Page 42

279 24 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 42*

*FREE BOOK*

***Masha Allah🥰 Naga comments Bila adadin and I soo much love ur review about this book, na tabbatar saƙon ciki na isa inda ya kamata...Allah ya raba mu da son zuciya yasa mufi karfin zuƙatanmu ya kuma raba mu da sharrin shaiɗan.... Son so❤️ masoya wannan littafi***

A sadda take bada labarin daki daki tana zub da hawaye masu zafi waenda suke fita daga ƙasan zuciyarta na ciwon irin abubuwan da aka yi mata a rayuwa seda dukkansu parlorn suka zubar mata da hawaye, da ta zo wurin rasuwar Usman da Abba kuwa seda ta so shidewa don kuka, mahaifiyarta ce ta dinga tausarta ba tare da tayi magana ba, lallai Amina bata da mutunci Amina bata san girman darajar da Allah yayiwa ɗan Adam ba...

Duk shiru suka yi suna jinjina irin wannan baƙar zuciya, Alhaji Usman ya share fuskanshi yace

"Duniya ta lalace kwarai da gaske, yanzu kowa nashi da kanshi kawai ya sani taya muke Tunanin samun rabauta bayan Bama anfani da hadisin nan da yace ka sowa ɗan uwanka abunda ka sowa kanka? Amina babu zuciya a kirjinta bata Tunanin makomanta, bata Tunanin Abinda kayi shi za'a maka! Ta mance cewa alkhairi fa Danko ne... Ta wulakanta ku ta tozarta ku daga ita har ɗan ta da be san darajar mace ba bare matar aurenshi, sun ɗauka a cikin masu arziki su sun gama hayewa basu san cewa a sadda 'Suka ga ZABUWA.. Da zanen ta suka ganta ba' Allah ubangiji yaji ƙan Usman ya gafarta mishi, shi kuma Yusuf se ya girbi abunda ya shuka don baze taɓa sha da kisan kai ba, lallai ne wadda ya kashe a kasheshi.. Ita kuma Amina Duniya ce tafi bagaruwa iya jima... Raed Na gode na gode maka kwarai da gaske a sadda ka tallafi rayuwar hidayat ka juya mata shi daga baƙi zuwa fari ba tare da ka san ita er uwarka ba ce kayi hakan da zuciya ɗaya Allah ya baka aljanna sanadiyar hakan bani da abunda zan saka maka dashi"

Shiru yayi yana jin ɗaci a makogoronshi duk sanadiyar balaraba ne ko kallonta baya son yi har gaban Abada, a hankali ya cigaba
"Ku kuma gamji da Laure Allah ya saka muku da alkhairi, na gode kwarai da irin sadaukarwar da kuka yiwa mata ta, halayyar ku da ta Raed ya nuna cewa lallai na Allah basa ƙarewa a duniya ko da an samu mugaye dubu irin Amina da Balaraba, ko duka dukiyan da na tara zan baku bazan saka muku ba sakamakon ku na wurin ubangiji sede bata ɓaci ba, in kun zaɓi zama damu na muku alkawarin farin ciki da wadata har karshen rayuwarku da izinin Allah, in kun zaɓi komawa na muku alkawarin ko wani dabba da kuke kiwo garke biyar biyar, kuna da kujerun Makka! Gida da kuma Motoci ina so a cikin jama'ar Garinku in za'a lissafa masu kuɗi Gamji ka shigo ciki da yardar Allah..... Hamza ka yi haƙuri ka gafarceni, ka sani bawa baya taɓa wuce kaddararsa hakanan abunda Allah ya rubuta wani be isa ya sauya shi ba se ya faru, kwarai Allah me yin yadda ya so ne a sadda ya so, ya fito da kyakkyawa daga cikin mummuna tunda na farfado ake min murnar samun ɗa irin ka me cikakken nagarta da kamala Dukda ga yadda mahaifiyarka take, ka ga kenan Allah babu ruwanshi da wacece mahaifiyarka so bana so ka sanya damuwa a ranka, bana so ka kasance cikin masu aibata ko saɓawa mahaifiyarka karka ce mata komai kuma karka yi fushi da ita ka kula da ita sbd ta kula da kai a sadda baka iya kula da kanka, sede ni ba zan iya cigaba da zama da ita ba na saketa saki biyu.... Zaka iya kaita duk wani wurin magani da kuɗina hakan be dameni ba, Allah ya riga ya nuna mata iyakar ta tunda ya Haɗa ka da wacce bata so gani ba a duniya, ya kuma ɗauke lafiya ta a sadda take farin cikin samuna wa kanta ita kaɗai, daidai lokacin da ya bani lafiyan kuma ya dawo da Aisha rayuwata ita kuma ya fitar da ita cikin hikimarsa da buwayarsa, kaga wannan babban darasi ne Allah ya sa muyi anfani da Ayar dake cikin wannan rayuwa tamu gabaɗaya"

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now