HAYATUL ƘADRI! page 83-84

156 18 1
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 83-84

Riƙe ni gam Mustafa ya yi cike da matsanancin tsoro yana sakin numfashi, na murtsike idanuwana na janyo wayata na kunna fitilar, har lokacin ana buga ƙofar ɗakina da ƙarfi, sautin ƙarar ya karaɗe ilahirin gidan ko ina yana amsa kuwwa saboda dare ne sosai.

Ina ƙoƙarin zame jikina yana daɗa riƙe ni yana tofa mini addu'a, da ƙyar na samu na zame jikina na sauka daga gadon, na riƙo hannunsa shi ma ya sauko, da fitilar wayata na haska mana muka nufi bakin ƙofar.

Sai da na karanta addu'o'i sannan na buɗe ƙofar cikin rashin tsoro, Shamsiyya ce a tsaye riƙe da ƙugu sai jijjiga jiki take yi, idanuwanta a kaina ta fara magana cikin zazzare idanuwa a zuwan aljanunta sun motsa.

"Au bacci ma kike yi don iya shege? Wato ke ga fitsararriya kin mari Yariman aljanu kina tunanin za ki zauna lafiya ne?"

Muka haɗa idanu ni da Mustafa, ban san lokacin da na kwashe da wata dariya ba, don na kasa riƙe dariyar, wai na mari yariman aljanu, ina dariyar ban fasa ba na dube ta na ce,

"Au Yarima na mara? Ashe ma ƙasƙantacce na mara kenan, ai na so uban Yariman na zabgawa mari ba Yariman ba."

Ta ci gaba da jijjiga jiki tana faɗin.

"Au haka kika ce? To kuwa ki durƙusa ki bamu haƙuri idan ba haka ba sai mun sabauta rayuwarki."

Na nuna ta da yatsa na ce,

"Billahillazi baku isa na baku haƙuri ba, kun yi kaɗan, kuma baku isa kuyi mini komai ba, ni fa kuna ba ni mamaki, shin in tambayeku mana? Me Shamsiyya ta tsare muku ne da za ku addabawa rayuwarta, mace nagartacciya mai haƙuri da sanin ya kamata, mai kirki da addini, mijinta ma yabonta yake yi, amma haka kurum kuna so ku ɓata mata mu'amalarta da zaman aurenta, to wallahi ba zai yiwu ba mu zuba ni da ku sai inda ƙarfina ya ƙare a kan 'yar'uwata Shamsiyya, ba zan bari ku cigaba da cutar da ita ba, annamimai maƙiya Allah, duk tuggunku a kanku zai ƙare wallahil azeem...

Kawai sai Shamsiyya tayi kasaƙe tana dubana jin kalamaina, kuma daman ina sane na ambaci hakan, a fakaice na nuna mata nawa makircin ya shallake nata, Mustafa yana ta riƙo ni ganin na rufe idanu sai masifa nake, amma na ture shi na ci gaba da bambamin faɗa.

"Na faɗa na sake faɗa wallahi baku isa ba, ba zai yiwu haka kawai ku zo ku ɓata mana zamanmu mai daɗi ba, ba za ku ɓata mata rayuwa ba, idan ni da ita tayi mini wani abu zan iya haƙuri na shanye, balle ma babu abin da za ta yi mini, babu wani makirci da za ta haɗa mini, domin na sani kuma na yarda ita ɗin mace ce mai mutunci da karamci, wadda duniya ta shaideta mai haƙuri ce, amma haka kawai ku zo ku ɓata mana zama ba zai yiwu ba."

Tuni na ƙaƙalo kuka na fara hawaye a zuwan tausayinta ya cika raina, na cigaba da magana ina faman share idanu.

"Ni dai yanzu burina ku fita daga jikinta ku barta ta sakata ta wala, ko ta samu salama cikin rayuwarta ta ci gaba da rayuwa mai inganci kamar kowa."

Sai lokacin Mustafa ya sanya baki a maganar cikin rawar murya ya ce.

"Eh wallahi, don Allah ku taimaka ku fita, kun ga dai ko me kuke so ina yi muku, duk abin da kuka buƙata ina kawo muku, don Allah don Annabi ku fita ku taimaka ku barta haka."

Uffan Shamsiyya bata ce ba sai girgiza jiki take yi, ganin taƙi yin magana sai na shigo da wata maganar da na san tilas ta tofa tata.

"Kuma sannan ina gargaɗinku da ku daina yiwa mijinta sata, ba damar ya ajiye kuɗi ko wayoyi a ɗakinta sai ku bi dare ku sace, ku ringa saka bayin Allah a damuwa, banda cutarwa abin naku kuma har da sata, kuna son ku ɓata mata rayuwa ku ɓata wa yaranta rayuwa saboda zalunci.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now