Page 20

266 22 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 20*

*FREE BOOK*

Tun daga nesa yake hangar kaman yaron nan da ya taɓa kade mahaifiyarshi har ta mutu, suna matsowa kusa kuwa ya taɓa shi wadda ya saka Raed firgita ya tashi kaman ze gudu, pastor Philip yayi saurin rikeshi yana cewa

"hey calm down we r not gonna harm u"

Pastor David yace
"Muhammad ya kake?"

Kallonsu Kawai Raed yake ya kasa magana don shi be sheda su ba, ganin da gaske be gane shi bane yasa yace
"Me kake yi anan haka Raed? Ji jikinka duk kashin shanu da ruwa? Me ya sameka a fuska haka?"

Se yaron ya sa kuka, duk wani tausayinshi ne ya kama su, lallashinshi suka yi tayi har yayi shiru yayi musu bayanin abunda ke faruwa Seda Philip yayi kuka da David ke faɗa mishi abunda yace don shi ba ɗan Nigeria bane ya je Mambila yawon buɗe idanu da yada addininsu ne shine ya sauka wurin Pastor David.

David ya ce cikin harshen turanci
"Tun daga sadda na kade mahaifiyarshi yaron ya kasa fita a raina, na sha zuwa don son ganinshi baban yake ce min baya nan ko yana makaranta in bashi kuɗi akan a mishi sayayya amma dubi yaron nan, kaman a bola yake rayuwa ko almajiri ya fishi kyaun gani.."

Yayi maganan yana share hawaye, Philip yace
"matsalanku kenan a Nijeria had it been a ƙasar mu ne taya hukuma zata bari a yi ma yaron nan Haka"

Bayan gama jimaminsu suka ce ya zo su je su yiwa baban nashi nasiha Sam ya ƙi ya san karshen shine a ciki, kyautar kuɗi suka bashi shima ya ƙi karɓa, A mota suka dauke shi zuwa gidan David suka bashi abinci ya hau ci hannu baka hannu ƙwarya, se kallon shi suke har ya gama suka saka shi yayi wanka Philip ya sa kayanshi a washing mashing bayan ya fita tas suka yi drying suka goge suka bashi ya maida jikinshi take yayi kyau.

A parlor suka zauna ya zauna a ƙasa ya kurawa TV da ake buga kwallo idanu, tsabar kallon da yake yiwa ball ɗin ko idanunshi baya son kaudawa be san time ya tafi ba seda ya ji kiran sallah a masallacin dake kusa da gidan David ɗin, da sauri ya miƙe yace ze tafi.

Seda suka bashi abinci ya sake ci kan suka maida shi inda suka ɗauko shi, a raɓe ya shiga gidan Badi'ah tace
"ka ci gaba da raɓe raɓe duk aikin da ka tara zan ga uban da ze maka ai, kuma babanka ya ce baka da abinci a gidan nan har nan da kwana biyu sbd kashe mishi sa da kayi kuma ka kiyayi sake haɗuwarku Duna kawai"

Kanshi kasa ya wuce ya ɗauko roban da yake diban ruwa ya fita ya fara jidowa Seda ya gama ya je ya kwanta a cikin dabobbin gwanin tausayi.

Daga haka David ya gane taimaka mishi, Philip ya koma amma da Tunanin Raed makale a cikin ranshi, rayuwar gidansu kuwa banda tsanani babu abunda ya ragu a gareshi, kasancewar shi yaro kuma abun ya mishi yawa yasa yayi developing Panic Attack..

Wani irin tsoron mutane yake, baya yadda ya kalli idanun kowa kullum a raɓe yake a wuri, idan kuwa ya tsorata numfashin shi se yayi ta seizing kaman ze mutu da kyar yake samu ya samu sauki se ya Haɗa kai da gwiwa yayi ta kuka.

A haka ya sake shekara biyu a gidan ya cika shekara bakwai, a lokacin ya san yana da wani abu guda ɗaya dake debe mishi kewa yake hana shi shiga damuwa wato ball, ze Haɗa ledojinshi ya sami wuri yayi ta bugawa to fa shine kaɗai zaka ga haƙorin shi yana murmushi se kuma in ya je wurin Daadida da ya kan Saci hanya yaje sama sama da kyar ze tsaya ta kulla mishi abinci a Leda ya tafi saboda kar a gane Babanshi ya kusa kashe shi.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now