Page 1

849 43 4
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 1*

*FREE BOOK*

Duƙe take a gaban murhun tana hura shi da iskar bakinta, daga idanunta har zuwa hancin ta da suka yi jajazir kasancewar ta fara tas zubar ruwa suke na hayaƙin da ya turnuke sararin wurin sbd kasancewar iccen ɗanya, hannunta da yayi baƙi sandiyar hura wutan ta sanya ta kamo ɗan kwalin kanta irin me yauki na da ɗin nan ta sa ta share hawayen idanunta kan ta mike a hankali tana gyara zanin da yake tsab tsab saboda tsananin tsabtarta sede a koɗe yake yayi fari fat..

Katon cikin dake jikinta na fallasa kanshi, a hankali take tafiya zuwa bakin rariyar su ta duka ta ɗauki buta tare da fyace hancin ta sossai, Seda ta wanke hannunta dake baƙi sbd hura itace kan ta wanke hancinta zuwa fuskanta ta sa sabulu guntu da ta tsinta wurin wanke wanken ta wanke hannayenta da kyau kan ta sake wanke fuskanta..

Wata yarinya dake gefen ta da suke matukar kama da bata wuce shekara 6 bane ta ce
"Mama wutan ya ki kamawa ne?"
Ajiyar zuciya ta sauke tana kara kikkimta mawankin tace
"Aisha ya zan yi, ya ki kamawa tsabar fifita kin ga yadda hannuna ya zama"
Yarinyar ta matso tana ɗaukan maficin ta cigaba da fifitawa tace
"mama ko in koma in sami baba me faskare ya tsanmmana rairayi da sauran faskare mu zo mu sa, yunwa nake ji kinga yaya manu ma dake rashin lafiya tun safe be ci komai ba"

Lumshe idanunta tayi da suke kyawawa har mamakin ganinta a irin wannan yanayi na rayuwa Ya rufe ni,(sede ba'a mamaki da ikon me duka) a hankali cikin muryarta dake fallasa rashin son Magana da hayaniyar ta ta ce
"Aisha baze gaji damu bane? Kullum muna kan yawo wurin shi neman faskare bayan ba saya muke ba?"
Dakuna fuska yarinyar tayi hawaye na zubo mata.

Matsowa matar tayi ta zauna a kujeran tsuguno dake wurin tare da karɓan maficin ta ce
"kar kiyi kuka bari na cigaba da fifitawa samu ruwan ya tafasa in dama kunun ki sha, kiyi hakuri"

Dukda ita karan kanta ba wani karfi ne da ita ba tsabar yunwa tun jiya da rana da ta sha kunun da ya zame musu jiki na garin masara da tsamiya bata kara saka wani abun a bakinta ba bayan ruwa har yanzu da ake neman karfe sha ɗaya na rana ban da Juyawa babu abinda yaron cikinta ke yi cigaba da fifita wutan tayi da kyar ta samu ruwan ya tafasa dama tun tuni Aishan ta dama musu garin masaran da ruwan tsamiya sbd rashin abun sarrafa shi kawai ta juye a ciki tana Juyawa har ya nuna.

Saukewa tayi Aisha ta je ɗan karamin kitchen ɗinsu dake zagaye da zink da yayi baƙi kirin ta ɗauko wasu kofuna marasa hannun arziki ta kawo guda uku, ba tare da sugar ba sbd basu dashi basu da dalili ta zuzzuba, ta Mikawa Aisha nata ta rufe nata a gefe tare da ɗaukan Ɗayan ta karasa kan yaloluwar taburma dake shimfiɗe cikin varender ɗin sun da rabi a fashe rabi da siminti, farin yaron da kammaninsu yake sak kaman Aisha da shima ba ze wuce 10yrs ba ta ɗago ta taimaka mishi ya zauna, jikinshi banda tururin zafi babu abinda yake fitarwa.

Cikin yanayin muryanta ta ce
"Usmanu tashi ka sa wani abu a cikinka ka ji? Sannu.. Daure babana"
Da kyar ya iya yin kurɓi biyu se amai, ya fara kelawa ruwa banza sanadiyar rashin komai a cikin nashi daga karshe ma banda kakari babu abunda yake yi, hawaye masu zafi ne suka kwararo mata, banda fatan Allah ya jefo mata Yusuf babu abunda take yi a ranta, zata tambaye shi zata roke shi ya taimaka kar yaron su ya rasa ranshi kwance a gida ko da ze zage ta har zagin ya Mannu a jikin ta ne bata damu ba.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now