HAYATUL ƘADRI page 87-88

153 20 1
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 87-88

*KU YI HAƘURI DA RASHIN JI NA KWANA BIYU, HAKAN YA FARU SAKAMAKON RASHIN LAFIYA DA NA YI, AMMA YANZU ALHAMDULILLAH YAU NA ƊAN JI DAMA-DAMA HAKAN YA SA NA WAIWAYOKU, SANNAN KUMA KUN SAN ASKI IDAN YA ZO GABAN GOSHI YA FI ZAFI, INA GODIYA DA ADDU'O'I DA FATAN ALHERIN DA KUKE MINI, DA BAZARKU NAKE TAKA RAWA MASOYANA, ALLAH YA SAKA DA ALHERI YA BAR ZUMUNCI. NA GODE SOSAI.*

Salon da ta ɗauka shi ne rage kuɗin cefene da yin girki mara daɗi, kwata-kwata bata san ta yi girki mai daɗi wanda zai gamsar da miji ya gamsar da mu gabaɗaya ba, ko miya ba ta yi sai dai ta dafa shinkafa fara ta soya mai ta daka yaji, ashe a wannan ɓangaren ma da ha'incin da take yi.

Mustafa yana da hali don bai rage mu da komai ba, kuɗin cefanen da yake bamu mai kauri ne ta yadda za ki sarrafa abinci mai inganci da daɗi, amma Shamsiyya kullum sai dai ta girka fara da mai ko wake da shinkafa, zai zage ya bayar da kuɗin cefane na ban mamaki amma ba za ta yi amfani da su ba sai dai ta ɓoye ta yi abinci garau-garau.

Ni kuma a daidai wannan lokaci na fito da nawa salon yin ƙayatattun girkuna wanda kunne zai yi motsi. Watarana a ranar girkina na girka jallop na dankalin turawa da kayan ciki, Mustafa ya ji daɗin girkin nan, ya riƙa yaba mini yana koɗa girkin.

Da safe idan ranar girkinta ne sai dai wai a siyo awara ta ɗari biyar, ta sanya a gaba tai ta danƙara ita da yaranta, ga kayan shayi amma ba za ta tashi ta haɗa ba, awarar ma idan an siyo a haka za a ci ba a sarrafata launi kala-kala don ta yi armashi.

Ni kuwa rana ɗaya na bayar aka sayo awarar ɗanya, nai mata wata irin suya mai ƙwai da attaruhu da albasa na dagargaza kamar dambu, tun kafin na kammala Mustafa ke leƙoni a ktcheen saboda ƙamshi ya cika masa ciki, faɗi yake.

"Jannat don Allah hanzarta mana, kar ƙamshin nan ya sumar da ni ban ji ɗanɗanon a bakina ba."

Dariya na riƙa yi masa, da na kammala kuwa ya ci sosai yana santi, sai ya zamana cikin shi ya buɗe. Alla-alla yake yi ranar girkina ta zagayo domin ya ci girkina, wai duk fa ina waɗannan abubuwan ne domin Shamsiyya ta gani ta koya, amma ina, gabaɗaya ta runtse idanuwanta.

Duk da ina laulayi haka nake dagewa na yi masa duk wani abu da yake buƙata, na ƙalƙale muhallina da jikina tare da yi masa girki na garari, da lemuka masu daɗi da ƙara kuzari, domin ba na barin shi siyan lemuka na kanti, nakan zage na haɗa masa nagartattu masu ƙara lafiya, Zoɓo, ginger, kunun aya, duk babu wanda ba na yi da sauransu.

Sai ga Shamsiyya ita ma ta baje ciki tana kwasar girki, idan na zuba mata ko loma guda ba ta ragewa sai dai na ga tana siɗar hannu saboda daɗi. Sosai na ƙara dagewa da yin girkuna masu daɗi, don na lura ita ko irin su normal pride rice ɗin nan da za a saka su green beans da carrot  ba ta iya ba, sai dai caɓaɓɓiyar dafaduka, da har ta fara kishi idan na girka abinci mai daɗi sai taƙi ci wai ta ƙoshi, daga baya da taga cutar kanta take yi sai ta zage take kila ta ci ta yi ƙat.

Ta rasa ya za ta yi da ni ta wannan ɓangaren, to a lokacin ina zaunar da 'ya'yanta na koya musu karatu, ta jima bata tayar da aljanun ƙarya ba amma a lokacin sai ga shi ta tayar, wai lallai sai na daina koyawa yaran karatun da nake koya musu.

Ni kuwa nai tsalle na dire na ce, "Wallahi baku isa ba, karatu ya zama dole na koya musu domin 'ya'ya na kowa ne."

Mustafa da kansa ya fuskanci tana rage kuɗin cefane, saboda a baya kafin ya auro ni bai taɓa lura da hakan ba, amma bayan ya auro ni ya ga yadda nake kashe kuɗi a fannin girki na yi mai daɗi, kuma dai ya san ba wata sana'a nake ba balle yace a kuɗin sana'ata nake ƙarawa, gara ma ita tana sayar da pure water leda leda, amma duk da hakan nawa girkin ya zarta nata nesa ba kusa ba. Da ya fuskanci hakan sai yake tambayata watarana.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now