HAYATUL ƘADRI! page 57-58

111 16 1
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 57-58

Yana riƙe da hannayena, kan cinyarsa kuma Muhibba ce a kwance, ya dube ni cikin tashin hankali ya ce.
"Mami ina da wata shawara."
Ni ma na kalle shi murya a sanyaye na ce.
"Wace irin shawara fa?"
Ya sauke ajiyar zuciya ya gyara wa Muhibba kwanciya, sannan ya ce.
"Akwai tarin damuwa da ɗaukar hakki idan na bar ki kika cigaba da zama cikin ɗakin nan, ɗakin ya gama ruɓewa, ya kamata na canja miki muhallin zama."
Na yi ɗan murmushi na ce.
"To yanzu ina kake tunanin za mu koma kenan?"
Ya ɗan ɗaga kai sama yana tunani, kafin ya sauke ya dube ni.
"Amm! Kin gane ko Mami, ni fa gabaɗaya zaman garin nan ne ma ya fita a kaina, duk da mahaifata ce, amma ina ji a jikina ya kamata mu bar garin nan gabaɗaya da zama, ko za mu samu sauyin rayuwa."
Na ɗan jim! Ina nazarin maganar shi, sai can na tanka masa.
"To yanzu idan mun bar nan ina za mu je? Kana da inda za mu koma ne?"
Ya ƙara damƙe hannuna yana matsawa, ya ƙura mini idanuwa ya ce.
"Mami ni da ina so mu koma can garinku Haɗejia da zama ne, idan ya so sai na nemi haya mu fara zama kafin Allah ya hore mini na fara gina nawa muhallin, ko ya kika gani?"
Sosai na ji daɗin abin da ya faɗa, domin ni kaina garin ya ishe ni, don dai kar na nuna gazawata ne, fuskata ɗauke da fara'a nace masa.
"Gaskiya na ji daɗin wannan maganar, to amma yanzu ta ina za mu fara?"
Shi ma ya saki murmushi ganin fara'ar da nake yi, ya ce.
"To ni Mami ai shawarar ki nake nema, ta ina kike ganin za mu ɓullowa abin?"
Na yi shiru na sunkuyar da kai ina tunani, wucewar minti ɗaya na ɗago kai muka haɗa idanu, ya sakar mini wani irin murmushi mai kyau wanda na ji tamkar na sumbace shi, na kawar da hakan a raina na ce.
"Abu mai sauƙi kawai ka yi magana da Mama, na san za ta ƙoƙarta mana ta ɓangaren ta a samu gidan da za mu zauna hayar."
"Kina ganin babu matsala hakan ya yi?" Ya tambaye ni yana sakin Numfashi.
Na gyaɗa kaina, "Sosai ma, babu wata matsala."
Ya yi 'yar dariya ya miƙa hannu yana ɗaukar wayar shi yana daddanawa.
"Bari ki gani Mami, da zafi-zafi akan bugi ƙarfe, kuma a bari ya huce shi ke kawo rabon wani, bari na ne mi Mama tun yanzu na sanar mata."
Ni ma na yi 'yar dariya idanuwana a kansa, wayar ta fara ringin, ya kai kunnensa a lokacin da Mama ta ɗaga kiran.
Ina ji suka gaisa, yana ta kwantar da kai cikin tsananin ladabi domin ganin girman iyayena da yake yi, bayan sun gama gaisawa ya shigo mata da zancen tare da sanar da ita shawarar da muka yanke.
Mama ta ce "Wannan abu ne mai kyau, Allah ya tabbatar da alheri, amma shin ka shawarci mahaifinka a kan maganar? Yana da kyau yasan hakan saboda yana da hakki a kanka."
Cikin ladabi ya ce, "A'a Mama ban faɗa masa ba, amma zan faɗa masa domin na ji abin da zai ce."
Mama ta ce, "Yauwa hakan na da kyau, idan muka ji matsayar shi sai a san abin yi a gaba ko?"
Ya ce, "Haka ne Mama, na gode Allah ya ƙara girma."
Ta ce, "Amin ya ALLAH, a gaishe mini da Muhibba da mamanta."
Cikin murmushi ya gyaɗa kai tamkar tana ganin shi yana shafa kan Muhibban.
"Za su ji da kyau Mama."
Ya sauke wayar yana dubana, muka yi murmushi, dayake na ji dukkanin tattaunawar su sai na ɗora nawa bayanin ba tare da na bari ya fara magana ba.
"Ka san me? Mama tana da gaskiya, kuma ta hango abin da bamu hango ba. Ya kamata a nemi shawarar Baba ba wai mu yanke hukunci kaitsaye ba."
Ya sauke numfashi ya ce.
"Ba ki ji an ce yaro ko ya hau bishiyar rimi ba zai hango abin da babba ya hango ba, tabbas Mama ta yi hangen nesa, kuma zuwa anjima zan samu Baba da maganar in sha ALLAH."
Na gyaɗa kai, ina shirin magana Muhibba ta fara mutsu-mutsu tana buɗe idanuwa ta farka daga bacci, ya saki murmushi ya ɗagota yana mata miƙa yana salati, sai kuma ya waiwayo ya kama rigata yana faman ja zai ɗagata sama yana faɗin.
"Mami oya! Mun tashi daga bacci a zo a bamu abincin mu."
Na saki murmushi ina masa hararar wasa, shi kam sai tura hannu yake cikin rigata domin ya kamo abincin Muhibba.

*******

Da ya samu Baba da maganar sai Baban bai nuna ƙin amincewa ba, illa ma addu'a da fatan alheri da ya yi, saboda Baba mutum ne mai matuƙar haƙuri da kawar da kai, kusan halayen shi Ahmad ya kwaso gabaɗaya. Sosai muka yi farinciki da goyon bayan da Baba ya bamu.

HAYATUL ƘADRI!जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें