Page 16

231 22 1
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 16*

*FREE BOOK*

***Kun jini shiru, am sorry ear infection ke damuna wlh kuma dae in har ka san ciwon kunne ka san bashi da sauƙi***

Da sauri hidayat ta shiga tana rike hannayenta tace
"it's ok calm down and tell me menene?"

A hankali tayi mata whispering
"blood"

Murmushi hidayat tayi tana girgiza kai, komai fa na yan gata daban ne ita da ta fara period banda ita da ubangiji babu wadda ya sani yanzu ji wannan kwarmaton, fitowa tayi ta cewa miss Mary please ta dubo musu sanitary napkins a dispenser ɗin jikin makarantar.

Kan ta kawo ta koma wurin Norah tace
"it's fine, kowacce mace nayi yanzu girma ne ya kama ki Norah, dole ki dage mu koyi abubuwa dayawa in ba haka ba kina cikin hatsari sbd a musulunci duk wacce ta fara al'ada ta balaga kenan, kuma duk balagagge kaman an buɗe masa sabon file ne babu abunda ze yi na motsi ko magana ba tare da an rubuta ba kuma dashi ake anfani a yi hisabi"

Hawayen ta ta share tace
"am now a woman?"

Dariya hidaya tayi ta gyaɗa mata kai, cikin mintuna talatin ta gama nuna mata yadda zatayi using har ta saka ta fito tana ta aikin sussune kai for the first time da take jin kunyar mutane har haka a rayuwarta don su basa kunyar komai.

Daidai nan babanta ya karaso, a ruɗe yake sbd yadda miss Mary ta kirashi sanye yake da kananun kaya as usual kaman yadda kuka san ɗan ball da kaunar shorts, ko face cap babu a kanshi haka ma be saka face mask ba fuskanshi banda walki babu abunda take sbd reflection na rana ga shi kaman yana anfani da skin care don kyaun fata, yana da skin color me matukar tsada da fusgan hankali.

Da sauri ya karaso ba tare da ya lura da hannun hidayat dake cikin nata ba kai ko ma ya lura su a wurin su ba komai bane ya sanya hannunshi ya kama nasu duka biyu yana kallon Norah from head to toes..

"Baby..! Are you alright? Me ya same ki?"
Ya jefa mata tambayar da ta saka ta dukar da kai kawai, ya sake matse hannayensu yace
"talk to me, kina da wata matsala ne da zan kasa kau dashi? Are you been bullied? Baki son environment ɗin ne? Should we change SC...."

"Daaad" ta kira sunanshi cikin kunya, yace
"yes darling menene?"

Kasa magana tayi se ta kalli hidayat dake tsaye a wurin kaman statue, shima shanyayyun idanunshi ya juya ya watsa mata..

Tun daga sadda Tattausan fatar hannunshi ta sauka bisa nata ta daskare a wurin, wuta ne ya ɗauke mata gabaɗaya ko maganan da suke a wurin ba ji take ba, tsammm haka take jin wani abu na yawo a jikinta wadda bata taɓa ji ba, yaaa salam! Ta faɗi a zuciyarta a sadda taji saukar kaifaffun idanunshi bisa kanta, ji tayi kaman ɗaure ta akai...

Norah ce ta zame hannunta wadda yayi sanadiyar saukar nata ya zame daga nashi hannun, tana kiran sunanta
"Miss hidayat"

Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke tana  dawowa daidai ta amsa a daburce, be bi ta kanta ba don wani lokacin gani yake kaman ba daidai take ba abu kaɗan ke gigitata..

Daga wurin miss Mary ya ji abunda ke faruwa, se ya juya yana kallon Norah da kaman ta shige ƙasa daga ita har Hidayat ɗin, murmushi yayi yana rungume ta yace
"my Lil girl is now a grown up woman"

KOWA YA GA ZABUWA...जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें