Page 36

294 21 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 36*

*FREE BOOK*

A haukace ta shiga ɗakin ta janyo akwatinta da tayo tafiyan nan dashi ta fara watsar da kayan ciki idanunta har basu gani da kyau, Allah kaɗai ya san abunda ke going a cikin zuciyarta babu irin Tunanin da be zo mata a cikin kai ba, da kyar hannunta dake rawa ya kai kan wannan Waist bag ɗin (in baku manta ba kan ta bar gidan yusuf ta ɗaura shi bisa kwankwasonta bayan kuma taimakon da Raed yayi mata dashi kaɗai suka tsira sbd yana a waist ɗinta ne..laalita/ kasheni ka ɗauka duka sunanshi ne).

Buɗewa tayi ta fiddo wani ƙaramin box wadda a idanu zaka san ya jima sede a da ɗin ma ba abu bane me arha, da gudu ta mike ta koma parlorn tana haki ta ɗago box ɗin tace

"a cikinku waye ya san wannan...!"
Muryarta a rarrabe yake fitar da maganan.

A hankali Alhj Usman ya fara matsowa hannayenshi na rawa kana kallon rauninshi karara don hawaye ke zuba a fuskanshi muryarshi na rawa yace
"kwarai na san wannan box ɗin, sarƙa ce a ciki ni na kawowa Aisha shi a wata tafiya na na karshe da nayi kan rabuwarmu....."

Kuka me tsuma rai Hidayat take yi, lallai wannan shine mahaifinta, amma ta yaya? Buba da yake kawu kuma suruki a gareta ya cuce ta cuta mafi muni amma Duka nata mahaifin ne sila...

Girgiza kai tayi tare da saurin ja baya a sadda ya sa hannu ze riƙeta gunjin kuka take tana cewa
"Ashe ni ɗin ɗiyar sunna ce? Ashe ina da asali da tushe da kuma gata? Ashe ni ba ƴar zina bace kaman yadda aka lanƙaya mun har ya zama shine tambarina? Alhaji ka cutatar da rayuwana na Rayu cikin tsantsar baƙin ciki da jarrabawa duk a sanadiyar ku! Na rasa duk wani gata, nayi baƙin ciki nayi kuka! Sede ka san ban taɓa yi maka Adu'a ba? Kaman yadda uwar goyo na take faɗi kilan rashin sanin takamammen mahaifina ya sa iyayen mahaifiyata suka kore ta ta shiga duniya! I believed that and I live my whole life with that belief Taya zaka zo rana tsaka ka nuna min soyayya in yarda??? Me yayi sanadiyar rabuwarku ba tare da kun yi la'akari da ni ba? Me nayi muku da zafi haka? Al...."

Kukan da yake yi da tari ya sa ta kasa cigaba da maganan se kuka, Daadida tace
"Haba hidayat kar hankalinki ya gushe mana, na tabbatar babu dalili Usman ba ze taɓa wofintar da Aisha ba...!"

"Kuma be tashi nemanta da abunda ke cikinta ba se after good 24 years? Haba Daadida! Ki duba tsabar coincidence har ɗana na sanyawa sunanshi ba tare da na san sunan shi ne ba! Daadida kin kuwa san yadda na Rayu? Kin san baƙin cikin dake ƙasan zuciyata? Kin san irin fansar dake raina? An zalunceni, an ha'inceni, an cuceni an ci mutuncina, an tozartani da mahaifiyata da bata san komai ba... Duk saboda mahaifina da ya zaɓi nesa damu Daadida na sha kwana cikin azabar yunwa, na sha kwana cikin azabar ciwo,  cikin talauci da yagaggun kaya, har roko na yi don sanyawa bakina abinci, nayi rayuwa ba tare da sanin menene farin ciki ba kuma yanzu in zo in bugi kirji in ce ubana attajiri ne? Bana so....! Bana so....!! Na yafe wallahi na yafe..!!!"

Yadda duk ta haukace ta sauya gabaɗaya ya ɗaga musu hankali ba su kaɗai ba har Raed da ya gama bada umarni a shirya komai ze wuce Nigeria don ma 6hours ne daga jedda zuwa Kano, faɗuwar Alhaji Usman yasa ba su kaɗai dake parlorn ba har Raed ya nufi jirgin da sauri yana ambaton innalillahi wainna ilahi rajiun..

KOWA YA GA ZABUWA...Donde viven las historias. Descúbrelo ahora