Page 25

293 20 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 25*

*FREE BOOK*

*Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Na gode matuka da adu'o'inku duk babu wadda ban gani ba... Allah ubangiji ya bar zumunci, baki yayi kaɗan ya furta irin godiya ta da kulawar ku... Wannan page ɗin naku ne masoyan Kowa yaga zabuwa🥰😍*

"Sam ba zan iya baka gudummawa wurin saɓawa mahaifiyarka ba ya hamza, mu cigaba da Adu'a kaji? Sannan kayi hakuri komai ze zo ya wuce kaman ba'a yi ba"
Ta faɗa a tausashe sbd yadda hamza ya fara bata tausayi da gaske yake sonta yake sossai.

Ajiyar zuciya ya sauke ba wai don hankalinshi ya kwanta ba suka yi sallama, ta jima zaune a wurin cikin tunani kan ta miƙe ta fito wurin yaran, yau har suka yi magrib da isha be dawo ba saɓanin yadda ya saba yi a gida tare da yaran.

Suna zaune a dining suna cin abincin dare ita kuma tana tsaye a kansu tana Haɗawa Junior custard ya shigo, sannu da zuwa suka mishi da kai ya amsa kawai ya wuce room ɗinshi.

Ba'a yi awa da shigar shi ba se ga Kimorah ta shigo sanye da wasu irin kaya da daga ka gani ka san wannan a addininsun ma an wuce gona da iri, kallo ɗaya ta yiwa dining ɗin tace
"Norah, baby Farrah hey!"

Kan ta wuce ɗakin Raed ɗin, lumshe idanu Hidayat tayi tana me kau da kai..

Norah ma fuskanta be nuna ta ji daaɗin zuwan na buduruwar mahaifin nasu ba, se cin abincin ya zama wani iri haka suka gama suka tarkata suka wuce ɗakin hidayat ɗin, duk yadda yaran suka so su sanya ta cikin hiran su bata iya shiga ba haka suka kyale ta..

"Ma....ma u..wa"
Junior ya fadi cikin harshen yara waenda basu iya magana ba, Norah na assignment ne Aisha kam har tayi bacci yayinda Farrah take riƙe dashi hakan yasa hidayat ɗin miƙewa tace

"bari in kawo maka junior"
Ficewa tayi Sam bata kula dasu ba seda ta zo tsakiyar parlorn, zaune yake a karkace system ɗaure a kafanshi yana kallon Umar series yayinda kwance daga jikinshi Kimorah ce tana ta mishi magana cikin kanƙan da murya.

Da sauri hidayat ta kau da kai ganin sun Haɗa idanu a hankali ta musu sannu kan ta wuce kitchen, buɗe fridge tayi ta ɗauki ruwa me sanyi ta sha sossai tana jin ba daidai ba gabaɗaya a yanayinta, ta jima tsaye nan ba abunda take kan ta ɗauki ruwa marar sanyi ta fito, bata kalli inda suke ba ta wuce ɗaki..

"Why are u looking at her?"
Maganan Kimorah yasa ya ɗauke kai daga kallon bayanta ya mayar system ba tare da yace komai ba.

"Meyasa se in ta maka magana kana share ni ne? Tun fa kan na tafi na dena gane maka ɗan kulani da kake wadda shi kaɗai ma yake sawa inji na fi kowacce mace ɗin ma yanzu baka yi, yanzu ko kwanciya nayi jikinka ka dinga ture ni kenan idan ba na nace ba sede in hakura, please in wani abu nayi maka ka faɗamun"
Tayi magana da harshen turanci cikin Raurau da idanu.

Yace cikin gajiya da komai da ma kallon..
"Please kimorah let me be! Ki shiga spare room ɗin chan ki kwana ko kije one of the rooms down stairs am not in the mood"

Zata yi magana ya ɗaga mata hannu tare da mikewa ya shige dakinshi, haka ya karasa duk abunda ze yi ya kwanta cike da wasu tunannuka..

Washegari tayi ayyukan ta fiye ma da yadda ta saba tashi don kan ace bakwai ta gama komai da komai tayi wanka, bata jira tafiyar yaran ba ta fice don Allah ya gani kwanan ta da wannan buduruwar tashi inuwa ɗaya ba karamin baƙanta ranta yayi ba, haka ta isa makarantar ma ajin bata wani fahimta sossai ba.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now