Page 9

229 21 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 9*

*FREE BOOK*

"Aisha..! Mutum ne ya baki duka wannan? Ya aka yi kika karɓa? Me wannan..!"
A tsorace dukansu uku suka zubawa kuɗin idanu, bunch ɗaya na 1000 kenan har dubu ɗari, Kuka Aisha ta fara tana rantsewa wallahi ita bata ma san ya saka ba.

Ta yarda da ita sede tsoron kuɗin take in ya dawo yace yana son wani abu daga garesu fa? Usman ne ya kwaso suka mayar cikin envelope ta mayar cikin jakar ta ajiye, da taimakon yaran ta rama sallolin dake kanta ta basu sauran tea ɗin da spring roll suka ci, har yaran suka sake bacci bata yi ba Tunanin wannan mutumi ya rufe ta, wanene wannan mutumin? Me manufarshi na taimakonsu?..

Banda magungunanta da allurar da be saketa gabaɗaya ba da ta san ita da bacci a daren nan se Allah, tana lallaɓa talaucinta bata shirya cin mutuncin Yusuf ba Sam.

Washegari da safe da Aunty jamila ta zo hidayat ta tambaye ta akan wani Muhammad da ya taimake su, tace
"Raed ne nima se da na bar wurin yaran nan nake jin ya shigo, karki damu mutumin kirki ne sannan kyauta ce fisabilillahi ba da manufa biyu ba Inde shine duk shekara yana shigowa asibitin nan taimakon bayin Allah"

Ajiyar zuciya ta sauke kan ta mata godiya sossai bisa kirkin da tayiwa yaranta da ita kanta, bayan Abba da Muhammad itace mutum na uku da bazata manta da ita ba, da taimakon Aunty jamila tayi wanka, da snacks ɗin nan suka sake karyawa babu yadda bata yi da Aunty jamila ba ta ci snacks ɗin ta ƙi, ta so taje gidan na Hidayat ta samo mata kaya sede hidayat ta ƙi a Cewar ta hidimar ze mata yawa amma a baɗini bata son zuwa ne taga sirrin su.

Se da rana ya ɗaga sossai kan aka kawo mata yaron, lulluɓe cikin zanin ta da bismillah ta karɓeshi tana rungumeshi cikin jikinta ƙaunar yaron na shiga har jininta, leƙa fuskanshi tayi masha Allah babu abunda ya bar mata, hawaye ne ya zuba mata Aisha ta sa hannu ta share tace
"Mama yayi kyau dayawa ko?"

Murmushi tayi tace
"hawayen farin ciki ne da godiya ga Allah da ya bani wannan kyakyawar halittar a matsayin kyauta wadda babu mahalukin da ya isa ya baka shi banda Allah"

Kafin ta haihu sunan Abba ne yake mata kai kawo a zuciya ta kudiri aniyar idan har ta haifi namiji to Abubakar ne sede yanzu zuciyarta ya chanza, kiran sallah tayi mishi hagu da dama kan ta kira shi da suna 'Muhammad Raed'

Aisha tace
"Mama ya sunan shi?"

Usman dake ta kallonshi ta kalla tayi murmushi tace
"Sunan Daddy ya ci, Allah ubangiji ya raya shi yasa yayi halin me sunan"

Murna a Wurin Aisha ba'a magana an saka sunan Daddy haka kawai take ƙaunar Daddy Muhammad, ita kuwa Hidayat idanu ta zubawa yaron bayan ta sa mishi nono a baki ya kama da sauri yana sha, a zuciyarta take raya...

''Me sunanka is our life savior, shi ɗin kaman wani mala'ika ne da Allah ya aiko mana cikin tsanani, a ranar da be zo asibitin nan ba da kila na mutu tare da kai a ciki, da kila Usman ya ɓata kenan ya shiga gararin rayuwa walau ya zama ɗan daba, walau ya kare a almajiranci da wahala, da kila Aisha rayuwarta ya gama lalacewa a matsayinta na ƴa mace me kankantan shekaru babu wadda ta sani babu wadda ya Santa''

Hawayen da ya ɗiga a kumatun yaron ne yasa ya fara mirmir da idanu alamun son buɗewa, murmushi tayi tana share mishi ɗigon hawayen.

Satin su biyu a asibitin, da Aunty jamila ta gaji da ganin hidayat da kaya guda ita ta kawo mata kala biyu, yayinda yaron hidayat ta bata kuɗi ta karo mishi kala uku, kayan su Aisha kuwa in sun sa sau biyu se ta wanke asalin nasu su saka na kwana biyu ta sake wanke na Wurin Aunty jamilan, abinci safe rana dare saya suke a bakin asibiti, sati biyu da suka yi a asibitin har wani kiba suka yi na zama wuri ɗaya da hutu.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now