HAYATUL ƘADRI! page 47-48

107 18 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 47-48

https://t.me/joinchat/HF-zgNIyT2EXO86h

*GA LINK 👆 ƊIN GROUP ƊINA NA TELEGRAM, MASOYANA DA MASOYAN LABARAINA SAI KU AFKA CIKI DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARAINA A SAUƘI, WANDA BA SU DA TELEGRAM YA KAMATA SU JE SU SAUKE A PLAY STORE DOMIN MU GAME A CAN. NA GODE* 

Na firgita sosai da ganin waɗannan abubuwa, idanuwa warwaje nake kallonsu ina sauke numfashi, bakina na rawa wurin furta addu'o'in da duk suka zo bakina. A haka na sanya hannu na ɗauki abubuwan da bisimillah, sannan na koma gefe na zauna ƙirjina na tsananin bugu, mamakina ya aka yi waɗannan abubuwan suka samu muhallin zama cikin ɗakina? Waye ya kawo mini su? Kuma na mene ne? Tambayoyin da na jerowa kaina kenan, wanda na san babu mai ba ni amsarsu a halin tunda ni kaɗai ce a cikin ɗakin, abu mai sauƙi a gare ni shi ne na duba su na warware layar don ganin abin da ke ciki, domin masu karin magana sun ce 'In ka ji na ƙiya, samun dama ne' ba zan ƙi buɗewa ba domin ina son sanin me ke ciki.
Da addu'a a bakina na warware, sai na ga takarda ce aka yi rubutu da jan abu, an saka sunana wato RAHAMA, amma a maimakon su yi amfani da ƙaramar 'ح' sai suka yi amfani da babbar 'ھ'.
Na jima zaune ina tunanin wannan abu, domin na san maƙiya ne suka aikata, shi kuma maƙiyinka ba ya ganin ramarka, tabbas dole na sake miƙewa da addu'a, na yi tunanin idan ya dawo na nuna masa, amma kuma sai na tuna tunda na dawo babu wata sakewa a tare da mu, ba ya mini magana gabaɗaya hankalinsa ya juye, duk da ni ina ta tuhumarsa a kan me yasa ya yi mini haka? Me yasa ya bayar da sheda mara kyau a kaina ya faɗi abin da ban yi ba? Amma yaƙi ce mini komai, duk da hakan na ƙuduri aniyar nuna masa ko da abin da zai ce, da ya dawo kuwa na nuna masa, amma abin mamaki bai ba wa abin kulawa ba, hakan ya sa na fawwalawa ALLAH komai, ina tuna cewa ko mutuwa na yi a wannan ƙadamin to na san ni ce da nasara. Ban ƙona kayan ba, sai na ɗauke su na je na zuba a masai na kora.
Na cigaba da addu'o'in tsari da neman sauƙi wurin ALLAH, kwananmu shida a haka babu wani sauƙi daga gare shi, sai a cikon kwana na bakwai sannan na fara ganin alamun sassauci daga gare shi, ma'ana ya dawo hayyacin shi.
Ya haƙura da zancen tafiya lagos, sannan ya fara yin baya-baya da Yaya Atika, ya daina zuwa wajenta, ya daina karɓar abinci idan ta kawo masa, sosai ya cigaba da ba ni kulawa a wannan lokacin.
Watan azumi ya riske mu a wannan yanayin, a haka duk da azumi da ɗawainiyar ciki nakan shirya na tafi wurin aikina, wataran shi yake raka ni har bakin titi na samu mota na tafi, wani zubin kuma har biyo ni yake yi idan na kammala aikina mu koma tare.
'Yan uwana da dangina da ƙawayena, suna ta sha'awar yadda muke kulawa da junanmu, suna ganinmu tamkar wasu ƙawaye ko abokai, duk inda nake yana tare da ni. Idan muka zauna muna tuna abubuwan da suka faru sai ya yi ta kuka yana ba ni haƙuri da faɗin.
"Mami ban san na aikata ba, ki yafe mini kin ji Mamina."
Ni kuwa sai dai na yi murmushi na ce.
"Babu komai mijina, komai mai wucewa ne."
A cikin azumin ne watarana abubuwa suka ɗan dagule saboda ban karɓi albashi ba komai namu ya ƙare, har a ka sha ruwa babu wani abin kirki da muka samu muka ci ni da shi, balle a zo kan abin da za mu yi sahur ɗin azumin washegari, muna zaune jigum-jigum, sai na dube shi ya ɗaga kansa sama ya runtse idanuwa, na san cikin tunani yake.
"Ka tashi ka hau mota a daren nan ka tafi wurin Mama domin mu samo abin da za mu ci, ka ga dai ba mu da komai, kuma na san ita ma ba ta yi tsammanin komai namu ya ƙare ba." Na ambaci hakan cikin sanyin murya tare da kamo hannayensa na riƙe.
Ya ware idanuwansa a kaina tare da sakin ajiyar zuciya, ya girgiza kai ya ce.
"Haba Mami, ni wallahi ba zan iya zuwa ba, ai da kunya a ce kullum ina safara gidanku karɓo abincin da za mu ci ni da ke, wannan ai shi ne 'Ka sayar da akuyarka amma ta dawo tana ci maka danga' Mama tana iyakar ƙoƙarinta, ba na son mu ƙureta."
Ni ma na girgiza kai na ce.
"Ba za mu ƙureta ba, domin ta san yanayin da kake ciki na jarabtar rashi, don ALLAH ka daure ka je ka karɓo mana."
Ya kuma gigiza kai yana lumshe idanu.
"Gaskiya Mamina ina jin kunya, ba zan iya zuwa ba, muyi haƙuri kawai.
Cikina ya murɗa mini saboda yunwa, Hausawa kan ce 'Tambarin talaka cikinsa' Tabbas haka ne kuwa.
Na yi juyin duniya amma yaƙi amincewa, ga hadari ya fara haɗowa a gari, da yiwuwar ruwan sama zai iya kecewa, ni kuma a yadda nake ji na kai azumi ba zan iya kwanciya haka ba har na tashi da wani azumin, miƙewa na yi kawai na shige ɗaki na ɗauki hijabina na saka na fito na yi hanyar fita daga kewayen, muryarsa na ji yana kirana amma sai naƙi amsa masa saboda na san zai iya dakatar da ni, shi kuma ba shi da komai da zai ba mu mu ci, haka ya tashi da hanzari ya biyo ni muka jera har bakin titi, yana ta mini ƙorafin wai a daren nan za mu tafi har Haɗejia wurin Mama, na yi masa shiru na tari mota da 'yar ragowar ɗari biyun da nake da ita, shi ma ya hau motar sai ga mu cikin ikon ALLAH mun iso.
Mama dai kawai sai ganinmu tayi, lokacin ƙarfe tara na dare, ga hadari sosai, na yi ƙoƙari sosai wajen haɗiye damuwata, ina ta fara'a, saboda ko dangina ba na bari su san damuwata, duk a ganinsu ba na cikin wata matsala ina samun yadda nake so. Idan na shiga cikinsu sajewa nake da su in ta wasa da dariya da barkwanci, ba na barin ƙofar da za su fuskanci ina da wata damuwa ko kaɗan.
Mama dai ta yi mamakin ganinmu, na zauna kusa da ita ina dariya, shi kuma ya zauna daga gefe kansa a ƙasa suka gaisa da Mama, ta waiwayo ta dube ni tana murmushi, kafin tayi magana na riga ta.
"Mama sai kika ganmu katsaham ko?"
Mama ta ce, "Eh wallahi, ga dare ya yi, ga kuma hadari, ALLAH dai ya sa lafiya Rahama?"
Na yi murmushi na ce.
"Mama ai yau ba lafiya ne fa."
Ta zaro idanu tana faɗin.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Me ya faru?"
Na ƙyalƙyale da dariya ina faɗin.
"Ah! Mama kwantar da hankalinki, cewa nayi yau ba zan iya bacci ba sai na ganki, haka kawai muna zaune wani shauƙinki ya taso mini, shi ne ya rako ni domin na ganki."

HAYATUL ƘADRI!Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora