Page 15

249 18 4
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 15*

*FREE BOOK*

Abunda idanunta ya faɗa kai ne yasa tayi hanzarin ɗaukewa tana runtse idanu, mace a kan jikinshi? Daga gani ma ba musulma ba?
Innalillahi wainna ilahi rajiun.. Wani irin rayuwa suke yi a gidan nan?..

Tayiwa kanta tambayar tana iya kokarinta wurin hana jikinta  ɗaukar rawar da ya fara, zaune yake bisa couch na ɗakin me taushi sanye da pants/boxers wadda be kai gwiwa ba kana iya ganin murɗaɗɗiyar jikinshi gabaɗaya, wadda gargasa yake nan kwance lublublub, a kan faffaɗar kirjinshi wata kyakyawar yarinya ce daga ganinta bata san me wani talauci ba, ta ci gayu ga nails an yi fixing dressing rabi jiki a waje kwata a rufe..

Daga idanunshi yayi ya sauke a kanta se ya ɗan tsaya yana nazartarta ganin yadda tayi wuri wuri, jikinta na rawa idanunta a runtse, magana yake shirin yi Wayanshi ya sake daukar kara..

"Handsome pls pick this phone samu mu huta da ringing.."

Dauka yayi cikin yanga ba wai don Kimorah tayi magana bane yasa yake so ya ɗauka no kawai ya ga ya kamata ya ɗaukan ne ya ɗaga..

"Daadida please.. Don't spoil my mood yanzun nan, I don't really know what's ur problem mutumin nan tun farko fari yace baya so na, yace he hates me nd hates everything abt me and I also fucking hates him..! You lied to me akan baki da lafiya u made me went to Nigeria but at last u saw what happened... I promise idan baki dena min maganan mutumin nan ba zan yanke duk wata alaka da zaki sameni ta waya am damn tired with ur stress..."

Shiru yayi yana sauke numfashin masifar da yake yana jin muryar matar na Kuka cikin kunnuwanshi wadda yake ji har tsikar jikinshi na tashi, yana son ta har ranshi itace mace guda da yake jinta har tsakiyar zuciyarshi kuma ita ce kadai ta rage mishi bayan yaranshi sede abunda take so daga gareshi shine yake kara nesanta su, be taɓa ganin macen da bata zuciya akan abu ba se akan Daadida she spent years tana abu guda bayan babu haske..

Zata yi magana yace
"I have to pray, good night"
Daga haka ya yanke wayan.

Mikewa yayi ya wuce toilet, Kimorah da take ta kallon Hidayat tun fara Wayanshi tace
"ke! Wacece ke?" Cikin harshen turanci don baturiya ce..

"New nanny!"
Tsaki ta ja tana kallon irin kyaun fuska da na sura da Hidayat ɗin ke dashi Dukda a cikin hijab take, wani abu ne ya tsaya mata a wuya, haka kawai hankalinta be kwanta da nannyn ba.

"Go to Paul ki ce mishi ya baki food ɗin ki kawo min am starving"

Fita tayi Paul shine cook ɗin masu aikin gidan kuma shine yake yiwa Oga abinci, ƙasa ta sauka a kitchen na kasan ta same shi tace ga abunda wata dake ɗakin oga ta ce..

Yana murmushi yace
"Kimorah.. Is her name she's the only fiancee of oga, ita kaɗai ta ciri tuta a cikin dubban matan da suke crushing a kanshi from different part of the world"

Kai kawai ta gyaɗa, banda faɗuwa babu abunda gabanta yake.. Zuciyarta ke tirsasata shiga hurumin da ba nata ba sede fa idan ta tuna da tarihin nan na mutanen annabi Musa waenda aka hana su kama kifi ranar Asabar se ranan Lahadi da kuma sauran ranakun se su je su ajiye abun kamun kifin ranar Juma'a se ranar Lahadi da safe se su zo su ɗauka wai su zasu yiwa Allah dabara..

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now