HAYATUL ƘADRI! page 7-8

173 18 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 7-8

*DON ALLAH WANDA YAKE CIKIN GROUP 1 KO HASSANA D'AN LARABAWA FAN'S KAR YA SHIGA WANNAN 2 D'IN* 👏👇
https://chat.whatsapp.com/JqZ3K5n1VZL6wvbC98Myfd

Hawaye ya zubo mini shar a kan fuskata, a take jikina ya kama mazari tamkar ana kad'a mini gangi. Ban san abinda ya karya mini zuciya don Ahmad ya ambata mini So ba, tunda ba yau na fara jin an ambata mini shi a duniyata ba.
Rawar da jikinsa ya d'auka sai ya shallake nawa, a sakamakon ganin hawaye na saraftu a kan fuskata. Ya matso sosai fuskarsa na nuna jimami, kusancin da ke tsakanina da shi ya sabbaba mini jiyo yadda k'irjinsa ke bugawa fat! fat!!
"Don Allah kiyi hak'uri Mamina! Tun ranar da idanuwana suka yi tozali da ke ba ki sake barin numfashina ya huta ba, matsananciyar soyayyar ki da na samu kaina a ciki ta k'arar da kuzarina da k'wanjina har tana k'ok'arin mayar da karatuna baya, sakamakon rashin ganinki balle na bayanna miki k'aunarki da ke shan sharafi a tsakiyar k'irjina."

Kalamansa suka dinga ratsa gab'ob'in jikina, har suka sake samar da sabon rauni a zuciyata fiye da tsammani, hawayena ya cigaba da zuba ina d'aukesu da yatsun hannuna. Ahmad ya dafe kai ya cigaba da magana cikin rashin kuzari.

"Iya rad'ad'in son ki da ya mamaye k'irjina ya wadatar Mami, ba sai kin had'a da zubar mini da hawayenki ba, ban san me zuciyata ta hango har tayi azarb'ab'in afkawa son ki ba, ni talaka ne kuma marayan da ya rasa uwa, sai dai ina fatan ki karb'e ni a ajin da nazo, na yi miki alk'awarin zama jarumi a soyayyarki, ta yanda zan zama bawanki wajen hidima da ke da hana ki hawaye, zan nuna wa duniya ina son ki, zan zama mai tausayinki da kyautata miki."

Duk da hakan sai na kasa magana, sai ma k'udundune kaina da na yi a cinyata hawayena yana gudun fita, ya rasa ya zai yi da ni, abubuwa biyu suka sake dakushe d'an ragowar kuzarinsa, kukan da nake yi da kuma rashin maganata. A haka Asiya ta shigo falon ta tarar da mu, sai kawai ta janyeni zuwa k'uryar d'akinta don jin ba'asin kukana. Na d'ago na dube ta na sharce hawayena ina jan hanci.
"Asiya kin san zan zo shi ne ku ka had'u ke da Muktar wajen gayyato mini jidali? Na tabbatar kin san k'udurina a kan karatu saboda me za ku sako shi cikin rayuwata domin yi mini karan tsaye?"

Asiya ta sauke numfashi tare da kallona ta ce,
"Ba ni da Muktar ne muka sako Ahmad cikin rayuwar ki ba. Allah ne ya sako shi, k'ila da nufin wata kyakkyawar alak'a da yake nufin k'ullata a tsakanin ku, Rahama tunda Ahmad ya d'ora idanuwa a kanki bai huta ba, har ta kai karatunsa da yake gab da kammalawa yana shirin samun matsala saboda fargabar tunkararki da batun, kodayake kin hasaso gaskiya wajen yunk'urin samar da had'uwarku a yau da muka yi, domin dai ki ji daga bakin Ahmad d'in, tunda an ce 'Wak'a a bakin mai ita ta fi dad'i."

"Karatu zan yi Asiya, ba aure zan yi ba." Na sake jaddada mata hakan idanuwana cikin nata.

"Karatu ba ya hana aure Rahama, kamar yadda aure ba ya haka karatu, koda Ahmad ya zo wa Muktar da zancen ki abinda Muktar ya fara sanar da shi, shi ne, batun kaiwa mak'ura da kika yi a son cigaba da karatu, Ahmad bai damu da hakan ba saboda ya bayyana ce wa zai iya jiranki har ki kammala, domin shi ma akwai abinda yake so ya cimma nan gaba kad'an kafin maganar aure."

Na yi shiru ina mayar da numfashi, ni dai ba zan ce ina son sa ba, kuma ba zan ce ba na son sa ba, hasalima ban tab'a samun kaina cikin yanayin da na samu a lokacin da yake furta mini kalmar so ba, maza dayawa da suka furta mini takaici nake ji har kamar na d'ora hannu a ka nayi ta ihu, domin zafin da nake ji a k'irjina, amma sab'ani wannan karon na samu kaina da bugawar zuciya ne, tare da raunin da ya mamaye ilahirin jikina har ya sabbaba mini fitar da hawaye daga k'oramar idanuna. Abin tambayar! Me hakan ke nufi?  Kafin na ba wa kaina amsa sai ga amsar ta fito daga bakin Asiya.

HAYATUL ƘADRI!Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon