Page 38

268 24 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 38*

*FREE BOOK*

Bata iya ta runtsa ba seda ta tabbatar da yayi bacci, ta kashe lokaci sossai tana kwantar mai da hankali a wayan har ta dena jin amsar shi, mikewa tayi ta watso ruwa ta zo tayi nafila tana me rokarwa mahaifinta lafiya tana kuma Rokon Allah yaji kan mahaifiyarta.

Washegari da wuri ta tashi da kanta tayi breakfast ta Haɗawa Abbanta ma breakfast wadda ze ji daaɗin shi, bayan ta gama taje tayi wanka a lokacin su Norah ma sun yi wanka suna tambayar ta ina taje jiya har suka yi bacci bata dawo ba?

Tace musu
"Dad ɗina ne be da lafiya I have to be there through out"

Aisha tace tana so ta ganshi, tace su shirya su je duka tare.

Bayan sun fito ta shiga wurin Daadida suka gaisa kan ta Haɗa mata breakfast ɗinta nan kan dardumanta don bata iya zaman dining wai na yara ne gwiwowinta se su sage, Albarka ta sa mata kan ta miƙe ta fito, tana rufe kofan yana rufo na parlor.

Idanunsu ne suka sarƙe cikin na juna, a tare suka sakarwa juna tattausan murmushi, kallonta yake daga sama zuwa ƙasa, sossai tayi kyau cikin Rigan lace da aka mishi ɗinkin manya, ya haɗu karshe ya kuma bi jikinta kasancewarshi milk da emerald green.. Ɗan kunnen kunnenta fashion marar girma ne emerald green se sarkan mamanta na gold dake wuyanta.

Shi kam as usual sanye yake da kananun kaya designers wando da riga black and ash, hannayenshi zube cikin aljihu, a hankali ya ciro su tare da warawa yana kallon idanunta, zare cute eyes ɗinta tayi kan ta make kafaɗa tana kallon kofan daakin Daadida, baki ya taɓe kan ya fara takowa zuwa gareta yana sakin murmushi ganin yadda ta sunne kanta kasa, shi kam ko a jikinshi ya rungumeta suka sauke ajiyar zuciya a tare.

Peck yayi mata a goshi yace
"Good morning Die hard!"

Tana motsa hannunta dake sanye cikin nashi tace
"morning paapi, hope ka tashi lafiya?"

Kai ya gyaɗa yana lumshe idanu sbd kamshinta dake aika mishi da saƙo yadda ya kamata, tace
"mu je kayi breakfast"

Ya kalli hannunta dake riƙe cikin nashi farare sol kyawawa a gyare tsab yace
"u rejected my proposal yanzu hannunki yayi somehow without a ring"

Murmushi tayi tana jan hannun nashi zuwa dining tace
"wani proposal kuma bayan na zama matar aure gabaɗaya, but that ring yana da kyau sossai fa!"

Yace
"I changed it with another one in mun koma zaki gani, baby gurl we are leaving together today right?"

Zata yi magana yaran da suka kalli baban nasu yanzu suka fara gaida shi, Junior har da saukowa ya zo wurinshi, ɗaga shi yayi ya cilla sama suna dariya suka zauna, da kanta tayi serving nashi ta Haɗa mai tea ta tura mishi gabanshi, itama ta zuba nata don already yaran sun yi nisa a ci.

Yana yin loma ɗaya ya lumshe idanu yace
"you cooked?"

Murmushi kawai tayi, yace
"kin san wani abu?"

Ta girgiza kai tana Kallonshi, yace
"from the first time I tasted ur cook taste ɗinshi be ƙara barina na huta ba, I always longed to eat ur cooking u r really a great Cooker! Thank God"

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now