HAYATUL ƘADRI! page 63-64

104 24 2
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 63-64

*NA SAN DA YAWANKU FEJIN JIYA YA ƊAGA MUKU HANKAKI HAR WASU SUN ZUBAR SA HAWAYE, BAN SAN YA ZANCE MUKU BA, AMMA WALLAHI AKWAI ABUBUWA DA YAWA DA BA'A AMBATA BA MA A WANNAN LABARIN, SABODA GUDUN TAYAR MUKU DA HANKALI, KAMAR YADDA WASU SUKE FAƊIN SUNA CIKIN TSANANIN FARGABA A DUK LOKACIN DA ZA SU KARANTA, INA SON SANAR MUKU SHI FA WANNAN LABARI TUNI YA FARU, DUK ABIN DA ZA KU JI YA RIGA YA FARU TARIHI JARUMAR KE BA NI NI KUMA INA ISAR MUKU DA SHI, WANI ABU DA NAKE SON KU FUSKANTA A FEJIN JIYA SHI NE: KU TUNA RAHAMA TUN TANA ƘANƘANUWARTA BABU ABIN DA TA TSANA IRIN SAKIN AURE, TANA JIN TAKAICI IDAN NAMIJI YA SAKI MACE, TO SAI GA SHI AN JARRABETA DA ABIN DA TA FI TSANA WATO SAKI, KUMA SAKIN MA HAR GUDA UKU WANDA YA RABATA DA ABIN DA TAKE SO HAIHATA-HAIHATA, BAYAN JARRABOBI DA ƘADDARORI DA SUKA SARƘAFE RAYUWAR AURENTA, SAI KUMA GA BABBAR ƘADDARA TA RISKETA, SHIN RAHAMA ZA TA CIGABA DA HAƘURI DA KARƁAR ƘADDARAR DA KE BIBIYARTA NE? KO KUMA ZA TA NUNA GAZAWARTA A KAN HAKAN? YA KAMATA MU CIGABA DA BIN LABARINTA DOMIN SANIN ME ZAI FARU DA RAYUWARTA A GABA, RAYUWAR DA BABU AHMAD A CIKINTA. NA GODE MASOYANA, RAHAMA MA TA GODE DA FATAN ALHERINKU GARE TA, KU CIGABA DA BIBIYATA HAR ZUWA LOKACIN DA YA KAMATA MU ƘARƘARE.*

Mama kawai ta ganni afujajan ne, hajaran majaran da ni kamar wadda aka wurgo. Ta tarbeni a tsorace ganina a yamutse ba yadda ta saba ganina ba, ban yi nauyin baki a wannan lokacin ba, illa buɗe baki da na yi na zayyane mata dukkan abin da ya faru kafin barowata daga gidan, ban ɓoye mata komai ba, dayake Mama ta ruɗe sosai sai ta fahimci maganata a bai-bai, ta za ci rama zagin da ya yi mini shi ne musababbin sakin da ya shiga tsakanina da shi, wanda ni kuma billahillazi sai bayan ya sake ni na ji zuciyata ta kasa jure wannan zagi har bakina ya kasa haƙuri na rama.
Ban san Mama da yawan fushi ba, amma a ranar sai idanuwanta suka rufe, ta shiga zazzaga mini faɗa tamkar ta kai mini duka.
"Ban taɓa sanin ba ki da hankali da tunani ba sai yau, ilimin ki bai amfana miki komai ba Rahama, wa ya faɗa miki ana mayarwa da miji magana? Mijin auren naki za ki buɗe baki ki zaga? Saboda ba ki da kirki?"
Mama ta cigaba da zazzaga mini faɗa, ina zaune da Muhibba kan cinyata na rasa abin da ke mini daɗi, a ƙoƙarina na fahimtar da ita sai ALLAH ya jeho Abba a yammacin ya dawo gida. Ya zo ya tarar da abin da ke faruwa, ba zan iya kwatanta muku tashin hankalin da Abba ya shiga ba, domin shi bai san komai kan rayuwar da na yi gidan aure ba, bai san haƙurin da na yi ba, bai san juriyar da na yi ba, a dalilin hakan ya yi fushi da ni irin wanda bai taɓa yi ba, yana tunanin ni na wulaƙanta mijina na zage shi har ya sake ni, inda Abba ya yi furucin tunda na kashe aurena sai na bar masa gidansa, ba zai karɓeni ba ko ma ina ne in tafi.
"Wallahi Rahama sai kin bar gidan nan a yanzu, tashi ki fita tun kafin na aikata miki abin da zuciyata ke ba ni umarni a kai, tunda har kika kasa haƙurin zama da wannan yaro mai matuƙar hankali da sanin ya kamata da haƙuri da tsananin zurfin ciki, amma ba ki iya haƙurin zama da shi ba, to wallahi sai kin bar gidan nan."
A tsugune nake gaban Abba, amma ina ji a raina ina ma ƙasar da ke wurin ta tsage kawai na shige a binne ni, wannan shi ake kira 'Rana zafi, inuwa ƙuna.' Wannan wace irin ƙaddara ce ke bibiyar rayuwata.
Yadda Abba yake ta faɗa yana nanata cewa in tashi in fita, haka jikina ke rawa ina neman rasa tunanina, Mama na zaune kanzil bata ce ba, takaici ne da tsantsar baƙincikin mutuwar aurena ke damun zuciyarta. Haka na miƙe cike da dauriya, na ɗauki Muhibba na saɓata a bayana na goyata, na fice daga gidanmu ban san inda nake saka ƙafata ba.
Na yi tafiya mai nisan gaske ba tare da ina bambance abubuwan da nake wucewa ba, ƙofar wani gida na samu na zauna, ina kallon wucewar mutane kowa yana sabgar shi, duk macen da za ta zo wucewa haka nake bin ta da kallo, ina ƙissima wace irin rayuwa take gudanarwa a gidan mijinta? Shin ita ma tana fuskantar ƙalubale? Shin daman haka mata suke shan wahala a gidan aure? Amma duk da hakan kuma Manzon ALLAH ya faɗa daga bakinsa da ba ya ƙarya cewa mata sun fi maza yawa a wutar jahannama, to shin me yake kai mata wuta? A take zuciyata ta ba ni amsa da cewa 'Rashin haƙuri da biyayya ga miji.' To idan haka ne kuwa ina saka rai da samun aljanna, domin na yi haƙuri, kuma na yi biyayyar aure.
Duk abubuwan da suka faru sai nake ganinsu tamkar a mafarki, so nake kawai na farka, amma da alamun ba mafarkin nake ba da gaske komai ya wanzu tamkar a majigin kallo, komai ya cushe mini, hawayen ma yaƙi zubowa bare na ji sanyi a raina.
Ina nan zaune masu wucewa na kallona, suna mini kallon almajira, har dare ya riskeni ina tunanin inda zan tafi, sai wajen sha ɗaya saura na dare na samu tunanina ya canko mini zuwa gidan Antina wato Anti Zulaiha.
Na ƙara saɓar jaka da goyon Muhibba a bayana, na riƙa cilla ƙafafuwa cike da tashin hankali, addu'a bata bar bakina ba, ambaton ALLAH bai bar kan harshena ba, ina ta roƙon ALLAH ya bayyana wa iyayena gaskiya, sannan ya cire mini damuwar mutuwar aurena, ya kuma cire mini tunanin Ahmad tunda komai ya ƙare a tsakanina da shi.
A haka na isa gidan Anti, wadda mijinta ma'aikaci ne shi ma yakan kwana uku a wurin aiki ko ma huɗu, lokacin dare ya fara yi sosai, na bubbuga ƙofar, na jima ina bugawa sannan na jiyo muryarya tana tambayar wane ne?
Da muryata da take a dakushe na amsa mata da ce wa.
"Ni ce Anti. Rahama ce."
Na jiyo takunta da sauri, ta buɗe ƙofar a yayin da take bi na da kallon mamakin dalilin zuwana a wannan dare, ta karɓi jakar hannuna muka shige ciki bayan ta mayar da ƙofar ta kulle.
A falonta muka yi masauki. Ina niyyar magana ta tare ni da tambaya.
"Rahama ya aka yi? Lafiya kuwa?"
Na girgiza kai na kwance goyon Muhibba, ta karɓeta a lokacin da na ba ta amsa da ce wa.
"Babu komai Anti, kina da abinci kuwa? Yunwa nake ji."
Ta gyara wa Muhibba kwanciya tana faɗin.
"Eh akwai abinci, kin yi sa'a wallahi, don da tuni na ba wa almajiri saboda na san ya yi mini yawa, ga mai gidan ba ya nan, je ki ktcheen ki ɗauko."
Na yunƙura na tashi na nuf ktcheen na zubo abincin, na dawo na zauna a nutse na yi bisimillah na fara ci, Anti dai sai bi na da kallo take, na gama ci tsaf na fita da kwanon, daga nan ɗauro alwala na gabatar da sallar magariba da isha'i da suka tsere mini.
Bayan na idar na yi addu'o'ina, sannan na raɓa kusa da Muhibba na  kwanta, Anti ma tana daga kwance daga gefe, sai a lokacin na sauke ajiyar zuciya na yi magana.
"Anti kin me ya faru kuwa?"
Ta gyara kwanciya ta ce.
"A'a, ban sani ba."
Na ce, "Hmmm! Mun fa rabu da Baban Hibba Anti."
Sai ga ta zaune kamar wadda aka fizga daga kwance, cikin matuƙar tsoro baki na rawa ta ce.
"Kun rabu? Ban gane ba? Me kike nufi ne?"
Ta jero mini tambayoyi, na runtse idanu sosai murya na rawa na ce.
"Ya sake ni Anti, Baban Muhibba ya sake ni har saki uku."
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un...!
Kalmar da ta fito daga bakinta kenan tana riƙe da kanta da alamun ya yi mata nauyi sakamakon jin kalamaina. Ta matso gare ni tana roƙoni a rikice tana faɗin.
"Ke Rahama ba na son wasa, wane irin saki kuma? Idan kowane namiji zai saki matar shi ba na tunanin Ahmad yana cikin waɗannan jerin mazan, saboda masifaffiyar soyayyar da ke tsakaninku."
Na girgiza kai, saboda na ga Anti ta tsorata, kuma ta ɗauki abin tamkar wasa ma, sai na yi mata ta mahaukaci don ta fi yarda, na kwaso rantsuwa na haɗa da kalaman bakina na furta.
"Wallahii azeem Anti mun rabu, na rantse miki da ALLAH Baban Muhibba ya sake ni a yau."
Ban tsaya nan ba sai da na kwashe labarin abin da ya faru tsaf na faɗa mata, sai ga Anti tana kuka hawaye na tsiyaya kamar famfo, ta shiga matsanancin tashin hankali, ni kuma tuni zuciyata ta ƙeƙashe ma, babu alamun kuka a tare da ni, na samu salama da yayewar ƙunci a raina.
Tausayina ya saka Anti kuka sosai, har ma ta dakatar da ni daga ba ta labarin da faɗin.
"Kwanta ki huta Rahama, da safe ma ƙarasa labarin."
Na zuba mata idanu na ce,
"To Anti."
Ta gyara mini shimfiɗa na kwanta ina rungume da Muhibba, cikin ikon ALLAH sai ga wani irin bacci mai masifar daɗi ya ɗaukeni, wanda na jima ban yi irin shi ba, ita kuwa Anti ba ta samu barcin ba, kwana tayi ba ta runtsa ba azabar tunani ya cika ranta, har mamakin barcin da na shaƙa ta yi, ita kuwa ta kasa, na gane hakan ne a lokacin da safiya ta yi na ga idanuwanta sun kumbura alamun ba ta samu barci ba.

*******

Ban tashi da ƙunci ba a washegarin, illa muguwar ramar da na tafka cikin kwana ɗaya tal da faruwar babban lamarin, ina gidan Antin sai ga Abbanmu ya zo har gidan ya same ni, saboda ya san cewar ina gidan dalilin sun yi waya da Anti.
Har cikin gidan ya shigo, ina tsugune a gabansa kaina a ƙasa a lokacin da Abba ke ce min.
"Daren jiya ban yi bacci ba, saboda duk uba ba zai aurar da ɗiyar shi a sako masa ita ya ji daɗi ba, ko kaɗan ban ji daɗin abin da ya faru ba Rahama, sai dai babu yanda na iya."
Ya ɗan yi shiru yana sauke numfashi, sannan ya ɗora da ce wa.
"Na yi waya da mahaifin mijin naki, a yadda yake faɗa mini babu wani batun saki a tsakanin ki da ɗan shi, sai dai ya tabbatar mini kun samu matsala har ma ya yi miki faɗa, amma babu batun saki, don haka ya ce zai sako Ahmad ɗin a gaba su zo domin a tattauna batun, yanzu ina so ki tattara ki koma can gida wajen Mamanku kafin su zo a san abin yi."

Sauraren Abba kawai nake yi, har ya gama ya tafi yana nanata mini na tashi na koma gida, sai bayan ya tafi na riƙa kuka, saboda ji na yi ba ma na son komawa gidan namu, saboda korar da aka yi mini, sai dai na san su iyaye ba a fushi da su, kuma sun aikata abu cikin rashin sani ne, wanda a kaso ɗari na rayuwar aurena basu san kashi casa'in ba, kashi goma kawai suka sani.
Anti ta riƙa rarrashina da lallaɓani, haka na tattara na bar gidanta na koma gidanmu, na cigaba da zama tsawon kwana goma, amma babu mahaifin Ahmad babu Ahmad, ina rayuwar ne kawai amma ba cikin jin daɗi ba, ban rasa ci ba, ban rasa sha ba, haka nan ban rasa wurin kwana ba, sai dai kuma babu mai yi da ni, hatta mahaifiyata da mahaifina har lokacin suna ganin baƙina, babu wanda zan gayawa damuwata na ji sanyi, kullum ina ɗaki tare da Muhibba a jikina, wadda nake matuƙar tausayamata domin na san mahaifinta ba ya yi da ita, tana cikin kwana na tamanin da uku da zuwa duniya ya sakeni.
Ban sake saka shi a idanuwana ba, nan na ƙara tabbatar da Ahmad ya shafe babina a tarihin rayuwarsa, kamar yadda ni ma na shafe nasa babin a tawa rayuwar, su iyayena gani suke ai ban faɗi daidai ba, babu wani saki a tsakanina da shi har guda  uku, suna jira ya zo a daidaita ne kawai.
Sai bayan kwana goma sha shida sannan suka zo da shi da mahaifinsa, basu samu Abba ba, sai kawuna da suka tattauna da shi, a nan wurin Ahmad ya sake maimaita cewar ya sakeni saki uku da gaske, babu wata alamar nadama a tare da  shi.
Haka suka juya, bai nemi Muhibba ba balle ya ganta, ya ma manta da ita.
Iyayena suka ƙara shiga tashin hankali da wannan batu, don sai a lokacin ne ma na san cewar a ranar da aka yi sakin Mama ta tura da motar masu kwaso kaya domin su kwaso furnitures ɗina a jera a gidan da aka kama mana haya, ganin kullum tana mini maganar naƙi mayar da hankali, shi ya sa ta tura su domin suyi mini bazata, sun tafi kenan ni kuma sai ga shi na zo da maganar saki, mun yi saɓani da su kenan.
Da dai aka fahimci saki uku ya tabbata tsakanina da shi, tunda ya sake maimaitawa da bakin shi cewar ya sake ni, sai muka shirya har da ni muka nufi garin domin a kwaso kayana.
A ranar na ga tashin hankali, ban san ina da tarin masoya a garin  ba sai da muka je ɗauko kaya, wallahi gidan cika ya yi da jama'a ana alhini, masu kuka suna yi, masu tsine wa Ahmad suna yi, masu tausaya mini suna yi, daga gefe kuma maƙiyana suna tasu murnar.
Umman Fati ta yi kuka tamkar idanuwanta za su zagwanye, ta yi baƙinciki,, haka kuma ta tausaya mana daga ni har shi, domin tana da masaniyar an cutar da mu.

Muka dawo gida, a wannan ƙadamin na buɗe sabuwar rayuwa, duk da ban rasa komai ba, kuma ban samu ƙalubale irin wanda yawanci 'ya'ya suke fuskanta daga wajen iyayensu idan an sake su ba, ina samun komai, ƙalubale ɗaya na fuskanta shi ne sauyin fuska da mu'amala daga wurin iyayena, Mama ta sauya mini kwata-kwata, tana jin haushina, gani take yi laifina ne kawai, ta ja baya da ni sosai, duk wani abu da zai je ya zo sai take nuna kamar ni naƙi zaman auren, haka mutane ma wasu suke zargina, musamman da suka ga babu wata damuwa a tare da ni, kowa ya juya mini baya, babu wanda yake ta tawa, na fawwala wa ALLAH lamarina, ba na zama na yi kuka a gaban kowa, ba na kaiwa kowa damuwata, idan ma na ji damuwar nakan ɗaura alwala na gurfana gaban Ubangijina na faɗa masa, na san shi ne ma fi sani a kan komai,  haka ban fasa zuwa makaranta ba saboda in ɗaukewa kaina damuwa, Muhibba kaɗai nake kallo na zubar da hawaye, musamman da lokaci yake ta ja amma mahaifinta bai taɓa nemanta ba.
Tafiya tai tafiya, wata ɗaya, wata biyu, wata uku, har an shekara cif da faruwar lamarin, babu Ahmad ba dalilinsa, bai zo ya nemi 'yarsa ba, bai taɓa turo wani ba, a lokacin ne iyayena suka fara fahimtar lallai ba haka aka bar shi ba, hankalinsu ya fara dawowa kaina da tunanin akwai wata a ƙasa.
Wanda mu bamu sani ba, ashe tun ranar da ya zo ya sake furta cewar ya sake ni a gaban kawuna, tunda suka tafi sai ya ɓacewa kowa, aka neme shi aka rasa, ya ɓace ɓat babu wanda ya san inda yake, mahaifinsa ma neman shi yake yi, shiru babu ɗuriyar shi tsawon shekara ɗaya da rabi wanda Muhibba har ta fara girma, amma bata san ubanta ba, wannan abu yana masifar tayar mini da hankali.
Watarana...



#Share
#Comments
#Vote



BY HASSANA ƊANLARABAWA ✍️

HAYATUL ƘADRI!Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon