar da komai na miƙa masa lamurana.
Na yi zurfi a tunani har ban san mun iso ba, sai da direba ya ankarar da ni tukun.

******

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar mana, ina rainon cikina, abubuwa kuma sun fara yi mana sauƙi muna jin daɗin rayuwarmu sosai.
A lokacin ne Yaya Atika ta haihu, danginsu na Kano da suka tashi zuwa suna kawai sai suka tarkato tun saura kwana biyu suna, ba su sauka a ko ina ba sai gidan da nake cikin kewayena, wai ni ce mai masaukin baƙi.
Ni dai na ga ikon ALLAH! Wato mutane ne waɗanda ba sa son zaman lafiya ko kaɗan, ba ƙaramin raini suka mini ba shi ya sa kowacce ta ɗebo kashinta kaina take yaɓawa, sun tarar da ni da abinci fal ktcheen da kayayyakin amfani, su a zaton su ɗan uwansu ne ya dire komai, ba su san ni da mahaifiyata muke ƙoƙarin hakan ba, shi ya sa suke kallona a sheƙe tare da ba ni umarnin girka musu abin da ransu yake so ko da kuwa ba na so.
A lokacin ne ni ma na yi nufin motsa ƙwanjina ko zai yi tasiri, domin naƙi yarda da rainin hankalinsu kwata-kwata, duk abin da na ga sun zo da rainin hankali a ciki ɗaure fuskata nake na fita daga sabgarsu, kuma sai abin da naga dama nake yi, ba su isa su saka ni ba kuma ba su isa su hana ni ba.
Akwai 'yar gidan Atika wadda tuni an mata aure ma, mai suna Hajara, yayar Sailuba ce, har da ita aka zo, maimakon ta sauka a gidansu sai ita ma ta tawo inda nake saboda tsabar neman rigima, duk da tana tutiyar gidana ya fi kamata ta zauna, tunda gidan Yaya Atika ba gidan ubanta ba ne, su tuni Yaya Atikar ta bar gidan mahaifinsu ita da Sailuba ta zo tayi wani auren har tana ta haifar wasu 'ya'yan, ita ba ta iya zaman aure saboda yadda take addabar kishiyoyi da 'ya'yan miji, da zarar ta gama da namiji sai ta fice ta auri wani, Atika makirar mace ce ta innalillahi, duk wasu siffofi na saɓa wa ALLAH sun bayyana a tare da ita, duk da girman da ya fara hawa kanta ba ta kunyar fita waje da kaya masu bayyana surar jikinta, don ko majalisar maza za ta wuce haka za ta hau karkaɗe-karkaɗen mazaunai da nonuwa don ta ja ra'ayinsu, ba ta damu da aurenta ba, duk inda za ta ja hankalin namiji nan hankalinta ya fi karkata, ga ta ita ba wata kyakkyawa ba, muni kamar a yankata a ɓoye wuƙar, amma dayake tana haɗawa da asiri wasu mazan sukan biye mata har ta ja ra'ayin su kuma har ta ja ra'ayinsu su afka kogin shaiɗanarta.
'Ya'yan Yaya Atika gabaɗaya ba su da tarbiyya balle kunya, sun ga yadda uwarsu take gudanar da rayuwarta shi ya sa suka zama makwafinta, za su iya gayawa kowa maganar da suka so hankali kwance duk girman mutum kuwa. To amma ni a wannan lokacin sai na ɗauke musu wuta ɗif! Don na ga wargi ma wuri shika samu, ba na zama cikinsu ma balle su jaza mini ɓacin rai, shiryawa nake na tafi makaranta na kulle ɗakina na bar su a kewayen, don ko ranar sunan ban zauna ba, tafiyata na yi makaranta saboda idan ka yi fashi ana yanke maka albashi tunda private ce, ni kuma ba na son a yanke mini tunda komai a ƙididdige yake.
Da na je makaranta a ranar sai na ji kamar na wuce gidanmu na zauna na huta kawai kafin su tattara su tafi, duk da Ahmad ba ya ba su goyon baya a wannan lokacin, yana bayana, amma wulaƙancin waɗannan mutane yana da yawa, domin wani rainin hankali da suka yi mini a safiyar ba don na jajirce ba da sun ga wallena.
Akwai ƙanwar Yaya Atika itama 'yar Hajiya ce, wadda har da ita a waɗanda suka tare a wurina, da safiyar ɗan da take goyo ya kyakkyaɓa uban kashi a wando ya yi dama-dama da shi, gabaɗayansu suka ƙi taɓawa wai ni zan wanke wannan kashi, ga ni da ciki mai azabar ƙyanƙyami, na ga dai babu ta yadda za a yi na taɓa wannan kashin saboda yanayin da nake ciki, ni kuwa na ce musu wallahi ba zan iya wankewa ba, naƙi taɓa yaron balle wandon da ƙuda yake bi, aikuwa sun shaƙa sosai, don ina jin su har Hajiya suka kira a waya suna faɗa mata ƙarya da gaskiya a kaina, wai na wulaƙantasu na tozarta su.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now