HAYATUL ƘADRI! page 35-36

108 13 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 35-36

*BA ZAN IYA KWATANTA FARINCIKIN DA NAKE SAMUN KAINA BA IDAN NA CI KARO DA SAƘONNINKU NA FATAN ALHERI ZUWA GARE NI, HAƘIƘA RUBUTU BAIWA NE, KUMA INA GODIYA GA RABBIL IZZATI DA YA BA NI KYAUTAR BAIWAR, NA GODE MASOYANA DA KUKE ƘARFAFA MINI GUIWA DA BA NI LAMBAR YABO, NA GODEWA ALLAH DA YADDA KUKE ƘARUWA DA RUBUTUNA, HAKAN BABBAR NASARA CE.*

*GA MASU SON SANIN ADADIN LITATTAFAN DA NA RUBUTA DOMIN SU NEMA SU KARANTA, TO GA SU:*

1- SANADIN HOTO!
2- HASSANA DA HUSSAINA
3- CIN AMANAR RUHI!
4- BAHAGON LAYI
5- GARKUWA BIYU!
6- BAHAGON LAYI(SABON SALO)
7- HAYATUL ƘADRI!

*WAƊANNAN SUNE ADADIN LITATTAFAN MARUBUCIYA HASSANA ƊANLARABAWA*

Duk wasu abubuwa na buƙata sai da Ahmad ya yi mini guzurinsu, tare da tsabar sassanyar soyayyarsa mai mantar da ni komai, muka ƙule a ɗaki babu wanda ya sake jin ɗuriya ta tunda ya dawo. Sai daf da magariba sannan muka silla wanka a tare ya yi shirin fita masallaci fuskarsa sai annuri take yi.
Yana dawowa daga Sallar isha'i ya same ni na kuma cancaɗa kwalliya ina jiran dawowarsa, don zaune nake ina duba kayayyakin da ya tawo mini da su tun daga kan sitturu da takalma da kayayyaki na gayu, a gefe guda ga kayan ciye-ciye nan masu yawa kuma kala-kala. Na samu kaina cikin tsananin mamakin yadda abubuwa suka sauya, duk da na san addu'a ba ta faɗuwa ƙasa banza, a raina na riƙa rayawa to ko dai ɓoye wasu kuɗin ya fi har ya samu yi mini hidima haka, tunda dai Hajiya ba za ta taɓa barin shi ya yi mini wannan hidimar ba, ko aike zai yo mini daga Abuja tilas ta hannunta yake biyo wa, kuma ba a kawo mini komai, don ya sha tambayata shin saƙo ya iso gare ni? Nakan ce masa a'a, yakan kasance cikin damuwa ya yi ta ba ni haƙuri da faɗin komai lokaci ne, watarana sai labari.
Ya shigo ya tarar da ni zaune, ya zauna kusa da ni kafaɗarmu na gogar juna, cikin murna na kwantar da kaina jikinsa ina murmushi na ce.
"Yanzu duk waɗannan kayan nawa ne?"
Ya shafa fuskata ya ɗago ni yana sakar mini kyakkyawan murmushinsa ya ce.
"Duk naki ne Mamina! Ni ban ga abin da zan miki na saka miki haƙurin da kike yi da ni ba, na ɗauko ki daga cikin gatanki cikin ahalinki babu abin da kika rasa, na kawo ki garin da ba ki san kowa ba kuma ina tafiya na bar ki, babu abinci wadatacce kamar na gidanku, babu suttura mai kyau kamar ta gidanku, babu wata kulawa gamsasshiya, duk a hakan kuma so na kike yi tare da nunawa duniya ni ɗin na gaban goshin ki ne, ina alfahari da ke Mami. Allah ya yi miki albarka."
Albarkar da ya saka mini tafi komai yi mini daɗi, na yi murmushi ina wasa da yatsun hannunsa na ce.
"Aure bautar Ubangiji ne, duk abin da kuma aka ambace shi da bauta tilas sai an yi haƙuri, don na tashi cijin gata da rayuwa mai kyau ba shi ke nuna a haka zan dawwama ba, akwai ƙaddara, akwai jarrabawa, kuma ina godiya ga ALLAH da sauyin rayuwa da na samu, a haka ɗin na fi wasu, don haka ka daina damuwa mijina."
Ya rungumeni ƙam yana sumbatar bakina, mun ɓata lokaci mai tsawo muna nunawa juna kulawa kafin ya sake ni ya miƙar da ni tsaye, muka shiga ɗaki ni da shi ya ɗauko mini hijabi ya saka mini, ya kama hannuna muka fita daga kewayen namu ya kulle da mukulli, ni dai ina ta kallonsa tare da mamakin inda za mu je.
Wani babban shago da babu kamarsa a garin ya kaini, ya ce na zaɓi duk abin da nake so a ciki, na riƙa mamaki, bayan uwar sayayyar da ya jibgo mini sannan yanzu yana so ya ƙara wata, da ya ga na kasa zaɓar komai da kansa ya fara jidar mini kaya yana ta tsokanata yana dariya.
Ya kashe kuɗi sosai babu ƙarya, muka dawo gida cikin farinciki da ƙaunar juna, ina ta murna, son mijina na ƙara tsumani, muka ci abinci cikin farinciki muna ta 'yan wasanninmu na ma'aurata. Daren ranar baccinmu ragagge ne saboda zallar soyayya da ƙauna da muka shayar da junanmu.

*******

Rayuwa ta cigaba da yi mana daɗi, a wannan zuwan tabbas Ahmad ya mayar da ni sarauniyar mata, babu abin da na nema na rasa, soyayya da kulawa kuwa kamar zai mayar da ni cikin shi, kullum muna nanuƙe da juna babu rabuwa, muka ƙara shaƙuwa sosai, ta ɓangarena ina ji a zuciyata babu abin da zai raba ni da shi saboda so da ƙaunar da nake masa sun kai maƙura. Musamman da muka samu yadda muke so sai nake ganin matsalarmu tana gab da yayewa ko ma nace ta yaye.
Kwanansa goma sha shida da dawowa a lokacin, amma yanayin rayuwarmu tamkar waɗanda suka shekara goma sha shida da aure, Ahmad ƙarshe ne wajen ba wa mace kulawa idan har yana tare da ita.
A ranar ne da rana tsaka muna cikin cin abincin rana ni da shi, wayarsa tayi ƙara, kamar ma ba zai ɗaga ba sai da na ankarar da shi sannan ya duba wayar, na ɗan kula kamar fuskarsa ta sauya, amma da ya ga ina kallonsa sai ya yi murmushi ya ce miƙe tsaye ya fita tsakargidan kewayenmu ya amsa wayar, har ya kammala wayar ban fuskanci da wa ya yi wayar ba, ya dawo falon yana ba ni haƙurin zaman jiransa da na yi, na yi murmushi na ce babu komai. Muka ci gaba da cin abincinmu muna ta wasanninmu.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now