Page 7

223 21 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 7*

*FREE BOOK*

Abba yayi nadamar hukuncin shi gareta yafi abunda ya fi a kullum se ya zub da hawaye in ya ganta, rashin kula da rashin suturu duk sun haɗu sun maidata tsohuwar da bata kai ba, yayi nadamar rashin sauraren ta kuma a kullum in har zata je gareshi ta kan karanci irin rokon gafararta da yake da idanu, shine kaɗai take kalla tayi farin ciki ta kuma buga kirji tana da wani a duniya shima yanzu ya tafi, bango mafi girma a rayuwarta ya zube tas bata da karfin fara wani tubalin bare ta sake gina makamancinshi a rayuwarta...

DAWOWA LABARI

Cikin wani irin yanayi take kukan, kuka ne wadda duk wadda ze kalleta ze san akwai abu mafi girma da ya sameta na rayuwa ganin yadda ko la'akari da jama'ar dake kai kawo bata yi, wata mata ce ta matso ta tare da dafata tace

"baiwar Allah kiyi hakuri! Duk tsanani yana tare da sauki ki duba condition naki it's not good for you da irin wannan kukan da kike"

Kallon matar take da idanun rayuwa daaɗi yake miki ni tawa rayuwar bata da sauran anfani banda na yarana, ba tare da tacewa matar kala ba ta mike ta nufi gate tana tafiya kaman iska ze ɗauke ta, da Kallo matar ta bita cikin tausayawa duk yadda akayi matarchan tana cikin depression me girma.

Har ta isa gida bata dena zub da hawaye masu zafi ba, a kofar gida ta ga Usman da Aisha zaune da gudu suka zo suka mata oyoyo, tana share hawaye wani na bin wani ta rungumesu itama, cikin sanyin murya tace
"Usman me yasa baku shiga ko wurin Asabe bane kuka zauna a kofar gida tun yamma?"

Aisha tace
"ba mun je ba su Lantana suka koremu wai tunda bamu da gado mu bar musu gida"

Bata sake cewa komai ba, hannunta na rawa ta fiddo key sede ta kasa buɗewa se Usman ne ya karɓa ya buɗe suka shiga, akwai wutar nepa alwala tayo suma duk suka yi cikin karfin hali a zaune haka ta miƙa sallar magrib da isha da ake ta kira.

Bayan sun idar tana jin yaran na azkar sede ita bakinta be iya yayi ba se a zuciya take binsu, bayan sun gama Usman yace
"Mama baki da lafiya ne?"

Aisha ma tace
"Mama kina ta kuka Ko Abba ya biki ya bugeki ne a unguwar da kika je?"

Rungume Aisha tayi ta saki sabon kuka, duk yaran ma se suka soma kuka, da kyar ta dakatar da kanta tace

"Usman, Aisha ina kun san Abbana na gidan umma?"

Aisha tace
"Umman Abbanmu wacce itama take dukanki?"

Lumshe idanu tayi tace
"Aisha ba na hana ki cewa ana dukana ba?"

Shiru yarinyar tayi, se Usman yace
"Abba da be da lafiya mama?"

Kai ta gyaɗa tace
"shine yau ya rasu, ya tafi ya barni ƴaƴana bani da kowa se ku se kuma Allah...."
Ta fashe da wani irin kuka.

Aisha tana shafa bayanta Usman na share mata hawaye, sun jima a haka Kan Aisha tace
"Mama malam yace haramun ne in mutum ya mutu a yi mishi kuka ko Ya Usman?"

Usman yace
"Eh Mama, muma ya ce mana duk hawaye da ze diga daga fuskanka kaman azabar wuta kake karawa wadda ya mutun"

Gyaɗa kai tayi tace
"Na dena! Na dena kunji?"

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now