Page 40

282 24 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 40*

*FREE BOOK*

Shiru parlorn ya ɗauka Aisha na riƙe da Hidayat har lokacin ta ɗaura kanta bisa cinyar ta tana shafawa, Allah kaɗai ya san me ke tafiya cikin ran Raed don gabaɗaya be taɓa sanin menene ainihin ciwo a zuciya ba seda yaga irin kalar kukan da Hidayat take yi, gabaɗaya he wasn't his self yana riƙe da Junior da ya fara rikici, hamza na zaune gefen Abba da yayi shiru kawai amma shi kaɗai ya san me ke tafiya a zuciyarshi.

Daadida ma na zaune gefenta buzayen nan ne namijin yana riƙe da Hajiya da take ta so ta fisge, gyaran murya mahaifin Rashida yayi yace
"Toh Alhamdulillah aka ce komai yayi farko zae yi ƙarshe, sannan duk nisan jifa ƙasa zata dawo, abubuwa da dama sun faru wadda kawunanmu duka suka kasance cikin duhu Dulum tunda ga wacce aka tabbatar da mutuwar ta zaune a gabanmu, sannan ga hajiya dake wasu maganganu kaman wacce ta samu taɓuwar kwakwalwa, na tabbatar kowa a nan yana son sanin me ya faru? Taya abubuwa suka kasance a haka? Yaya kowannenku yayi rayuwa?"

Shiru ya ɗan yi kan ya cigaba
"Aisha! An auro ki an raboki da iyaye da en uwanki aka tsallake gari ya gari aka kawo ki har garin Kano, aka kuma damka amanarki hannun Hajiya Balaraba, ta karɓa hannu bibbiyu wadda seda kowa yayi sha'awar zamanku ake yiwa Usman dacen samun maatan kwarai kwatsam se kuma abubuwa suka juye, shin me ya faru?"

Ba tare da ta kalli hajiya balaraba ba tace hawayenta ya kasa tsayuwa
"Kaman yadda duk kuka sani sunana Aisha haifaffiyar garin mambila na jahar Taraba, na taso nayi rayuwa da iyaye na kaɗai ba tare da wani ilimi akan zama da kishiya ko kishi ba, ko da aka kawo ni garin Kano wallahi da zuciya ɗaya na shiga gidan yaya balaraba, a yadda ta karɓeni ta riƙe ni kaman ƙanwarta kowa se yayi sha'awar zaman mu, da ita zamana lafiya amma da mijina gashinan.... Mun Rayu cikin wannan aure da daaɗi ba daaɗi, dukda son juna da muke, matsalar da muka fara fuskanta shine a duk sadda ranar kwana na ya zagayo jini ne ze balle min baze tafi ba har se ya bar wurina ya koma wurin balaraba, tun bamu damuwa har abun ya zo ya fara damun mu saboda ina neman shekara da aure babu abunda ya taɓa shiga tsakaninmu.

Da farko iyayena na so samu da matsalar, don damuwar har ta saka ni fara rama Dukda Alhj be taɓa nuna damuwa ba yana hakuri yana kuma Adu'a nima yana kokarin kwantar min da hankali da cewa lafiya ta ƙalau Dukda kankatar shekaruna na san ba lafiya ba, ranan muna zaune da Yaya balaraba se take tambaya ta..

"Ni kam Aisha lafiyanki kuwa? Kwanan nan fa se rama kike tayi ko de mun kusa jin kukan jinjiri ne kike ɓoye min?"

Nayi murmushi nace
"wani irin kukan jinjiri bayan abunda ya dame mu ya damemu"

Tace
"ban gane ba?"

Nan na faɗa mata duk abunda ke faruwa, ban san kowa a Kano ba, bani da ƙawa bayan mahaifiyata a lokacin kuma sede ziyara, basu da waya a gida bare in faɗa mata damuwata ta waya, na ɗauki dukkanin yarda da amana na baiwa yaya balaraba, tashin hankalin da ta shiga a sadda taji wannan labari ko Alhj se haka, tayi ta damuwa tana maimaita maganan bayan kwana biyu ta nemi mu je wurin wani malami ya duba matsalar kilan mutanen ɓoye ne.

Ban yi mata musu ba na tambayi Alhj, ze nuna rashin amincewa na saka mishi rikici don a ganina ba shine a cikin matsalar ba, Allah kaɗai ya san irin azabar ciwon mara da nake sha a duk bayan kwana biyu, haka ya kyale mu muka tafi malamin nan ya tabbatarmin da matsalar sheɗanu ne ga abunda za'a kawo a fara jinya.

KOWA YA GA ZABUWA...Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang