Part 22

280 20 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 22*

*FREE BOOK*

"ASSalamu Alaikum pls can I sit here?"
Ta faɗa tana kallon Hidayat.

Murmushi tayi mata tace
"Wa'alaikumussalam warahmatullah, bismillah..!"

Zama kyakyawar matashiyar black beauty tayi tace
"thank u, am rashida from Nigeria and you?"
Tayi murmushi tace
"masha Allah, nima sunana hidayat daga Nigeria"

Wani irin zaro Idanu Rashida tayi tace
"kaiii wai dama ke ƴar Nijeria ce? Wow kin san Allah kullum ina kallonki na ɗauka irin Larabawa lebenon ɗin nan ce, masha Allah sister u r so beautiful"
Tayi magana tana kallon orange gyale da Hidayat ɗin tayi wrapping ya fito da fuskanta dake nan smooth gwanin kyau.

Dariya ta ba hidayat wadda seda ta dara, tace
"haihuwar Nijeriya girman Nigeria kuwa!"
Ita dae Rashida na ta mamaki ga hausa radau bakin hidayat kam, tace

"Ina karanta MBBS second semester 100lvl ke fa?"

Tace
"law, nima second semester 100lvl, ashe tare muka shiga"

Rashida tace
"ai ko na samu ƙawa dama tunda na zo ni kaɗai nake yawo kaman aljana"

Hira suka cigaba da yi, rashida buduruwa ce kuma wayayyiya daga ganin ta kuma ƴar gidan manya ce gata da surutu, nan take suka saba da Hidayat, kan a tashi har sun shaku tare suka fito daidai lokacin da taji saƙo a wayanta..

Dubawa tayi taga an
"at the entrance of ur school just passing-by nd I guess it's ur closing time, can I pick u up?"
Duba sunan ta sake yi
"Sir Raed"

Tana shirin dauke idanu kenan kuma wayan ya fara ringing
"ya hamza!"

Ɗagawa tayi ta gaida shi ya amsa yace
"Ina gate ɗin ku kin tashi ne?"

Rikicewa tayi tace
"am uhmm ai.. ai na wuce tuntuni"

Shiru yayi kan yace
"is ok, zamu haɗu anjima ko?"

Kai ta gyaɗa tace
"in Shaa Allah by the way it's Friday half day ne ai"

Yace
"ok see u later"

"thanks" ta faɗi tana kashe wayan.

Seda ta tsayar da Rashida na mintuna taga tafiyar hamza kan suka fito sallama suka yi da Rashida ta tafi ita kuma ta nufi motan cikin tafiyan ta na natsuwa, in ka ganta bazaka ce ta haihu har uku ba, yarinya ce wacce ko 25 bata rufa ba amma kaddara da rabo ya zaɓa mata wahalar rayuwa.

A jikinta take ji kaman ana kallonta sede batayi kuskuren ɗaga kai ba har ta isa motar ta buɗe gaba ta shiga, sanyi da kamshin motar na dukanta.

Sanye yake da kayan kwallo har takalmi da alama shima tun safe se yanzu yake shirin komawa gida, cikin muryarta me sanyi tace
"Good Afternoon sir"

Ba tare da ya kalleta ba Yace
"Afternoon how's studies"

Tace
"Alhamdulillah!"

Babu wanda ya sake magana a cikinsu banda qira'ar minshawi dake tashi se take jin wani sanyi sanyi na shiganta ga tausayinshi na rufe ta don da gaske yake shirin koyon Addininshi dole ya tsani Mahaifinshi yanzu ma Allah ne kaɗai ya san da irin damuwar da yake kwana.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now