Page 32

265 24 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 32*

*FREE BOOK*

"Assalamu Alaikum warahmatullah..!"
Dakakkiyar muryarsa ta shiga kunnenta ta aika mata da wani sako me karfi har tsakiyar zuciyarta, bata san sadda ta zauna ba.. Muryarta na breaking tace

"Wa'alaikumussalam warahmatullah....ina kwana?"

Seda ya ɗau seconds kan yace
"kuna lafiya?"

Tana jan kasan dankwalin kanta dake bisa kirjinta tace
"Alhamdulillah..! Yaran...su suna school"

Lumshe idanunshi yayi yana kishingiɗa da kyau yace cikin kasalalliyar murya dake nuna gajiyawa.
"I know! didn't call the kids, I called you die hard."

Shiru duk suka yi na seconds kan yace a sanyaye
"na kasa cigaba da jurewa, I cannot believe soyayyarki tayi min Illar da take son hana min daily activities ɗina, die hard for this 8days ni kaɗai na san irin halin da na shiga da na hora kaina da jin murya da kuma ganin ki, I gave you space ko zaki fahimci kema kina jin a little bit abunda nake ji but to no avail babu abunda ya chanza ko? You hate me ko?"
Daga muryarshi take jin ɗacin zuciyarshi duk sbd ita, hawaye ne ya gangaro mata tana ta son yin magana muryarta na rawa..

"It's OK! Don't cry u don't have to, I understand. Take care"

Har ze sauke wayan tayi saurin cewa
"wait!"

Lumshe idanunshi yayi yana sake rike wayan da kyau a kunnenshi kaman wani ne ze kwace..

"Am...am so sorry for hurting ur feelings, it was never intentionally, it's just hard to believe cewa ni hidayat nice Muhammad Raed ya zaɓa a matsayin Abokiyar rayuwa duk tarin mata masu aji, kyau, nasaba, dukiya da kyaun asali..."

Hawayenta ta share da tafin hannunta kan ta cigaba a sanyaye..
"U pleaded with me to share my heart ko da ba zan baka duka ba, Raed zuciyar hidayat gabaɗayanta mallakinka ce, ni da kai kaman ruhi ɗaya ne dake rayuwa a mabanbantan jiki...! Ka rokeni na baka dama.. Na baka a yanzu Raed, na mallaka maka ragamar rayuwata please Raed be my only husband, sirrina, farin cikina, make me ur only woman bcs u are my true and last love, I love you every second of every day....we missed you beyond words pls come back home paapi"

Tana kai nan ta sauke wayan kunya na rufe ta, da gudu ta tashi ta shige ɗaki kaman wata yarinya ta zube bisa gado tana rufe fuskanta ji take wasai ta sauke abunda ya tokare mata zuciya, ita kanta bata san tana son shi haka ba seda taji bakinta na amayar da zancen zuciyarta wadda ita kam bazata ce ga sadda ta tsara su ba.

Sako ne ya shiga wayanta, da sauri ta janyo ta buɗe.

"Thank you! Thank you so very much, you don't know how badly I wanted to hear you say that! U made me the most happiest person in the world, I love you for exactly who you are today and I will love you tomorrow and the day after very same day🥺😘"

Murmushi ta saki tare da ɗaura wayan a saitin zuciyarta tana lumshe idanu, ƙaurin abincin ta yasa ta tashi da sauri ooh soyayya ya sa ta mance abu ta ɗaura da sauri tayi kitchen tana murmushin kanta.

****

"Daadida she accepted me, ta bani dama a rayuwarta.."
Yayi maganan muryarshi na bayyana irin farin cikin da zuciyarshi take ciki.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now