Page 13

248 17 2
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 13

*FREE BOOK*

*Adda Haneefa and herlieymertouh this page is for you😍🥰❤️*

"Ina zaki je with this 2 little kids? Wai ni kam are you in ur right senses? How can you be so reckless abt ur kids well being? Do u really want them death as Usman?"
Maganan ya mugun dakarta, hakan ya sakata tsayawa Chak...

Me yake nufi? Zuciyarta yayi matukar zafi, ashe wani ze iya ganin laifinta akan yaranta? Yana ɗauka sakacinta ya saka kullum take cikin matsala? Bata ga laifin shi ba don ba shine a shoes ɗin hidayat ba, bata ga laifin shi ba saboda be san wacece hidayat ba..

Hawayen da take zubarwa ta sa hannu ta share, ba tare da ta juyo ba tace

"I never wish anything bad to them, na yarda akwai sakacina wurin rasa Usman sede ya zanyi? Ina zanje? Wurin wa zan je? Duk ban sani ba, bani da kowa bani da komai taya zan fara duk ban sani ba...! Don Allah ka gayamin ta ina zan fara???"
Ta karashe tana zubewa kan gwiwowinta tare da fashewa da kuka me tsananin cin rai, idan ta tuna sanadiyar kare mata duka Usman ya tafi se taji kaman ta kashe kanta ta huta sbd dacin zuciya...

"Who are you?"

Ya watso mata tambayar yana kallonta fuskanshi da little bit tausayinta da ya fara kama zuciyarshi daga ganin yadda take kuka she's terrified, and restless.

Kasa magana tayi se kuka, Aisha na duke a gabanta tana goge mata duk hawayen da suka zuba, hakan se ya motsa zuciyarshi...
Ganin kaman bata da niyyar amsa mishi tambayar yasa yace cikin cool voice

"I just wanna help, nd I cannot trust you with the work am gonna give you in har baki gayamin wacece ke ba!"
Yayi maganan yana maida idanunshi kan system ɗinshi, zafi zafi yake operating system ɗin a hankali yaji maganan ta cikin sanyi da karaya ta fara bashi labarinta tun daga farko yadda ta tashi ta ganta har zuwa kawo yanzu..

Tun yana yin typing ɗin sauri sauri har ya dawo a hankali a hankali daga karshe hannayenshi ne kawai zube bisa keyboard ɗin, ya lumshe idanunshi be taɓa jin labari makamancin wannan ba, yana Tunanin nashi labarin shine mafi munin labari ashe ba haka bane..! Ashe nashi azabar kaɗan ne shi namiji ne for that matter gashi yayi building career ɗinshi yayi kuɗi fiye da uban nashi..

Ashe akwai mutane haka? What a world are we living in.. Ya rabb.

Duk wannan Tunanin a zuciyarshi yake saboda kukan da take yi jin tsikar jikinshi yake a matukar tashe, har rawa zuciyar shi yake... Yarinya karama ce sossai wacce sa'anninta suna nan suna building career ɗinsu but nata is already shattered..

"How... How can I help you?"

Fuskanta da ya kumbura ta share, tace
"I want revenge!"

Da sauri ya ɗago ya kalleta jin yadda tayi maganan daga muryarta zata san har cikin zuciyarta abunda take nufi kenan..

"Da kaina nake so in bi ma Usman hakkin shi... Usman died bcs of me! Usman ya tafi saboda kare min duka how can I forget that?"

Kallonta ya cigaba da yi ba tare da ta kalleshi ba ta sake cewa

"Ina so in nemi aikin yi ko wani iri ne wadda za'a dinga biyana da wahalana, I want to study I want to be a barrister ta yadda zan dawo rayuwarsu kaman dirar mikiya!"

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now