HAYATUL ƘADRI! page 13-14

149 11 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 13-14

Mama da ke tsaye ta hard'e hannuwa a k'irji tana kallona fuskarta d'auke da wani irin murmushi, farincikin da ba shi da misali ya baibaye zuciyata, a take na sa hannu ina matsar da yaran da ke gabana zuwa gefena, na kwashi sauri da sassarfa na nufi Mama, ta bud'e mini hannaye ina zuwa na afka k'irjinta na k'ank'ameta gam kamar za a k'wace mini ita, hannayenta bisa bayana tana shafawa tana ta sakin murmushi, danshin hawayena da ta ji a k'irjinta ya sa ta d'ago kaina daga jikinta tana kallona.

"To mene ne abin kuka kuma Rahama? Kukan na mene ne? Ta tambayeni idanuwanta a kaina.
Na kwantar da kaina a kafad'arta ina ji a zuciyata duk duniya babu wanda ya kaini murna, a hankali na ce "Na farinciki ne Mama."
Ta yi y'ar dariya ta ce "Na ga alama kam, domin na ji hawayen da sanyinsu suka fito ba da d'umi ba."
Ni ma na yi dariya, yara suka zo suka kuma kewaye mu sai rik'e ni suke yi, Mama ta dube su ta dube ni.
"Yau fa ba zama 'Matar falke ta haifi jaki' Yadda yaran nan ke marmarinki anya za su barki ki huta ma kuwa?"
Na dinga shafa kansu ina murmushi, na b'allo jakar da ke bayana na zuge na d'auko jakar alawar(Milkos) na dank'awa Maimunatu na ce,
"Maimunatu ja su ku shiga ciki ki rarraba musu, ga ni na shigowa.?
Da murnarsu suka bita ciki suna tsalle, muka had'a idanu ni da Mama muka saki murmushi.
Mama ta ce "Mu je ciki kiyi wanka ki huta ko? Ga abinci can an tanadar miki kala-kala sai wanda kika zab'a."
Na rik'e hannunta murmushi ya kasa barin fuskata, na ce,
"Allah sarki Mamana na gode, amma kafin nan ina son ganin Abbana, ina yake?"
Ta ce "Abbanki yana tare da d'alibai masu d'aukar karatu. Na san shi ma da ya san kin sauka da tuni ya sallame su don ya ganki."
"Aikuwa ba zan iya jurewa har su kammala ba, bari kawai na iske shi ina son ganinsa Mama." Na fad'i hakan ina kalllonta.
Ta yi dariya "Rahama y'ar gidan Abbanta."
"Kuma y'ar gidan Mamanta ba." Na k'arasa mata ina dariya.
Ita ma tayi dariya muka wuce ciki, inda kai tsaye na wuce d'akin karatun Abba. Na shiga da sallamata cikin d'okin ganinsa, a dai-dai lokacin da suka shafa addu'ar tashi daga karatun. Farincikin da na hango a fuskar Abbana ta fi gaban kwatance, hak'oransa sun kasa rufuwa fad'i yake "Marhaban da Rahamatullahi...
Na k'arasa da hanzari na zube guiwoyina a k'asa cikin girmamawa, ban san me yasa hawaye ya sake tsattsafo mini ba sai dai jin zubar su na yi shar a kan fuskata, na kasa magana sai sharar hawaye nake yi, Abba dai dariya ya yi yana duban d'alibansa su uku da ke gaban sa.
"Malamai ku gane mini Rahama da raguwar zuciya, to mene ne na kuka kuma daga dawowa?"
Suka yi murmushi, d'aya daga cikinsu ya ce "Akaramakallahu kukan murnar ganinka take yi, musamman da ya kasance ta d'auki tsawon lokaci bata ganka ba."
Abba ya yi murmushi ya juyo gare ni ya ce "Wai haka ne Rahama?" Na gyad'a masa kai na kasa cewa uffan har lokacin hawaye na zubo mini.
D'aliban Abba suka yi masa sallama suka fice, ya waiwayo kaina ya ce.
"Bari dai na zo na ji dalilin da malaman makarantarku suka zamar mini da ke bebiya, sumul na kai musu ke amma kin dawo mini da nak'asu a tare da ke."
Dariya ta kufce mini duk da hawayen fuskata, na rufe baki ina dariya, Abba ma ya yi dariya ya ce.
"To ina ta magana Rahama ta kasa amsawa, ba dole na zargi haka ba."
Na matsa kusa da shi a hankali na yi magana.
"Abbana!"
"Na'am Rahamata." Ya amsa.
"Na yi kewarku sosai Abba, shi yasa farincikin ganinku ya sanya ni hawaye."
Ya girgiza kai "Mu ma duka mun yi kewarki, musamman ni da idan na laluba na rasa mai taya ni karatu, sai na ce Allah sarki ina ma Rahama tana nan."
Na ce "Ayya! Abba ni ma kullum idan zan yi karatu a makaranta nakan tuna ka, musamman idan zan yi tafsiri."
Ya gyad'a kai cikin murmushi ya ce "Da kyau! Na ji dad'i da ba ki zubar da karatunki ba, kina bita sosai ko?"
Na gyad'a kai na ce "Eh Abba ina yi sosai, har ma na janyo wasu muna yi tare, ai ban tab'a sauka daga turbar daga ka d'ora ni ba."
Cikin murna Abba ya ce "Ma sha Allah! Allah ya yi miki Albarka, to yanzu ya kamata ki je kiyi wanka ki huta ki ci abinci, sai mu zauna domin na ji labarin makaranta da yadda komai ya tafi ko?"
Na yi dariya na ce "Aikuwa Abba za ka ji in sha Allahu."
"Madalla!" Abba ya ambata.
Na mik'e zan fita daga d'akin, har na kama k'ofa zan fita Abba ya ambaci sunana tare da tambayata.
"Rahamatullahi! Shin Ahmad ya san da dawowar ki a yau kuwa?"

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now