Page 30

280 27 10
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 30*

*FREE BOOK*

*Fav sis🥰❤️ wannan page ɗin naki ne I love you ok😘**

**Allah in ga Ruwan comment in ba haka ba tohm ni de Zaku jini a salansa🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️**

Garin yayi lublub kaman hadari Dukda ba hadarin bane sede tarin ni'ima da garin yake dashi shine ya ɓoye ranan a irin wannan lokacin, tana ta kallon hanya Dukda ba tafiya me nisa suka yi ba suka iso wani gaɓar ruwa me cike da tarin boats Parke a bakin gaɓar daga nan kana iya kallon effile tower Tarr sbd ginin da ya riƙe shin a kan ruwan yake.

Buɗe mata kofan da Paul yayi shi ya yanke mata Tunanin abunda ta zo yi anan ɗin, bayan ta sauko ya nuna mata wata mata baturiya yace
"she will guide u ma!"

Tace
"wait! Are you leaving?"

Yace
"yes ma! My work here is to just drop u and go back home"

Kai ta gyaɗa ya shiga motan ya fice kan ta kalli matar dake gaisheta ta amsa, jagora ta mata zuwa wani tamfatsetsen jirgin ruwa me tsananin kyau fari Kal, wani keɓantaccen wuri daga nan sama da yake kawace da tables farare ta ajiye ta tace
"enjoy the view of seine river ma"

Sossai kyaun wurin ya tafi da ita, ko don girman jirgin ne ko kuma don kyaun shi ne yasa bata ji wani alaman tashin inji ba kan ta ankara dae taga jirgin yayi nisa da bakin gaɓar, mikewa tsaye tayi ta taka a hankali ta karasa wurin karafunan jirgin ta rike tana kallo, masha Allah..

Bata taɓa ganin kayatuwar wuri haka ba, waennan karafun na Paris da ake kira effile tower an kawata shi da wuta blue da ja se walwali yake yi, se ta jita a cikin wani ni'ima na musamman wurin yayi shiru hakan ya saka mata peace of mind, zuciyarta blank ba Tunanin komai se kyau da ni'imar kogin.

Bata san iya adadin lokutan da ta dauka a haka ba wata mata daban da na farko ta zo tace
"weldone ma! Oga said it's time for prayer and dressing"

Kallon kayan jikinta tayi me ya faru zata chanza? Bata yi musu ba tabi bayan matar suka dan sauka cikin jirgin kan ta buɗe wani wuri suka shiga, wow ashe akwai wuri haka a jirgi bata taɓa sani ba se yau, parlor ne me ɗauke da ɗaki da kitchen da toilet, kuma komai akwai, tana ta aikin mamaki har ta nuna mata yadda zata yi anfani da bayin ta fice.

Da tayi alwala se ta tsaya kallon madubin bayin tana kallon kanta, lokuta da dama ta kan bace a tunani in zata ɓata lokaci a gaban madubi se ta shiga kokonton itace wannan ko wata me kama da ita, gabaɗaya ta tashi daga wanchan hidayat ramamma me idanu kaman na Mayu ta koma wata classic chic, ita kanta tana son yadda take tafiyar da rayuwar ta da kuma tsarin dressing ɗinta a natse ba hayaniyar kaya se na tsantsar kyau.

Fitowa tayi ta gabatar da sallahn la'asar ɗinta don ta samu sallaya a shimfiɗe da katuwar ƙimar jalbib a cikin ledan shi ta ɓare.

Bayan ta idar matar ta dawo rike da wasu akwatuna guda biyu tace
"permit me to dress you ma!"

Kai ta gyaɗa mata tana kallon ikon Allah, ita fa duk bata san me wannan ɗin yake nufi ba kuma, haka dae ta daure ta yi yadda matar tace a take ta fara rangada mata light nude makeup da yayi mugu mugun blending da skin color ɗinta ya bata wani astonishing color me fusgan hankali.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now