Page 35

280 24 3
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 35*

*FREE BOOK*

***Alhamdulillah! Ina matukar godiya da irin kulawar ku a gareni waenda suka kirani, waenda suka min SMS, waenda suka min saƙo ta what'sapp da ma masu min fatan samun lafiya a cikin groups Na gode sossai ALLAH ubangiji ya saka muku da gidan Aljanna, Allah ya bar zumunci.. Waenda basu sani ba kuma har sukan tambaya Bani da lafiya ne har yanzu kuma ina kan samun sauƙi ne, akallah na sha 12 bags of drip. Ciwo yake zuwa farar ɗaya saukin se a hankali... Ku cigaba da sani cikin Adu'o'inku Allah ya bamu duka lafiya me anfani🥰🙏***

**Wannan shafin sadaukarwa ce gareku daukacin masoyana❤️❤️**

%%%%

Wani irin kakkarwa jikinshi ya ɗauka kaman ana buga mishi gangi a firgice a kuma razane yana kokarin miƙewa sede saɓanin hakan kifewa yayi yana me cigaba da son yin magana jikinshi babu inda baya rawa..

Da sauri mutumin ya durkusa gabanshi yace
"calm down Yaya buba, nine dae Usman ba wani ba... Me ya sameka kake cikin wannan mawuyacin halin kai kaɗai? Ina Mama? Ina Aisha da abunda ke cikinta?"

Ai kakkafewa idanun buba suka fara lallai lallai yana son yin magana sede ya kasa se hawaye sharrrr suke zubowa, da kyar ya iya fito da Kalmar
"Ina Aisha?"

Usman yace
"ban gane ba yaya buba?"

Badi'ah dake makale jikin kofa tace
"Hmmm ai Alhaji bana manta irin cin kashin da buba yayiwa Aisha da abunda ke cikinta korar kare shekaru da dama, korar da yayi sanadiyar tsananin fushin mahaifiyarshi gareshi wadda ba tantama sanadiyar shiganshi wannan hali kenan muma gashi muna fama babu cin yau bare na gobe"

Dabas haka Alhaji Usman ya zube gumi na tsatsafo mishi ko ta ina, idanunshi suka rine a take suka juye zuwa wani abu daban jikinshi har rawa rawa yake....

"Ya Buba! Innalillahi wainna ilahi rajiun..! Innalillahi wainna ilahi rajiun!! Ka kori Aisha da abunda ke cikinta??? Aishar tawa?? Aisha fa??" Abunda kawai yake iya maimaitawa kenan.

Isa ne ya zo ya riƙe shi yace
"Alhaji kayi haƙuri a bi komai a sannu kaga kaima ba isashiyar lafiya ne da kai ba gashi babu wadda ya san kayi wannan doguwar tafiyar kar wani abu ya zo ya sameka..."

Hanky fari Kal dake tashin kamshi ya ciro ya share fuskanshi kan ya miƙe da taimakon Isa, ya kalli Badi'ah yace
"Ina mama? Karki ce min ta rasu don Allah"

Tace
"tana nan tana jin daaɗin rayuwar duniya ina mutuwa yanzu"
Isa yace a zuciyarshi 'ji jahilci'

"Address ɗin ta zaki bani"
Usman ya faɗa cikin wani irin mawuyacin hali.

Tace
"nima ban san wani Adara ba shi buba kaɗai ya san wurin"
Tana kai nan ta juya ta wuce ta san yau Alhaji Usman se ya daure buba har igiya tayi saura..

Kallon kwantaccen buba dake ta kuka Alhj Usman yayi, cikin tausayawa Dukda ƙasan zuciyarshi akwai daci da raɗaɗin abunda Buban ya mishi wadda har Abada baze gogu ba idan ba Hasken idaniyarshi ya gani ba sede yace

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now