HAYATUL ƘADRI! page 25-26

126 14 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 25-26

*Ina kuke y'an k'walisa? Ina masu son birgewa da sutturu na kece raini da do? kuna ina masu sayan d'ai-d'ai ko sari? To ku marmatso ga damarku ta samu, Shahararren kamfanin nan mai suna D'AN LARABAWA INVESTMENT ya zo muku da kayayyaki masu sauk'in farashi da kyau na ban mamaki, kayan mu sun had'a da Atamfofi, laces, shadda, matrials, mayafai, hijabai, takalma da jakunkuna, sark'ok'i, dogwayen riguna, kayan ktcheen, kayan bacci, akwatuna, zannuwan gado, da sauran kayayyakin ado na mata da maza, ga duk mai buk'atar kayanmu zai iya nemana ta lambar waya ko kuma ya shiga wannan group da ake tura kayan a kan farashi mai rahusa, muna turawa costomers kaya a duk inda suke a fad'in Nigeria har ma k'asashen k'etare da yardar Allah👍🥰💃🏻 sayan na gari maida kud'i gida, ku shigo ku kwashi garab'asar kayanmu kuma ku tallata ku samu rabonku na alheri, ga masu sayan d'aya ko sari za ku iya neman HASSANA D'AN LARABAWA A KAN NUMBARTA TA WATSAPP KAMAR HAKA👇*

08080049548

*Ko kuma kai tsaye ku shiga group d'in D'ANLARABAWA INVESTMENT ta wannan link d'in 👇*

https://chat.whatsapp.com/H42ARTX76x3Ku4pRKbFHW6

Sai kun zo 💃🏻🥰👏

Ta mik'e tsaye tana kallona.
"Muje ki nuna mini inda suke."
Na mik'e a hankali k'afafuwana na hard'ewa na wuce na yi gaba ta biyo ni a baya har muka shiga ktcheen d'in, na waiwayo na kalleta tare da nuna mata tulin kayan da ke zube, irin su, shinkafa; taliya; macaroni; semonvita; kus-kus; mai; maggi; da duk wasu kayayyaki na gara da ake kaiwa mace.
Yaya Atika ta sauke mayafinta k'asa ta ci d'amara da shi kamar wadda za ta yi aikin k'arfi, sannan ta dumama hannu kan kayan ta rik'a jida son ranta, komai sai da ta d'iba babu abin da ta bari, ta ware su a gefe ta fita tare da tattaro yaran da ke gidan suka dawo ina tsaye ina kallon ikon Allah, domin a al'adar garin ba a raba kayan gara, ango da amarya kawai ake barwa, yaran suka gaishe ni na amsa cikin sakin fuska domin ni ina da son yara, ta nuna musu kayan suka rik'a jida suna fitar mata da su babban tsakar gidan, har suka kammala gabad'aya. A lokacin ne ta juyo ta dube ni ta ce.
"To ni zan tafi, idan ya dawo ki sanar da shi na wuce sai kuma gani na biyu."
Na yi murmushin yak'e na d'an rusuna.
"To Yaya Atika ki gaida gida, Allah ya tsare hanya."
Ta amsa da "Ameen." Tana kwance d'amarar mayafinta ta yafa, sannan ta kwashi sauri buguzun-buguzun ta fita, na bita da kallo ina sauke numfashi.
Na jima tsaye a ktcheen d'in ina ta sak'e-sak'e, har dai na gaji da tsayuwar na ja sagaggun diga-digaina na fito na tsaya a kewayen nawa ina hango k'ofar fita, a lokacin ne na hango yadda yaran gidan ke fitar wa da Yaya Atika kayan da ta d'iba zuwa waje, alamu sun nuna tafiya za ta yi da su kenan, ba batun rabawa dangin miji da tace, tunda dangin mijin ai suna cikin gidan.
Da naga babu amfanin tsayawa tunane-tunane a kan abin da ya riga ya faru, sai kawai na wuce falona na yi kwanciyata kan kujera, na lumshe idanu ina tuna kalolin soyayyar da Ahmad ya nuna mini a daren jiya.
Can wurin wucewar awa d'aya da tafiyar Yaya Atika sai ga shi ya shigo, lokacin har bacci ya fara d'aukata, na d'an bud'e idanu kad'an ina duban shi, da muka had'a ido sai ya yi saurin sunkuyar da kai, ya juya ya fita ina jin sa ya shiga ktcheen d'in, ko kayan garar ya duba oho! Ya dai jima kafin ya dawo falon ya samu wuri ya zauna, sai k'asa da kai yake yi alamun jin kunyata, don ya kasa had'a idanuwa da ni.
To haka dai zamana ya fara mik'awa, a farkon zuwana ban san kan jama'ar gidan ba, tunda ba zan iya ware masoyana da mak'iyana ba dalilin ban d'auki lokaci da su ba, shi yasa na sakawa kowa idanu don na gane takun kowa kuma na nak'alci yadda zan zauna da su. Tsakanina da mijina kuwa sai son barka, soyayya har da ta fitina nuna mini ita yake yi, kullum yana tare da ni ba ya barina na samu kaina cikin kewa, idan kulawa na yiwa mutum yawa ni dai a wannan lokaci zan iya cewa tayi mini yawa, domin Ahmad yana riritani fiye da zato ko tsammani. Sai dai har zuwa lokacin da na kwana bakwai cif a gidan  babu wani abu da ya shiga tsakanina da shi ta hanyar auratayya, sai dai fa soyayya babu kalar wadda ba ma yi, tun ina tsananin kunyarsa har na rage ni ma na fara zama y'ar gari, idan yana mini abubuwa ba na sanin lokacin da nake mayar masa da raddi, Ahmad ya yi mini sabon da ko kusa ba na son na bud'e idanu na ga ba ya kusa da ni, a take nake jin kewarsa ta mamaye ruhina da gangar jikina, ba ni da wurin kwanciya sai jikinsa, muna shak'ar k'amshin juna da tarairayar juna.
Idan dare ya yi a nan al'amarin yake rincab'ewa, domin iya yin sa ba ya samu ya shige ni saboda wata irin k'aramar k'ofa da Allah ya halitta mini, haka zai ta lalubensa da bidirinsa ya sha kuka ya gode Allah amma babu damar yi, duk iya k'ok'arinsa kuwa, musamman idan yaga ina kukan azaba saboda dannawar da yake yi don ya samu ya shiga, haka zai hak'ura ya rungumeni kawai muyi bacci.
A kwana na takwas ne Allah ya bawa Ahmad nasarar jefa k'wallo cikin raga, sai dai mun sha bak'ar wahalar da sai da muka kusa suma daga ni har shi, biji-biji ya yi mini, hak'urinsa na tsawon lokaci ya tattaro ya yi aiki da shi a wannan ranar, bayan komai ya lafa ne kuma da kansa ya rik'a hidimar d'ora ruwan zafi ya gasa mini jikina da k'asana sosai, muka yi wankan tsarki a tare ni da shi, sannan ya d'auko ni cak saboda tafiya ma kasawa na yi, da na mik'e sai k'afafuwana su kama rawa.
Bayan mun yi sallar Asuba ina rungume a jikinsa yana ta ba ni kulawa da tarairaya kamar ya lashe ni, daga ni har shi jikinmu zafi rau kamar wad'anda zazzab'in soyayya ya kama, muna kwance lamo yana ta karanta mini kalaman k'auna, a yayin da nake jin mak'urar tuk'ewar so da k'aunarsa na baibaye jinin jikina, ban tab'a jin so da d'okin kasancewa tare da shi kamar lokacin ba.
Wayarsa da tayi k'ara ta d'auki hankalinmu, ya d'an yi tsaki yana k'ara nutsa kaina a tsakiyar k'irjinsa, ya yi magana a hankali.
"Waye da asubar nan zai shiga rayuwarmu?"
Wayar ta ci gaba da k'ara ba tare da ya d'auka ba har ta katse, aka sake kira, a lokacin ne na yi magana a hankali.
"Ka d'aga mana, baka sani ba ko wani abu ne mai muhimmanci, waye yake kiran ne?"
Ya shafa kaina yana tura yatsansa cikin kunnena yana mini tafiyar tsutsa, na sauke numfashi ina sake k'ank'ame shi saboda yadda nake jin wani zir-zir a ilahirin jikina, can na tsinto muryarsa yana ce wa.
"Ni ban ma duba mai kiran ba Mamina, amma bari na duba."
Ya kai hannu ya d'auko wayar da ke gefen gadon, ya kai idanu kanta a dai dai lokacin da take shirin katsewa, a zabure ya mik'e zaune da ni a jikinsa har yana fama mini mik'in da ke jikina, na runtse idanu tare da cije baki da fad'in.
"Wash! Wayyo Allah na."
Jikinsa na rawa sosai ya k'ara mak'aloni jikinsa yana mini sannu, sai kuma ya mayar da hankali kan wayar ya yi maganar zuci wadda ta fito fili.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Ashe Hajiya ce take kira ban d'aga ba."
Ya fara k'ok'arin kiran lambar saboda ta katse a karo na biyu, na tsura masa idanu ina kallon yadda ya gigice sosai, a haka wayar tasa ta kuma d'aukan k'ara, da hanzari ya cire ni a jikinsa ya matsa gefe ya d'aga wayar cikin matuk'ar girmamawa da sanyin murya ya fara magana.
"Hajiya barka da asuba, ina kwana? An tashi lafiya?"
Dayake muna dab da juna kuma sifikar wayarsa tana da k'ara ina jiyo abin da take ce wa, wadda muryarta ta nuna cikin fad'a take amsawa.
"Idan ban tashi lafiya ba zan samu damar kiranka ne? Saboda baka da mutunci shi ne tun d'azu ina kiran ka kana jefa kiran nawa a kwandon shara ko?"
"Ba na kusa ne Hajiya, don Allah kiyi hak'uri." Ya ambata cikin ladabi da rawar murya.
A harzuk'e ta ce "Kai yi mini shiru da Allah, mak'aryaci kawai, kana tare da wannan figaggiyar yarinyar ta ina za ka saurari kirana, to yanzu ma na kirawo ka ne na shaida maka cewa, billahillazi ban amince ka k'ara ko da awa uku cikin wannan garin ba, ka had'a yanaka-yanaka yanzun nan ka kama hanyar Abuja."
Cikin tashin hankali ya dafe k'irji ya ce "Hajiya don Allah kiyi hak'uri, yau kwana tara ne kacal da zuwan Rahama garin nan, bata san kowa ba, bata saba da kowa ba, sai ni kad'ai, idan na tafi na barta a wannan yanayin za ta sha wahala ne, don Allah kiyi hak'uri da wannan hukuncin Hajiya."
Kamar za ta fasa wayar haka ta taso masa da fad'a.
"Wallahi ka ji na rantse maka tilas ka kama hanyar Abuja a yau d'in nan, ka tafi ka nemi kud'i, da ka zauna kana manne da ita soyayyar za ka ba ta ta ci ta k'oshi? Batun bata san kowa ba ai aure ta zo yi, don haka ko ta saba ko kar ta saba wannan ruwanta ne, amma ina tabbatar maka idan ka sake ka k'etare umarnina wallahi sai ka yabawa aya zak'inta."
K'it! ta katse wayar ta bar shi da waya a kunne ya saki baki cikin matuk'ar tashin hankali, a haka wayar hannunsa ta zame ta fad'i k'asa saboda yadda jikinsa ya yi matuk'ar sanyi, kawai sai ya had'a kai da guiwa yana sauke wani wahallalen numfashi.
Na janyo jikina da ke mini ciwo na matso gare shi, na sanya hannu na d'ago kansa, zaro idanuwa na yi da naga hawaye na fita ta cikin idanuwansa, cikin gigita na yi magana.
"Lafiya? Me ya sa kake kuka ne? Wai wace ce Hajiyar nan ne?"
A maimakon ya ba ni amsa kawai sai ya fashe da kuka tare da janyo ni jikinsa ya rungume ni, mun jima a haka hawayensa na sauka saman k'irjina har ni ma zuciyata tayi rauni na fara hawayen, sai lokacin ya d'ago ya goge mini fuskata, yayi magana cikin shak'ak'k'iyar murya.
"Kiyi hak'uri Mamina, don Allah ki yafe mini saboda zan koma Abuja a yau."
Gabana ya yanke ya fad'i, amma ban nuna masa ba sai dai na k'ura masa ido ina kallonsa, ya ci gaba da ce wa.
"Yau ce ranar da na d'ora miki wani nauyi wanda ya kamata a ce na tsaya na lura da ke tare da ba ki kulawar da ta cancanta, sai dai ina so ki mini uzuri Mami, banda shingen da aka saka mini tsakanina da ke a yanzu babu mai raba ni da ke."
Na yi shiru duk jikina a sanyaye, ba na k'aunar rabuwa da shi ko kad'an, Abuja ba nan ba ce don ban san yaushe zai dawo ba, ganin na yi shiru sai ya sake k'ank'ameni har lokacin yana hawaye, yana mini magana cike da rauni.
"Ni kuma k'addarata kenan, ta inda aka jarrabe ni kenan Mami."
Tausayinsa sosai ya kama ni, na kai hannu ina share masa hawaye, ya rik'e hannun nawa yana ta kallona yana sakin ajiyar zuciya, na d'an yi murmushin da nasan zai kawar masa da damuwa na zame hannuna na kai kan fuskar shi ina shafa dogon hancin shi.
"To yanzu don Allah kukan na mene ne, kana namiji kana kuka haka?"
Ya tsura mini ido ya girgiza kai ya ce.
"Kukan abubuwa biyu Mamina, ina kuka ne a kan zaluncin da zan miki na tafiya in barki a wannan yanayin da ya kamata a ce na zauna na lura da ke saboda nauyin da na d'ora miki, sai kuma kukan ba zan iya yiwa Hajiya musu ba, ya zame mini dole na cika duk umarnin da ta gindaya mini."
"Wace ce Hajiya." Na sake tambayar shi.
Ya sauke numfashi ya ce.
"D'auki Hajiya ki sanyata a gurbin da mahaifiyata ta bari, kamar yadda ba zan iya ja da mahaifiyata ba da tana raye, ita ma ba zan iya ja da ita ba."
Tun daga nan na fara fahimtar karatun, duk da ban fahimta gabad'aya ba amma na d'auki haske, zan so dai na k'ara samun bayani a kan wannan Hajiyar.
Na ba shi k'warin guiwa wurin ambata masa yardata kan tafiyar shi.
"Kar ka damu da ni, zan iya yiwa kaina komai ko da ba ka nan, kawai ka sanya a ranka duk inda kake ina tare da kai, kaima duk inda nake kana tare da ni, a yadda na fahimta Hajiya tana da matuk'ar muhimmanci a wurin ka, don haka zan taya ka domin nuna biyayya a gare ta, tashi ka shirya."

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now