Page 45

359 21 1
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 45*

*FREE BOOK*

"Har yanzu da sauran ku a sanin rayuwa Kausar... Kai Yusuf har ka isa kayi claiming right akan yaran nan? Anya akwai zuciya a kirjinka? Ka manta yadda ka dinga dukana kana azabtar dani da yunwa duk don kawai saboda kar su zo duniya? Ka manta duk wannan? Ka manta yadda ka ɗaga Usman ka buga kanshi da pillar wadda ya zama ajalinshi? Kana Tunanin wannan rayuwa da kake ciki shine kaɗai alhakin ran Usman? Yusuf wallahi wallahi da za'a bani izinin kashe mutum kwara ɗaya rak a duniya babu wadda zan zaɓa in halaka se kai, ka sani baka ga komai ba... A da nayi niyyan in ɗau fansar Usman da hannuwa na sede a yanzu na fasa wannan kuduri, kar ka yi tunanin saboda Abba ne ko su Aisha a'a, don babu ruwan Allah da wani yaci albarkacin wani a ranan gobe, ranar da uwa zata guji ƴarta, ƴa ta guji uwarta dangi su guji dangin su.. Abunda duk ka aikata shi kaɗai kai kaɗai zaka girbe abunka.. Aisha!!"

Ta kira Aisha dake cikin mota, saukowa yarinyar tayi ta tako ta zo kusa da Hidayat tace
"mommy ga ni!"

Inda Yusuf yake bata kalla ba, wasu irin hawaye masu ciwo ne ke fitar mishi, se a yanzu yake jin wani irin ƙaunar yaran da son su na shiganshi, kallon Aisha yake yana fata ko sau ɗaya ne ta kalleshi ta kira shi da suna 'Abba' abunda da a baya idan sun kira shi da hakan ji yake kaman sun jingina shi da mutuwa, Kallonshi hidayat tayi ta kalleta tace

"Aisha ga Abbanki na magana..!"

Aisha bata juya ba tace
"Mommy ni shi ba Abba na bane, ga daddynmu nan..!"

Ta Nuna Raed, rarrafowa Yusuf yayi yana shirin kai hannu Jikin Aishan don riƙeta wani irin ihu ta saki tana tsugunawa ta boye kanta cikin kafafunta

"No! Please don't touch, karka taɓa ni Mommy kice kar ya taɓa ni mugu ne! Ze kasheni yadda ya kashe yaya Usman... Mommy don Allah mu tafi kar ya dake ki ba zan iya shigar miki kaman ya Usman ba...!"
Gabaɗaya ta ruɗe, da sauri Raed ya ɗaga ta yana calming nata.

Yusuf kife kanshi yayi a ƙasar wurin yana kuka sossai, hidayat tace cikin muryarta dake rawa sossai
"ka gani ko? Yusuf ruwa cikin cokali ya ishi me hankali ya sha yayi wanka! A yanzu da nake da komai cikin harda duniya wato kuɗi ina da daman da zan sa a daureka ko a kasheka ba tare da kowa yace komai ba amma ba zan yi hakan ba! Ka zauna kayi tunanin laifukanka da hukuncin ubangiji kilan ka rage wasu abu daga cikin manyan zunubanka..."

Juyawa tayi tana kallon Abba tace
"Abba ni ma mutum ce kaman kowa, ina da zuciya a kirjina Abba sun min abunda ko kuɗi nake takawa basu cancanci taimakona ba, amma ba zan iya barin su hakanan ba! Abba ka basu wani abu su sake gina rayuwa albarkacin Abbana"

Daga haka ta juya ta koma mota tana share hawayenta, duk da kallo suka bita har ta koma, sossai umma da Yusuf ke kuka lallai rayuwa, haka Mahaifinta ya rubuta cheque ya ba umma, duk suka koma mota wannan karon kam Aisha motar Raed ta shiga suka bar arean, Maami bata ce komai ba saboda ta san idan Yusuf me hankali ne kalaman Hidayat gareshi shagube ne, idan ya fahimta yayi aiki dashi ya yiwa kanshi idan kuma be yi ba duk kanshi aka ce 'A word is enough for the wise'

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now