Page 4

268 18 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 4*

*FREE BOOK*

Cikin rawar murya tace
"A'a umma don Allah kiyi haƙuri wlh Abba ne ya matsa na ɗauki kuɗin machine shine zan zari dubu ɗaya.."

Wasu Zafafan maruka hagu da dama ta ɗauke ta dashi wadda Seda ta saka ta kaiwa kasa tana ji kaman amsa kuwwan maganan umma tana cewa
"Munafuka! Algunguma sharri zaki yiwa Alhajin? Ina ya ga bakin magana da har ze matsa ki ɗauki kuɗi? Idan ba salon sata ba me yasa da kika shigo baki shiga cikin Gida ba kika sulale nan? Eyee wato da mudi me gadi bai ce min kina nan ba sede mu zo mu samu an wawushe Alhaji? No wonder kullum kwanan duniya ake samun kuɗi ya ɓata.."

Hawaye ne masu zafi suka zubo mata, ta sa hannu ta goge har lokacin bata ji daidai sbd umma ba bahaushiya bace irin kabilan kudun nan ce da suka ginu da tuwo da wahala hakan yasa hannunta na daga cikin hannun da in ta sauke maka se ka rasa natsuwa da ji na tsawon lokaci, cikin rawar murya tace
"Wallahi ban taɓa ɗaukan abin wani ba umma kuma ke sheda ce, da ina sata da tun kan nayi aure da kin sani Allah ya gani b..."

Gwaɓe mata baki tayi wadda Seda ya fashe umma tayi.

"Rashin kunya kuma zaki min? Eh lallai dole.. Karki ga kaman kin haihu biyu ko kina da tsohon ciki wlh baki sauya a idanu na ba, be dame ni ba yanzu in lakaɗa miki na jaki in ga uban da ya tsaya miki a garin Kano, banza ƴar Zina...."

Faɗuwar mutum da suka ji yasa duk suka juya, Jijjiga Abba ya fara wadda har yana sulmiyowa daga cikin kujeran ba tare da sun kula ba seda ya faɗi.

Da gudu suka yi kanshi suna kiran sunanshi, umma na shikenan ta kashe min shi ta huta.

Kaman daga sama se ga Yusuf da kaninshi mus'ab da gudu suka ɗauki Abba suka fito zuwa mota.

Hidayat bata tsaya ba ta shiga motan tare da kafe shi da idanu tana zub da kwallar takaici da baƙin ciki, babu wadda ya kula sbd tashin hankali suka ja suka yi asibiti umma ta biyo su da motan ta, suna parking a harabar kumfa ya fara fita daga bakin Abba hankali tashe Hidayat ke share mishi da hijab ɗinta.

Buɗe idanu yayi ya kafe ta da shi, wani natsuwa da karfin gwiwa ta samu a take ta fara karanta Kalmar shahada abu da ikon Allah mutumin da ya shekara ɗai ɗai har shekaru bakwai da watanni a yanayi na jinya da rashin magana da tsananin ciwo ya buɗe baki kalmomin na fita a rarrabe ya fara cewa

"Kiyi haƙuri da rayuwa, ki yafe min hidaya!"
Sune suka fito kaman an fusgo su daga bakinshi, kalaman da suka yi sanadiyar karasa ruɗata tsabar hawayen dake kwaranya har bata iya gani da kyau tana girgiza kai tace
"baka min komai ba Abba..! Baka min komai ba..!!"

Murmushi yayi se ya fara karanta Kalmar shahada daga karshe numfashinshi ya tsaya Chakk.

Daidai lokacin da Yusuf ya fisgota waje ba tare da yayi la'akari da cikin jikinta ba, isowarsu kenan da gadon marasa lafiya don a ɗauki Abba sede likitan na lekawa yace

"Innalillahi wainna ilahi rajiun! Sede haƙuri Allah ya riga ya amshi abun shi"

Ihu umma ta kwala, yayinda hidaya da ta riga da ta san da mutuwar sede bata yardar ma zuciyarta ba seda taji daga bakin likitan, chaak duniyar ta tsaya mata Sam bata san me suke yi ba.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now