Page 27

263 23 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 27*

*FREE BOOK*

*Afuwan jiya kun jini shiru was very busy ne*

Lip ɗin shi ya ɗan cija yana kau da kai daga kallonta, yaran ta zubawa abincin se ta zuba nata zata wuce ɗaki ya ce
"Miss hidayat! Why can't u eat here?"

Farrah tace
"yes please you always don't like eating in the dining with us"

Lumshe idanu tayi tana jin yadda bugun zuciyarta ke harbawa, dawowa tayi ta ajiye plate ɗin tare da ɗan jan kujera ta zauna, daga su har yaran babu wadda ya sake magana se junior don ta hana su magana yayinda suke cin abinci, Sam a takure take don lokaci lokaci tana iya jin kaifin idanunshi a jikinta alamun yana kallon ta, hakan yasa take cin abincin kaman baby jikinta na mutuwa a hankali kaman yadda nashi ma yake amsawa.

A duk sadda ze ga lips ɗinta yadda take tauna abincin kaman wani jan aji ko yanga wadda ya san duk ba haka bane rashin sabo ne kawai da ci a haka ɗin tunda bata yi ɗin, se yaji tsikar jikinshi na neman tashi... Tsammm haka yake shagala da kallon nata, hannun abincin ta kuwa har mantar dashi inda yake yake yi, sun riga sun saba da cimar kasashe barin ma French dishes Amma yanzu da ya kan zauna yaci abin da ta girka se yake jin ba ze iya cigaba da cimar Paul ba.

Ita kuwa askin da yayi ne yake ɗaukar hankalinta, a hankali take satar kallon kan nashi da lowcoat ya maidata se ya kara mishi wani irin kwarjini da haske, yanzu ne take Kallonshi as cikakken musulmi don in zaka ɗau lokaci kana Kallonshi kana iya hango taɓon sallah da ya fara yin baƙi daga goshin shi.

A duk sadda idanunsu zasu haɗu se su wani basar kaman ba Satan kallon juna suke ba, haka dae aka gama cin abincin ta tattare wurin suka koma parlor anan suka cigaba da tarihin annabawa inda take basu na Annabi Musa da firauna, sossai nan kam ya sakar mata idanu yana kallo wadda wani lokacin har kakarewa take saboda yadda gabaɗaya ta rasa natsuwar ta take neman Rikicewa..

Fahimtar hakan ya saka shi sakin murmushi me sauti, tarihin da ba'a karasa ba kenan ta gudu don ya hanata sukuni da kaifaffun idanunshi.

Kaman yadda yace ɗin kuwa haka ta shirya Dukda tana Tunanin CA ɗin ta kaman wasa ta duba group chat ɗinsu se taga an yi canceling hakan ya bata natsuwar tafiyar, washegari da yamma suka fito duk a shirye.

Sanye yake da wasu designers shirt and trouser na kamfanin Dolce and Gabbana wadda daga kallon ido kaɗai zaka fahimci ba kananun kuɗi ne aka kashe wurin sayar su ba, kafafunshi as usual sanye da rufaffun takalma, facing cap baƙi da kuma face mask baki ne a fuskanshi, hannunshi ɗaure da Iwatch na kamfanin Samsung. Ba karamin kyau yayi ba barin ma yadda yake tafiya cike da mazantaka.

Daga gefenshi yaran ne kusan dukkansu riga da wando ne jikinsu se suka daddaura after dress me shara shara da kananun designers half sunna da daga gani zaka san na asalin Larabawa ne banda duwatsu babu abunda ke walwali a jikinsu, Junior sanye da kananun kaya shima me kyau rike a hannun Norah, murmushi yake saki sa'i da lokaci idan yaga yaran a haka tare dashi se yake jin cikakken farin ciki me sanyi wadda be san dalili ba.

Duk mota suka shiga bayan ya karɓi junior, agogo ya duba yana me mata uzuri dukda jira na daga cikin abunda ya tsana amma se ya lura Inde har itace ze jira baya jin ginshira da jiran, ya san shirya yaran nan ne ze hanata yin nata cikin natsuwa, kaman an ce ya ɗaga kai ya hango ta tana tahowa..

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now