Page 8

234 22 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 8*

*FREE BOOK*

Taku biyu ya qara ya waiwayo ya kalli Farah yace
"baby let's help her she's really in need of that OK?"
Yamutsa fuska tayi kan ta sake mishi hannu ta koma gefe tayi folding hands nata kaman wata babba, girgiza kai yayi ya san fushi tayi sede jininshi ya kasa kyale shi yin biris da wanchan yarinyar, Aisha ya nufa yace

"uhm Gayamin! menene?"
Seda ta kalleshi kaɗan kan tace
"likita yace mamana zata haukace ko ta mutu in aka wuce awa shidda ba'a mata aiki ba gashi yanzu saura awa d'aya.."

Ta karashe da kuka, kallonta yake in disbelief yace
"likita yace haka? Ina babanki?"

"Yayana yaje ya nemo shi kuma na san ko ya same shi baze biya ba sede ya doke shi ya kore shi"

Lumshe kyawawan idanunshi yayi da suka ɗan sauya kaɗan ya mike daga kyakyawar durkuso da yayi a gabanta yace
"muje let's see the doctor"

Hannunta ya kama suka nufi ciki Farah na binsu daga baya baya sbd kyamar Aisha da take, office ɗin likitan ya shiga wadda yayi saurin mikewa daga ganin Moh Raed washe 32 ɗinshi yayi yana Mika mishi hannu sede Raed fuskewa yayi yace
"menene matsalar maman wannan?"

Bayani ya mishi akan an kawo ta an barta da yara gashi tana shirin zauce musu sbd jijjiga da take tayi, yayan yarinyar ma be yi goma ba amma yanzu ya tafi nemo uban su, lumshe idanu yayi da kaman ɗabi'ar shi ce kan ya ware su akan likitan, Seda ya ja iska kan ya tambayi kuɗin aikin.

A lokacin da likitan ya faɗa mishi wani takaici ne ya zo mishi wuya abunda ko dubu ɗari be yi ba, ba tare da ya zauna ba yayi call, se ga ɗaya daga cikin bounchers dake rike da folder ya zo, kudade masu yawa yayi dropping ma likitan yace
"prepare for the operation now!"

Ya juya kenan se kuma ya sake Juyowa, "make sure after the operation you change her to the Amenity ward give her all the care she needs, am very sure this will be morethan enough"
Ya karashe yana nuna kuɗin da yayi dropping ɗin.

Kai likitan yake ta gyaɗawa yana cewa
"in Shaa Allah"

Ficewa yayi yana me kallon agogon Gucci dake daure a hannunshi jirginsu to Paris is in a jiffy gashi he will like to help this little girl more, but he didn't have any other option.

Yana tsaye aka turo Hidayat, Aisha yake ta kokarin consoling sede ganin an fito da mamanta yasa ta sake jakar kayan haihuwar dake hannunta tayi wurin gadon da gudu, kallon Gadon yayi for seconds kan ya ɗauke kai, baze iya cewa ga kamannin maman ba he only saw her coily hair dake zube bisa pillow, her arched eyebrows a slim nose  nd her cherrie lips da suka yi jajazir a bushe alamun yunwa da rashin abinci me kyau

Ba tare da ya sake kallon gadon ba ya Riko Aisha yana rarrashinta, Farah dae bata ce musu komai ba don ba duka abunda suke faɗa take ji ba, hausa na musu wahala sossai gwara ma ita da ƴan uwanta dake chan gida Paris, dayake ita purse na dad ne duk inda zasu tare suke zuwa yasa ko wani shekara take shigowa Nigeria, yau daddyn ta is talking to stranger a gabanta har mantawa ma yayi da ita yau akwai daru, shima da ya san kayanshi in ya kalleta sede ya sakar mata soft smile, a tare ya Riko hannayensu zuwa mota lokacin har mutanen shi sun gama abunda ya shigo dasu asibitin, Manyan snacks ɗin Farah ya ɗiba dayawa ya zuba mata cikin wani fancy Leda ya Mika mata.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now