Page 33

304 28 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 33*

*FREE BOOK*

**Aunty safeeya da maman sadiq😍😍 wannan page ɗin naku ne kuyi yadda kuke so dashi son so❤️**

"Ya hamza don Allah ina so ka saurare ni da kunnen basira, karka fassarani da abunda yake ba tsarina bane tsarin Allah ne, Raed ya taimaka min a sadda bana cikin hayyacina ina kan gadon mutuwa ta da baƙin cikin rayuwa da kuma baƙin cikin ɗa namiji, da taimakon Allah da na Raed aka yi mini aiki cikin sa'a, a sannan yarana were stranded shi ya taimaka ya basu natsuwa da kwanciyar hankali, a sadda mahaifin Usman ya kashe min yaro na fito titi bani da maraba da mahaukaciya Raed shine ya zo ya taimaka min zuwa asibiti he did his best Amma kwanan Usman ya riga ya kare ya tafi, Raed shine ya ciyar a wannan wurin makoki har aka watse wadda uban da ya haifeshi be iya mishi ba bayan yayi ajalinshi, taimakon wannan bawan Allahn be tsaya iya nan ba, bayan Yusuf ya wulakanta ni iyayenshi sun koreni...mugaye suka so hallaka min yarinya su hallaka rayuwata Raed shine ya bayyana ya taimaka mana, ya dawo min da murmushi da farin cikina, ya bani dama me girma a rayuwarshi, ya maida ƴaƴana tamkar nashi ina zaune a gidan Raed ne da sunan aiki amma kudaden da yake kashewa ni da yarana yafi karfin albashina na shekara, please put yourself in my shoes kana tunanin akwai wani abunda wannan bawan Allahn ze nema daga gareni in kasa mishi?"

Wani irin bakin miyau hamza ya hadiye, yana jin wani irin turirin zafi na ratsa jini da jijiyarshi, zuciyar shi tayi baƙi kirin.. Be iya magana ba ta cigaba.

"Kayi hakuri da abunda zan faɗa yanzu, idan duk aka jingine sadaukarwar Raed ga rayuwata beside all that ina son shi, ba zan ce ga sadda na fara ba sede na san cewa a yanzu Raed shine farin cikina, kayi Hakuri ka cigaba da zama a matsayin yayana na riga na ba Raed ragamar rayuwata....."

Katse ta yayi yana zub da hawaye yace
"Hidayat ba se kin ce ban kai Raed kuɗi ba, ba se kin sanar dani Raed ya fini suna da tashe ba, ba se kin tabbatar min da cewa Soyayyar da kika fara nuna min tun a baya yaudara bace, ashe fakewa kawai kika yi da hajiya... Hidayat ba zan iya hakura dake ba, wlh ko duk abunda na mallaka zan iya baiwa Raed a matsayin sadaukarwar shi gareki ya bar mini ke, don Allah karki hukuntani da rabuwa don ba zan Jura ba"

Hawayen da ya zubo mata ta share...
"Mutum baya auran matar wani ya hamza, kana da ilimin addini ka sani komai ya faru already a rubuce yake, kar son zuciya ya sa ka fassarani a baibai, kuɗi kuma ba ze taɓa sayan sadaukarwar R....."

Faɗuwar abu taji da karfi, se taji ihun Hajiya tana kiran sunan Hamza, ruɗewa tayi bata kashe wayan ba tana ji hajiya na ihu tana kiranshi da jijjiga shi, tana ji har sadda aka fita dashi asibiti kan ta kashe ta kife fuskanta bisa tafin hannunta tana zub da hawaye cikin damuwar halin da ta jefa hamzan ciki.

Ta jima anan kan wayanta ya sake ɗaukar kara ta duba se taga layin zainab ne don tayi saving..

Ɗagawa tayi tare da sallama, zainab na kuka tace
"Hidayat don Allah kiyi hakuri da abunda nayi miki, nayi shi ne out of bacewar tunani da hankali, na auri hamza ne ba don yana so na ba se don soyayyar da ni nake mishi, a farkon aurenmu ya duba kamata da cancantata ya fara bani kulawa har zuwa sadda na samu cikinshi hankalina a kwance yake, sede daga sadda kika bayyana cikin rayuwarmu na rasa gane kan Hamza, na san halin matan yanzu a yadda hamza ya gigice a soyayyar ki se nayi zaton aikin asiri ne hakan yasa na kira na miki barazana ga mamaki na har yau baki fadawa hamza ba, don a yadda yake sonki na san da kin faɗa mai da watakila zamana ya kare a gidanshi, wannan dalili yasa kunyar abunda na miki ya baibayeni har nake jin zan iya kiran ki in baki hakuri sede ban yi hakan ba don hankalina be kwanta ba se yanzu na samu dama, don Allah kiyi hakuri.."

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now