Page 34

341 20 3
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 34*

*FREE BOOK*

*My Meerah😍❤️ wannan page ɗin naki ne se yadda kike so za'a yi😘*

Wannan tafiya shi ya zama silar chanzawar rayuwarta gabaɗaya, tafiyar da ya zama silar farin cikinta da samun dawamammiyar kwanciyar hankali, ingantacciya kuma nagartacciya, kwarai Allah ya riga ya mata zaɓi..

Jirgin su be sauƙa a ko ina ba se King Abdulaziz international Airport jeddah, ko a mafarki bata taɓa mafarkin zata ziyarci ɗakin Allah ba, se gata nan a ciki tsamo tsamo kusa da manzon Allah, hawaye ne ya zubo mata daidai sadda suka Haɗa idanu bayan ya gama sauka, da idanu yayi mata alamar hawayen na me? Girgiza kai kawai tayi, tare da kankame hannun Rashida.

Motoci na musamman ne suka zo suka dibe su zuwa masaukinsu, hotel ne me zaman kanshi wadda daga tsaruwarshi da securities ɗinshi kama daga mutane da na'urori zaka san ya wuce na ya ku bayi, flat ne na musamman a inda suke ɗin parlor da ɗakuna huɗu, kuma kowanne self content komai da komai akwai a gyare yake tsab.

Baccin gajiya duk suka yi kan su tashi ya musu order na abinci kala kala, nan suka baje a parlor suka ci daga nan suka fita don kallon garin jeddah kan su wuce, dayake Rashida ta san Saudia sossai hakan yasa ya kyale su ya tafi harkokinshi daga karshe seda ya dangana da Riyadh sbd wasu meetings don Saudia suna so su saye shi...

Be dawo ba se washegari amma ko wani lokacin cin abinci za'a shigo musu dasu gasu nan se wadda kowa yayi ra'ayin ci, washegari da yamma ya dawo a daren ya kira wayanta yace mata yana so su ɗan fita amma su biyu kawai..

Shiryawa tayi cikin jallabiya peach and red kirar Kasar Oman ya ji ado kam, se bata yafa gyalen ba ta ɗauki Red gyale tayi wrapping ta sa red flat shoe, da Rashida suka bar yaran suka fito yana sanye da kananun kaya as usual riga da wando, da kanshi ya buɗe mata bayan motar ta shiga, shima ya zagaye ya shiga bayan kusa da ita motar ta bar harabar hotel ɗin.

"Hidayah!"
Ya kira sunan cikin husky masculine voice ɗin nan nashi wadda seda taji a jikinta rabon da ya kirata da Hidayat ya jima.

"Na'am paapi!"

Ya waiwayo gabadayanshi gareta yana kallonta yace
"alfarma nake roko na san kaman nayi sauri sede ina ganin menene anfanin soyayya idan ba hakan ba, ina son ki kina so na mun fahimci juna bamu da kowa se kawunanmu da yaranmu, don Allah ki bani dama in sake shiga rayuwarki na dindindin"

"paapi ka wuce duk wata alfarma ko roko a gareni, duk abunda ka yanke mana ko zaka yanke mana na tabbatar me kyau ne kuma baze cutar damu ba so na baka dama.."
Ta faɗi itama tana kallon shi.

Lumshe idanu yayi ya buɗe yana sakin murmushi yace
"Gobe zamu wuce madina, kaman yadda kika sani a aikin Umura zuwa madina is optional duk wani aiki na Umura a Makkah ne kuma a Makkah ya kare, gobe in Allah ya kaimu idan mun isa masallacin manzon Allah za'a ɗaura mana aure don ina so ki isa ga ɗakin Allah da martabar Aure bisa kanki..!"

Kallonshi kawai take se hawaye ya fara zubo mata, me yafi wannan? Anya akwai wadda ze sakata farin ciki a duniyan nan bayan Raed, ita hidayat ce za'a ɗaurawa aure a madina! Ya Allah ina Yusuf, ina umma da su Surayya su zo su ga yadda rayuwarta ya inganta, ta nagartu da samun cikakken masoyi wadda yafi maza dubu a gareta, ita kam me zata mishi ta saka mishi bayan tsabtatacciyar soyayya da kauna marar algus?

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now