Page 21

257 21 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 21*

*FREE BOOK*

"In shaa Allah we will all be happy again..!"
Da kyar ta iya faɗan hakan tana share fuskanta tare da ƙin Kallonshi.

Be fahimci me take nufi da we will da tace ba hakan yasa ya miƙe tsaye yana me ci gaba da kallonta ya kai babban yatsanshi ya sosa giranshi kan ya juya ya fice kawai.

Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke tare da bin bayanshi da kallo har ya fita, mikewa tayi taje toilet ta wanke fuskanta Tare da fitowa ta sauka kasa ta ɗauko junior wurin Miss Mary, ta dawo ta karasa Haɗa musu table ɗin duk fuskanta ba wani fara'a tana jin hayaniyar su daga wani room kuma na gidan dake daura da na Dad ɗin nasu bata De leka ba ta koma ɗaki tare da shayar da Junior tana Tunanin mafita, ta yadda zata shiga rayuwarshi a hankali ta samu ta karkato da hankalinshi zuwa bautar Allah ɗaya.

Har dare yaran basu dawo sun dame ta ba, ko da Aisha ta shigo ce mata tayi Daddy ne ya hana su zuwa kar su takura ta she need a space, murmushi kawai tayi ta shirya yarinyar ta kwanta.

Norah ma ta shigo ta mata good night ta kalleta tace
"Norah hope u prayed?"

Kai Norah ta gyaɗa mata tace
"we prayed with Aisha in my room"

Murmushi tayi tace
"ok kiyi adu'a kan ki kwanta"

Tace
"good night miss hidayat!"

Ta juya ta fice.

Kwanan Father biyar ya tafi duk yadda ya so ya sa Raed sallamar Hidayat kin amincewa yayi, dama kuma su abunda basu iya ba takurawa yara Dukda hidayat ta fahimci sarai baya kaunar ta sede tana mishi uzuri don ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar Raed ɗin kuma ta san duk me ƙin ta a bayan umma ne.

Ta kan yi waya da ya hamza akai akai don shi da gaske yake son ta yake kuma yana so ya aureta anytime soon.

Sanadiyar shakuwarsu da Farrah kuwa shine rashin lafiya da tayi, hidayat ta kula da ita sossai wadda ya kawo kusanci tsakaninsu har yarinyar ta fara son ta, ta kuma fahimci daga miss hidayat har Aisha basu da wani nakasu kawai dae dama kishin Aisha take.

Zaune yake a parlor yana aiki a system ɗinshi yayinda yaran suke tare da Hidayat a ɗaki a irin wannan lokaci ne take musu tarihin annabawa, sanin yana parlor yasa ta fara first move ɗinta cikin danne fargabar da ya cika mata ciki tace
"mu yi tarihin nan a parlor"

Aiko da gudu suka fito itama ta fito, kallo ɗaya ya musu dukansu ya maida idanunshi kan abunda yake yi suka samu wuri suka zauna tare da saka ta a tsakiya.

Ba tare da ta kalleshi ba ta fara musu da
"yanzu bari mu fara yin tambayoyi akan darasin mu na baya, wa ze gaya min annabawa nawa Allah ya ambaci sunansu a Qur'ani?"

Dukkansu uku suka ɗaga hannu ta nuna Farrah.
Da sauri yarinyar tace
"25"

Hidayat tace "Attakbir"
Suka ce "Allahu Akbar"

"To wa ze kira min sunayensu ɗaya bayan ɗaya?"

Norah ta ɗaga hannu ta mike ta fara lissafo su daga kan Annabi Adam (As) har zuwa kan Annabi Muhammad (SAW) zuwa lokacin hankalin Raed ya fara yowa kansu.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now