Page 18

249 18 2
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 18*

*FREE BOOK*

**Assalamu Alaikum warahmatullah gaisuwa irin ta addinin musulunci, fatan duk kuna cikin koshin lafiya? Kuyi haƙurin jina shiru jiyan kaman yadda Zaku sake jina shiru daga wannan se ranar Friday in Allah ya kai rai.... Bautar ƙasa nake gamawa jibi Thursday kenan, tunda Monday ya shigo bamu da zama yini muke wurin abubuwan gamawan da ciwon kai, bacci da gajiya nake dawowa bani da natsuwar typing Sam, fatan Zaku min uzurin hakan. Na gode***

Da sallama ta tura kofan ta shiga, yana lulluɓe cikin bargo daga kafafunshi har kanshi a natse ta karasa gefen bed side ɗin ta ajiye tray ɗin, bata bi bugun zuciyarta ba ta gyara murya kaɗan tace

"Sir ur tea is ready"

Be motsa ba seda ta sake maimaitawa ya kai zara zaran yatsunshi ya janye bargon fuskanshi ya bayyana, gajiyayyun idanunshi ya buɗe a kanta hakan ya sakata saurin rausayar da nata don bazata iya jurar kallon cikin idanunshin ba..

Mikewa yayi ya zauna tare da jingina bayanshi da jikin gadon yana sake kallon fuskanta dake nuna taradaddin rashin lafiyan nashi.

Ganin ya zauna yasa ta ɗauko ta mika mishi karamin tumbler ɗin ya sa hannu garin karɓa hannunsa ya ɗan gogi nata kaman wacce ta sa hannu a cikin wuta ta wani zare da hanzari tare da saurin zaro idanunta kuma tana kallon tea ɗin da ya kusa barewa jikinshi.

Da sauri ya riƙe da kyau yana kallonta itama idanun nata ta ɗago ta kalli fuskanshi se ta duburce, wani malalacin murmushi ya saki yana janye idanunshi ba karamin dariya ta bashi ba, ita kuwa mutuwar tsaye tayi tana kallon kyaun halittar da Allah ya mishi, ba karamin kyau murmushin ya mishi ba.
Ganin ze kara kallonta yasa ta ja baya ta fice da sauri, tean shi ya cigaba da sha yana murmushi lokaci lokaci bayan ya gama ya koma ya kwanta yana me sake rufe jikinshi, cike da Tunanin dalilin ciwon shi yana da wani abu guda idan har abu ya dameshi to se fa ya kwanta ciwo wadda kaman ya zame mishi jiki a daaa chan sede yanzu da ya mance menene damuwa hakan ya zama wani sabon abu a gareshi, so yake ya tantance wasu wasin da zuciyarshi ke yi ya tsayar da ita a matsaya ɗaya sede kwakwalwarshi ta kasa yardar mishi da amsa guda ɗaya tak dake amsa kuwwa daga cikin kanshi har zuciyarshi..

Tana komawa ɗaki ta samu Hamza na kiranta, ɗauka tayi sbd ya kusa yankewa suka fara waya yana mitar bata neme shi ba, daga karshe Aisha ya nema ta Haɗa su suka yi ta surutu, har junior ta makalawa yana ta kiran Daddy suna ta dariya ita dae idanu kawai ta zuba musu, hamza na matukar kaunar yaran nata Dukda be kai Raed ba sede she appreciate..

***

Juyi kawai yake yi from this side of the bed zuwa other side, numfashi da karfi yake ja sede kaman wadda aka shake mishi wuya numfashin baya wucewa zuwa cikin cikinshi hakan yasa yake ta kokawa da numfashin kaman me tashin asthma, zuciyarshi wani irin kuna take kaman an aje garwashin wuta, be saba ambaton Allah ba bare ya ambata yaji sauki, gashi dakakkiyar zuciyarshi bazata bari yayi kuka ba..

Cikin tsanani haka yayi ta juyi se daga baya Allah ya taimake shi ya janyo numfashin da karfi yana mikewa zaune lokaci ɗaya, saitin kirjinshi ya dafe yana haki kan daga karshe ya Haɗa kanshi da gwiwa idanunshi sun rine sun yi jajazir, ya jima be samu attack na panic ɗin nan ba se yau, ya kuma haɗu da wani mummunan mafarki da yayi..

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now