Page 28

256 21 3
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 28*

*FREE BOOK*

**Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka, fatan duk muna cikin koshin lafiya, kwana biyu kun jini shiru lafiya ta ƙalau wallahi I was extra busy ne, I was occupied ta yadda ko online bana hawa se in ya kama so waenda suka min messages zan yi reply in na karasa natsawa kuyi hakuri! Waenda suka kirani kuma na gode🙏 Allah ya bar zumunci**

"Nace ku min bayani dallah dallah!!"
Ya daka musu tsawa a karo na babu adadi, gabaɗaya rayuwarshi be taɓa samun sukuni ko na miskala zarratin ba, komai yanzu baya mishi daaɗi, komai baya sa shi farin ciki, bakin cikin da yake kwasa da yaran cikinshi abu ne da baze faɗu ba.

A tsorace suka fara bayani dallah dallah sace sace da ake ta mishi sune suke yi suke rabawa tsakaninsu, yadda zarah ta sace kudadenshi suka ɗaurawa Mairamu, yadda suka yi ta Haɗawa Raed tuggu yana ɗaukan munanan mataki a kanshi.

A hankali wani irin sanyi ke rarrafowa yake lulluɓe shi kwarai laifi me girma ya aikatawa ubangiji da ya jarabceshi da waennan matayen, wacce ita ce jin daaɗin duniyar shi yayi silar mutuwar ta da hannayenshi, abunda yake taɓa mishi zuciya shine har karɓar diyya yayi amma yaronta ko biyar be amfane shi da kuɗin ba a Tunanin shi mamanshi shi take kashewa kudadenshi da suke ɓata.

Yunkurawa yayi da nufin rufe su da dukan mutuwa sede jininshi da ya hau a take ya saka ya yanke jiki yayi wani irin faɗuwa, ihu suka kurma dukansu uku suka yo kanshi da gudu, ganin mummunan yanayin da yake ciki yasa suka fita suka nemi taimako aka zo aka yi asibiti dashi.

Tashi ɗaya bayan dogon bincike likitoci suka tabbatar da irin faɗuwar da yayi da yadda jikinshi ya hau fiye da ƙima ya samu paralyze komai baze iya yi da kanshi ba.

Sun sha kuka a lokacin kam, kwananshi goma a asibitin yana cin wuya don ko magana a karkace yake fitowa, su kuwa tun suna jinyar da ɗan daaɗin rai suka fara mishi kawai na dole, don suna yi suna mita, ko Daadida basu kira sun sanar da ita abunda ke faruwa ba har aka sallamo shi ya cigaba da cin baƙar wuya saboda rashin kula.

****

Kira yake yana sakewa sede be same ta ba, haka baƙin ciki na cinshi ya dawo asibitin ya cigaba da kula da Abban shi zuciyarshi ba daaɗi, yana jin tsananin ciwo da idan har aka ce ya rasa hidayat babu abunda ze hana shi mutuwa, hawaye ke cika idanunshi yana maidawa shi karan kanshi be san wani irin soyayya bace wannan.

"Ham....za!"
Muryar Abba cikin Crack ya kira sunanshi saboda bacewa da yayi cikin tunani.

Da sauri ya mike ya iso kusa shi tare da kama hannunshi se hawaye sharrrr

"Abba yau Kaine ka kira sunana da bakinka? Ashe zan sake jin amon sautin muryar ka da kunnuwa na? Alhamdulillah ya Allah!"

Shafa kanshi Abba yayi a hankali yace
"menene? Yake damunka"
A rarrabe maganar ke fitowa.

Da kyar ya iya tsayar da hawayen shi yace
"Abba hidayat ce take so ta kashe ni! Abba na rasa me ke damuna a kanta anya ba wani sakamako bane soyayyar nan? Abba wallahi ji nake kaman zan yi hauka..."
Kuka ya ci karfin shi.

"Kana... Kaiwa Allah kukan ka kuwa?"

Girgiza kai yayi yace
"Abba Bana samun natsuwar yin ibada yadda ya dace, Abba na san hakkin aure na kuma san ina tauyewa zainab hakokkinta saboda masifaffen soyayyar da nake yiwa Hidayat amma na kasa controlling kaina in ba kaina natsuwar da ta dace..."

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now