Page 37

315 23 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 37*

*FREE BOOK*

Wasa kawai take da yatsun hannunta tana alwalar kuda wadda babu ruwa, motar ta ɗauki shiru banda sanyin Ac da fitinannen kamshin shi babu abunda ke tashi, yadda yake tuƙi kaman ba ze tafi ba tunda ya ɗauko ta yasa ta ɗan ɗago ta saci Kallonshi.

Da suke Gaisawa da Ummi kaman ranshi ba'a ɓace ba amma kallo ɗaya ta mishi taji bata so ta sake Kallonshi cikin wannan ɓacin ran ko ba Sanadiyarta ba bare sanadin ta, a hankali tace

"Paaapi!"
Be amsa ba Dukda muryar da tayi anfani dashi ɗin ba karamin shigarshi yayi ba, Raurau tayi da idanu muryarta na rawa tace

"am so sorry....! Na san ban kyauta ba amma..."
Kukan da yake son kubce mata ne yasa tayi shiru, kaman ze share ta sede ba ze iya ba, parking yayi gefen titi ya zuki iska ya fesar a lokaci ɗaya ya sanya hannu ya yaye hijab ɗin jikinta ya cire kan ya mirginota zuwa cikin jikinshi ya rungume.

Dukkansu idanu suka lumshe suna jin kewa, soyayya da kuma tausayin juna.

Hawayenta ne yake diga mishi har cikin fatar kirjinshi, ƙara sanyata yayi jikinshi cikin taushin murya ya ɗago haɓarta yace
"shhhh! Baby gurl you cried enough today pls don't start again now..."

Hannunta ta ɗaura bisa rigar shi ta kara riƙe shi jin yadda yake sake mannata da jikinshi cikin salo.
"My fatherrr....!"

"Shhhh baby don't say anything about him, ba laifinshi bane now u know who that evi...."
Da sauri ta saka tattausan hannunta ta rufe lips ɗinshi.

"Duk munin halayyar iyaye babu inda aka mana umarni da mu ci mutuncinsu ko mu zage su, Paapi I love you and bana son fushin ubangiji ya hau kanka saboda Baba Buba, pls find a place in ur heart and forgive him ɗan Adam ajizi ne..."

Kallon mamaki yake jifan ta dashi yace
"after all he have done to you? And my aunt? I mean ur mother?"

Kai ta gyaɗa tace
"Besides ni na yafe mishi, please forget the past and focus on the future..! Kaga ba don shi ba kila we will end up as cousins not lovers, ba don shi ba kila da baka min taimakon da ze sa in ji duk duniya babu wadda bana so ko kuda ya taɓa ba kaman kai... Maybe I wouldn't have given birth to Usman, Aisha and Junior you! Ka ga every disappointment is always a blessing..! Had it been be maka abunda ya maka ba da pastor polycap be ɗauke ka ka zama the greatest footballer of our Era ba..."

Yadda ta kare maganan da wink yasa ya saki wani malalacin murmushi, lip ɗinshi ya kai yayi pecking idanunta da ta lumshe, ya dawo yayi na hagu kan yayi kissing nose tip ɗinta daga karshe ya dira a lips ɗinta.

Seda ya gaji don kanshi ya gyara mata kwanciya yana saka hannunshi na hagu ya tallabo chin ɗinta yana shafawa a hankali yace
"Baby gurl you are a blessing indeed! I love you"

Tace
"nima haka yayana!"
Fuska ya ɓata yana turo lips yace
"what?? What's nima haka again? I said I love you"

Dariya tayi har hakwaranta na fita tace
"love you more..!"

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now