Part 23

270 19 1
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 23*

*FREE BOOK*

"Na tabbatar ba se na nemi sani ba ina magana ne da Hidayat daga Paris kike ko ma ina ne... Ba na kira bane in ji muryanki ko maganan ki ba na kira ne in buga miki gargadi me karfi akan mijina... Wallahi wallahi in baki fita hanyar mijina ba se na zama ajalinki! In baki ji tausayina ba nima ba zan ji naki ba.. Kaman yadda ya tsallake ya bi ƙasa ƙasa ya tafi wurinki har wata uwa duniya be damu da ya barni da tsohon ciki ba haka nima zan tsallako in zo har inda kike in halakaki in baki kyalemin miji ba.. Daaɗin abun Kuma kema macece kaman yadda kika min Allah yasa a miki ninkin ba ninkin, bazawarar banza..!"

Tsit aka kashe wayan, tsamm hidayat ta tsaya a tsaye kaman an dasa ta tana kallon fuskan wayan da dama a hansfree ta saka, daga bayanta ya ɗan leko fuskanta don ya saka hannu kenan a kofan ya fara jin muryar yayi niyyar shigewa sede jin yadda ko ma waye magana take a harzuke da bala'i yasa ya dawo da baya.

Hannunshi ya saka yayi waving fuskanta se tayi firgigit ta dawo da sauri ta kalleshi tana fiki fiki da ido wadda ta saka shi dariya, duk yadda ya so ya danne seda sautin dariyar ya fito.

Yace
"Au wai dama bazawarin naki ma me mata ne?"

Raurau tayi da idanu ya sake sakin yalwataccen murmushi tare da ɗaga duka hannunshi yana shrugging kafaɗa yace
"I surrender! Ni ba ni na kar zomon ba"

Bata san ta Harare shi ba seda ya zaro Idanu duka waje yana kallonta da sauri ta shige zuwa room ɗinta tana ɗan murmushi, bayan ta shiga a fili ta furta
"nima na rama.."

Ajiyar zuciya ta sauke ta sake kallon fuskan wayanta, layin Nigeria ne kwarai kenan matar Hamza ce, baki ta taɓe ita bata san a gaske hakan na faruwa ba seda ya faru a kanta a yanzu, abunda ya daure mata kai shine yadda mata suke iya furta yin ajalin mace akan ɗa namiji, Hausawa suka ce maza ƴaƴan mamansu.. Lallai kam.

Aisha da su Noor da suka shigo ne yasa ta mance Tunanin wata matar Hamza da ta kirata, da shirin kwanciyar su suka ce yau a ɗakinta zasu kwana.

Gadon ta bar musu ta sauka kasa da blankets masu taushi, Seda ta tabbatar sun yi Adu'a kan suka kwanta.

Wayanta ne yayi ringing ta duba taga hamza se matarshi ta faɗo mata, baki ta ɗan taɓe kan ta ɗauka suka gaisa yace
"gobe kam in Allah ya kaimu zan ga hasken raina"

Tace
"uhmm hasken ranka kam na chan ka barota Nigeria.."

Yace
"ban gane ba!"

Tace
"manta kawai, ya Paris to?"

"Babu daaɗi tunda baki a kusa dani"

Tace
"hope kana ji daga wurin Aunty na?"

Dariya yayi sossai yace
"Zainab ɗin ce Auntynki?"

Tace
"eh mana, itace first wife ai Allah ya riga ya bata girman"
A ranta kuwa tace Ashe sunanta zainab!

Sama sama suka ɗan ƙara hiran kan suka yi sallama ta kwanta itama.

Washegari kaman yadda ta saba da wuri ta gama musu komai suka fice a tare shi kam har lokacin be baro ɗakin gym ɗinshi ba ma.

Bayan sun gama lectures suka haɗu da Rash, hira suka sha seda taga call ɗin hamza kan ta kalleta tace
"kina da wani class ne?"

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now