HAYATUL ƘADRI! page 29-30

123 15 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 29-30

*Muna sayar da MTN data akan price Mai sauki 1gb 300 2gb 600 expire 30 days ga masu bukata suna iya tuntubata akan  WhatsApp number dina ko a kirani 08066268951*

Muna nan tsaye k'arar da muke jiyo wa tana ci gaba da k'arfi, har kamar da doke-doke, muka kalli juna ni da Umman fati ina dafe da k'irjina saboda na tsorata sosai, a hankali ta girgiza kai na ga ta juya ta nufi k'ofar fita, haka ni ma na ja k'afafuwa na bita domin ganewa idanuwana abin da yake faruwa.
Gabad'aya matan gidan muka tarar a babban tsakargidan da y'ay'ansu a na casun dambe, da facalata matar yayan Ahmad da suke uba d'aya, tare da matar babansu Ahmad d'in, jikina babu inda ba ya rawa da idanuwana suka gane mini yadda ake ba wa hammata iska ana kai naushi, zage-zage kuwa na rashin mutunci kamar kunnuwana za su toshe, suna tona wa junansu asiri, gidan ya cika da hayaniya har mak'ota suka fara shigowa rabon fad'a, wani irin fad'a na jahilci domin babu abin da yake fita a bakinsu sai manyan zagi da bankad'e asiran juna, da na ga abin ya zurfafa da sauri na juya na shige kewayena jikina na tsuma, ban tab'a ganin hakan a rayuwata ba, shi yasa da na gani ya zame mini bak'on lamari.
Kan kujerata na zube ina hawaye, sai ga Umman Fati ta shigo jikinta a sanyaye ta k'ara zama gefen da nake, ta dube ni ta ce.
"Rahama saurin kuka ba naki ba ne, kin shigo cikin wata irin rayuwa ne da ba ki saba da ita ba, wadda za ki koyi darasin zaman rayuwa da yawa, don haka sai kin zama jaruma, kin mayar da zuciyarki jajirtacciya kuma dakakkiya, wannan kad'an kenan da ki ka gani daga cikin halayen matan gidan nan da Allah ya had'a ki zama da su, babu ilimin addini da na zamantakewa a gare su sai tsantsar jahilci da gulmar juna da munafurci, kinga waccan bishiyar da ke babban tsakar gida, to a nan ake shimfid'a tabarma a na baje hajar munafurci da gulma, duk wadda ba ta wurin to babinta za a bud'e a yi munafurcinta, haka d'abi'arsu take, ga shi ba sa iya rik'e sirrin mazajensu, komai fallasawa junansu suke yi, don haka idan fad'a ya tashi a tsakaninsu za ki ji suna tonawa junansu asiri suna gore-gore. Na san za ki yi tunanin to ina mahaifinsu Ahmad yake har ake wannan bidirin a gidan nan, to daman na gaya miki a baya shi mutum ne mai tsananin sanyi, ba shi da wani k'arfi a gidan nan duk sun raina shi, bai isa ya yi magana ba rigimar ma tana iya dawo wa kansa. Don haka ina mai ba ki shawara da ki san irin zaman da za ki yi da kowaccensu, kar ki sakar musu fuskar da za su rik'a saka ki cikin gulmammakinsu, duk da na san cewa kina da ilimi kuma kina da hankali."

Tashin hankali! Tabbas na sake shiga rud'u da wannan bayanin, ko ta ina ba dad'i kenan, zama da jahilan mutane irin wad'annan akwai k'alubale, sai dai zan yi duk mai yiwuwa wurin ganin na k'ok'arta na sai ta su a hanya, domin tabbas daga ganin rayuwarsu ba su gama sanin Allah ba.
Na share hawaye na yi wa Ummaf Fati godiya da taimakon da tayi mini ta share min hanya d'od'ar wurin fuskantar abin da ke gabana, sannan kuma da fito da ni daga duhun da tayi zuwa cikin haske, mun jima muna tattauna lamuran rayuwa kafin ta yi mini sallama ta koma kewayen ta, har lokacin kuma hayaniyar fad'an na tashi da k'yar ta lafa.

*********

An shiga wata na uku da tafiyar Ahmad, amma har lokacin bai waiwayoni ba saboda Hajiya bata ba shi dama ba, duk da ban rasa abinci ba amma kud'i ya fara yanke mini, sai na tashi ba ni da ko k'wandalar da zan yi cefane, na rame sosai kullum ba na iya bacci sai sallolin dare da karatun Al'Qu'ani, sai kuma kuka da ya zame mini tamkar fitar numfashina, musamman idan muka yi waya ya karanta mini kalaman nan nasa masu tsumani, to ba na iya bacci sai tunaninsa da son kasancewa da shi.

Saura kwana biyu ya cika wata uku cif ya kira ni a waya yake shaida mini nan da kwana biyu zai dawo, wallahi sai na rasa inda zan saka kaina saboda farinciki, amma duk zumud'ina sai na lura nasa zumud'in ya ninka nawa sau ba adadi, sai dai ya ce mini zai fara biya wa ta Kano wurin Hajiya, daga nan sai ya wuto garin. Tunda na ji hakan sai hankalina ya so tashi, saboda na san babu alheri a tare da matar nan, amma ni ban isa na raba su ba tunda kamar uwa take a wurinsa, ni alk'awarin da na d'auka ma ba zan nuna masa na san komai ba, tunda shi bai gaya mini ba, duk da na san rufe masa baki aka yi.
Ina so na yi kitso da k'unshi, da kuma gyaran jikina domin tarbar mijina, sai dai babu halin hakan saboda ba ni da kud'i, ga shi ina son na yi masa girki mai k'ayatarwa saboda ya jima bai ci abincina ba, ba zan iya kiran waya gida na ce a aiko mini da kud'i ba, saboda basu san baya nan ba ma, kuma sun san na tawo da kud'i garin, za su yi mamakin ina na kai kud'in tunda ina tare da mijina kuma komai shi ne mai yi mini. Haka ranar na wuni cikin tunane-tunanen yadda zan samu kud'in da zan kawar da matsalar gabana.
Zuciyata ta ba ni shawara kan na ranci kud'i wurin Umman Fati, bayan Ahmad ya dawo sai na bata, ko a rayuwar k'uruciyata ban tab'a cin bashin wani ba, hasalima na tashi da tsoron cin bashi ne saboda yadda na ji ana wa masu cin bashi azaba idan suka mutu da hakkin wasu, amma tilas haka na yi shahadar k'uda saboda ba ni da yadda zan yi, na samu Umman Fati da zancen, take kuwa ta d'auko kud'i ta ba ni, saboda daman tana da sana'ar yi, tana da baro baro da take bayar da hayarsu ana d'iban kaya tana tara kud'i.
Washegari na yi kitso da lalle, har ma da gyaran jiki, sai ga ni na fito ras na yi kyawu na ban mamaki, sai dai ramar da na yi wadda ta fito a zahiri.
Ranar da zai dawo kuwa haka na tashi na gyare kewayena tas, na yi turaren wuta ko'ina ya d'auki k'amshi, na yi girkuna kala-kala masu matuk'ar dad'i na adana, sannan na fesa wanka da kwalliya wadda na jima ban yi irinta ba, na k'ame zaman jiransa.

HAYATUL ƘADRI!Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin