Page 14

234 22 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 14*

*FREE BOOK*

*Afuwan today I wasn't myself abubuwa sun cunkushe min ayi hakuri da wannan*

No.1.3 Le Marais
4th Arrondissements, Saint Thomas d'Aquin.

Shine sunan home Address da taga sun yi horn daga bakin hadaddiyar gate ɗin, gabaɗaya layin gidajen ba kananun Gidaje bane, Gidaje ne da suka haɗu suka kuma gaji da haɗuwa daga nan inda suke suna kallon Effile tower dab dab dasu kaima ka san me zama kusa da Effile tower ba karamin abun duniya ya tara ba..

Harabar gidan kaɗai abun kallo ne, riƙe da hannun Aisha suka sauko kaman yadda aka buɗewa Moh Raed ya sauko rungume da Junior, ma'aikatan gidan ne a jere cike da tsantsan girmamawa suke mishi welcome..

Hannu kawai ya ɗaga musu ya juya ga wata farar baturiyar mata yace
"Miss Mary this is the new nanny, show her around..!"

Cike da girmamawa tace
"Noted sir..!"

Daga haka ya miƙa mata junior ta zo ta karɓe shi cikin taka tsantsan, Juyawa yayi ya wuce rike da hannayen girls ɗin nashi kowacce na zuba shagwabanta da complain ɗinta..

"You welcome, am miss Mary I am the house keeper, can I please show you around Miss...."

Hidayat tayi murmushi tace
"Hidayat.. Thank you nice meeting you"

Miss Mary ta sake cewa
"Wlcm miss hidayat"

Daga haka suka nufi ciki bayan ɗaya daga cikin mazan da bata san aikinshi ba ya turo musu akwatunansu, babban parlor ne wadda ya haɗu iya haduwa komai na more rayuwa akwai a cikinshi banda sanyin Ac da kamshin freshener babu abunda yake tashi. Daga gefe suka hau wani steps zuwa sama shima again wani parlorn ne different design da wadda suka bari shima a kyau kam karshe ne har kasa tantance wanne yafi kyau hidayat tayi..

Aisha dake rike da Ɗayan hannunta jikinta yayi sanyi wadda hidayat ta san musababbin ganin su Farrah da basu yi welcoming nasu bane, sbd yarinyar haka take idan ka nuna mata baka sonta tana iya yinta wurin ganin ta kaurace maka duk zakwaɗinta kuwa..

Babban ɗaki ne me ɗauke da gado da wardrobe, coffee table da haɗaddun kujerun su, white curtains da beddings ne se sanyin Ac ke tashi har da TV akwai a ɗakin. Miss Mary tace

"this is ur room Miss Hidayat freshen up nd I will show u to d kitchen nd the girls rooms"

"thank you!"

Abunda hidayat tace kenan, bayan Miss Mary ta fita hidayat ta fara yiwa Junior wanka kan tayiwa Aisha, itama tayi suka sauya kaya suka yi sallah nan ma fa se guessing gabbas tayi sbd bata ga dae musulmin da zata tambaya ba kab gidan..

Suna nan zaune Aisha na wasa da kumatun Junior aka yi knocking hidayat ta mike ta je ta buɗe wata mata ce daban ta mata murmushi tare da mika mata tray ɗin dake rike a hannunta na abinci..

French fries ne da chicken se ketchup da ruwa, karɓa tayi tare da godiya.
Bayan sun gama cin abincin miss mary ta dawo tace sir yana son ganinta..

Mikewa tayi tare da gyara gyalen kanta ta ɗauki Junior Aisha ta biyo bayanta suka fito, relaxed suka same shi a parlorn na saman hannunshi news paper ne yana dubawa ya sauya kaya zuwa three quarter da armless shirt, kanta ƙasa ta zauna a kan center rug ɗin tace

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now