Page 44

295 22 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 44*

*FREE BOOK*

"Good morning..!"
Yayi whispering yana zare mata hijab ɗin na jikinta, murmushi ta saki me taushi tace

"Good morning, hope an tashi lafiya?"

Ƙara shigar da ita jikinshi yayi yace
"in akwai abunda yafi lafiya ma yau na tashi dashi baby gurl, sannu da aiki"

Ba tare da ta kalleshi ba tace
"sannu! Ammm se Naga kaman akwai namiji dake shigowa nan ko? Shiyasa na saka hijab"

Yace
"Nah! Daga nan har Paris babu namijin dake da hurumin shiga min parlor bare kitchen baby gurl, that was before"

Bata sake cewa komai ba ta ajiye kular da ta gama kwashe dafaffen Irish ɗin, se ta tsaya cikin kunyar ce mishi ya saketa ta gama Haɗa breakfast ɗin, Sam duka wannan bambarakwai take jin su wai namiji da suna Hajara, leƙa fuskanta yake yi daga wuyan ta yace

"wait! Baby gurl are you avoiding my eyes?"
Ya karashe da sautin smile, bata ce komai ba
Yace
"please don't! Kin fa riga kin zama rakumi ni kuma akalarki duk inda zaki je yanzu a tare dani zaki, so feel free around me we are already one and I love you ok?"

Duk yadda ta so sunnewa haka ta hakura kaman yadda ya faɗa kuwa duk inda tayi tare suke yi, breakfast ɗin ma kusan plate ɗaya suka yi da tea cup guda, bayan sun gama suka sake kwanciya bacci ba su suka farka ba se wuraren azahar.

Kitchen ta sake shiga bayan tayi wanka tayi sallah tayi pasta half wadda yaji vegetables, bata sa a kula ba sbd shima ya sauko yana tare da ita so a plate suka juye shi ya wuce dashi cikin parlor yayinda ita ta ɗibi drinks da cup, a tsakar parlorn suka zauna suka ci abincin cikin nishadi, bata taɓa Tunanin haka aure yake ba.

Bayan sun gama yace su je su shirya su tafi asibiti, cikin doguwar rigar Abaya ta fito maroon wadda yayi mugun amsar ta, ta rufe kanta da gyalen, wayanta kawai ta ɗauka ta fito a parlor ta same shi suka fita a tare hannunshi cikin nata.

Ko a motan ma hiran su suke yi na masoya fuskokinsu cike da nishadi wadda ze tabbatar maka hankalinsu a mugun kwance yake, a haka suka shiga asibitin riƙe da hannun juna, kunya ne ya rufe ta a sadda suka tarar da iyayenta a ɗakin da duka yaran tare da Daadida.

Daadida ta kasa shiru tace
"Aaa lallai se yanzu ake ganinku?"

Basu amsa ba se murmushi, ya gaida Abba, sannan Maami duk cikin jin daaɗin ganin da suka musu suka amsa, suma daga ka gansu ka san ma'aurata ne masu cikakken natsuwa da kwanciyar hankali, ita dae hidayat na ta fama da Junior dake tambayar ta ina taje ta barshi.

Baba Buba kallon su kawai yake yana hawaye tare da murmushin karfin hali, rayuwa fa kenan, lallai mahakurci mawadaci dubi yadda duk suke cike da walwala shi kuma gashi kwance yana girban abinda ya shuka.

Duk waje suka fita inda suka shimfiɗa carpet aka zazzauna ana hirarraki kaman dae yadda kuka san asibiti, anan ne ma Daadida ta kawo maganan ko za'a ɗauko matanshi duk babu me kira cikinsu yaji halin da yake ciki, a lokacin da yake bukatar su a sannan suka yi watsi dashi, su da baya so a sadda yake da mamora sune ke taimakon shi a yanzu.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now